أَوۡ تَكُونَ لَكَ جَنَّةٞ مِّن نَّخِيلٖ وَعِنَبٖ فَتُفَجِّرَ ٱلۡأَنۡهَٰرَ خِلَٰلَهَا تَفۡجِيرًا
“Ko kuma ya zamana kana da wata gona ta dabinai da inabi, sai kuma ka vuvvugo da qoramu ta tsakiyarta su kwarara sosai
أَوۡ تُسۡقِطَ ٱلسَّمَآءَ كَمَا زَعَمۡتَ عَلَيۡنَا كِسَفًا أَوۡ تَأۡتِيَ بِٱللَّهِ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ قَبِيلًا
“Ko kuma ka rufto da sama a kanmu, kamar yadda ka riya, ta faxo yanki-yanki, ko kuma ka zo da Allah da kuma mala’iku (mu gan su) ido-da-ido!
أَوۡ يَكُونَ لَكَ بَيۡتٞ مِّن زُخۡرُفٍ أَوۡ تَرۡقَىٰ فِي ٱلسَّمَآءِ وَلَن نُّؤۡمِنَ لِرُقِيِّكَ حَتَّىٰ تُنَزِّلَ عَلَيۡنَا كِتَٰبٗا نَّقۡرَؤُهُۥۗ قُلۡ سُبۡحَانَ رَبِّي هَلۡ كُنتُ إِلَّا بَشَرٗا رَّسُولٗا
“Ko kuma ya zamana kana da wani gida na zinari, ko kuma ka hau sama, ba kuwa za mu amince da hawan naka ba har sai ka saukar mana da wani littafi da za mu karanta shi.” Ka ce (da su): “Tsarki ya tabbata ga Ubangijina, ni ba kowa ba ne face mutum Manzo.”
وَمَا مَنَعَ ٱلنَّاسَ أَن يُؤۡمِنُوٓاْ إِذۡ جَآءَهُمُ ٱلۡهُدَىٰٓ إِلَّآ أَن قَالُوٓاْ أَبَعَثَ ٱللَّهُ بَشَرٗا رَّسُولٗا
Kuma babu abin da ya hana kafirai su yi imani lokacin da shiriya ta zo musu, sai cewar da suka yi: “Yanzu Allah ne zai aiko mutum a matsayin manzo?”
قُل لَّوۡ كَانَ فِي ٱلۡأَرۡضِ مَلَـٰٓئِكَةٞ يَمۡشُونَ مُطۡمَئِنِّينَ لَنَزَّلۡنَا عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ مَلَكٗا رَّسُولٗا
Ka ce: “Da mala’iku ne suke tafiya a natse a bayan qasa, to da lalle Mun aiko musu mala’ika daga sama a matsayin manzo.”
قُلۡ كَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدَۢا بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ بِعِبَادِهِۦ خَبِيرَۢا بَصِيرٗا
Ka ce: “Allah Ya isa shaida tsakanina da ku: Lalle Shi ya zamanto Masani ne ga bayinsa, kuma Mai ganin (abin da suke aikatawa) ne.”
وَمَن يَهۡدِ ٱللَّهُ فَهُوَ ٱلۡمُهۡتَدِۖ وَمَن يُضۡلِلۡ فَلَن تَجِدَ لَهُمۡ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِهِۦۖ وَنَحۡشُرُهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ عَلَىٰ وُجُوهِهِمۡ عُمۡيٗا وَبُكۡمٗا وَصُمّٗاۖ مَّأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ كُلَّمَا خَبَتۡ زِدۡنَٰهُمۡ سَعِيرٗا
Wanda kuwa Allah Ya shiryar to shi ne shiryayye; wanda kuwa Ya vatar to ba za ka sami wani mai taimakon su ba in ban da Shi; za kuma Mu tashe su ranar alqiyama a kan fuskokinsu suna makafi, kurame, bebaye; makomarsu Jahannama; duk sanda ta lafa sai Mu qara musu qunarta
ذَٰلِكَ جَزَآؤُهُم بِأَنَّهُمۡ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَقَالُوٓاْ أَءِذَا كُنَّا عِظَٰمٗا وَرُفَٰتًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ خَلۡقٗا جَدِيدًا
Wannan ne sakamakonsu saboda lalle sun kafirce wa ayoyinmu, suka kuma ce: “Yanzu idan muka zama qasusuwa kuma rududdugaggu, anya kuwa za a tashe mu a sabuwar halitta?”