ٱلَّذِينَ جَعَلُواْ ٱلۡقُرۡءَانَ عِضِينَ
(Su ne) waxanda suka mai da Alqur’ani kashi-kashi[1]
1- Watau suka yi imani da wani vangare suka kafirce wa wani vangare.
فَوَرَبِّكَ لَنَسۡـَٔلَنَّهُمۡ أَجۡمَعِينَ
(Na rantse) da Ubangijinka tabbas za Mu tambaye su gaba xaya
عَمَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Game da abin da suka kasance suna aikatawa
فَٱصۡدَعۡ بِمَا تُؤۡمَرُ وَأَعۡرِضۡ عَنِ ٱلۡمُشۡرِكِينَ
To ka tsage gaskiyar abin da aka umarce ka da shi, ka kuma kawar da kanka daga mushirikai
إِنَّا كَفَيۡنَٰكَ ٱلۡمُسۡتَهۡزِءِينَ
Lalle Mu Mun isar maka (sharrin) masu izgili
ٱلَّذِينَ يَجۡعَلُونَ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَۚ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ
(Su ne) waxanda suke sanya wani abin bauta tare da Allah. Ba ko da daxewa ba za su sani
وَلَقَدۡ نَعۡلَمُ أَنَّكَ يَضِيقُ صَدۡرُكَ بِمَا يَقُولُونَ
Haqiqa kuma Muna sane da cewa qirjinka yana qunci game da abin da suke faxa
فَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ وَكُن مِّنَ ٱلسَّـٰجِدِينَ
To sai ka yi tasbihi tare da godiyar Ubangijinka, ka kuma zamo cikin masu sujjada
وَٱعۡبُدۡ رَبَّكَ حَتَّىٰ يَأۡتِيَكَ ٱلۡيَقِينُ
Ka kuma bauta wa Ubangijinka har yaqini ya zo maka (wato mutuwa)
أَتَىٰٓ أَمۡرُ ٱللَّهِ فَلَا تَسۡتَعۡجِلُوهُۚ سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ
Al’amarin Allah ya zo, don haka kada ku nemi gaggauto shi (watau ranar alqiyama). Tsarki ya tabbata a gare Shi, Ya kuma xaukaka daga abin da suke tara (Shi da shi)
يُنَزِّلُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ بِٱلرُّوحِ مِنۡ أَمۡرِهِۦ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦٓ أَنۡ أَنذِرُوٓاْ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱتَّقُونِ
Yana saukar da mala’iku da wahayi na umarninsa ga waxanda Ya ga dama daga bayinsa da cewa,: “Ku yi gargaxi cewa,, lalle ba wani abin bauta sai Ni, to sai ku kiyaye dokokina.”
خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّۚ تَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ
Ya halicci sammai da qasa da gaskiya. Ya xaukaka daga abin da suke tara (Shi da shi)
خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ مِن نُّطۡفَةٖ فَإِذَا هُوَ خَصِيمٞ مُّبِينٞ
Ya halicci mutum daga maniyyi, sai ga shi mai jayayya a fili
وَٱلۡأَنۡعَٰمَ خَلَقَهَاۖ لَكُمۡ فِيهَا دِفۡءٞ وَمَنَٰفِعُ وَمِنۡهَا تَأۡكُلُونَ
Ya kuma halicci dabbobin ni’ima. Kuna da (abin) xumama jiki tattare da su, da kuma sauran abubuwan amfani; daga gare su ne kuma kuke ci
وَلَكُمۡ فِيهَا جَمَالٌ حِينَ تُرِيحُونَ وَحِينَ تَسۡرَحُونَ
Kuma kuna da abubuwan ado a tattare da su, lokacin da kuke dawowa (daga kiwo) da kuma lokacin da kuke fita (da safe)
وَتَحۡمِلُ أَثۡقَالَكُمۡ إِلَىٰ بَلَدٖ لَّمۡ تَكُونُواْ بَٰلِغِيهِ إِلَّا بِشِقِّ ٱلۡأَنفُسِۚ إِنَّ رَبَّكُمۡ لَرَءُوفٞ رَّحِيمٞ
Suna kuma xaukar kayayyakinku masu nauyi zuwa garin da ba za ku iya isar sa ba sai da qyar. Lalle Ubangijinku tabbas Mai tausayi ne, Mai rahama
وَٱلۡخَيۡلَ وَٱلۡبِغَالَ وَٱلۡحَمِيرَ لِتَرۡكَبُوهَا وَزِينَةٗۚ وَيَخۡلُقُ مَا لَا تَعۡلَمُونَ
Dawakai da kuma alfadarai da jakai (Ya halitta muku su) don ku hau su kuma su zama ado. Zai kuma hallici abin da ma ba ku sani ba
وَعَلَى ٱللَّهِ قَصۡدُ ٱلسَّبِيلِ وَمِنۡهَا جَآئِرٞۚ وَلَوۡ شَآءَ لَهَدَىٰكُمۡ أَجۡمَعِينَ
Kuma bayanin hanya madaidaiciya haqqi ne a kan Allah, daga kuma (hanyar) akwai karkatacciya. Da kuma Ya ga dama lalle da Ya shirye ku gaba xaya
هُوَ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗۖ لَّكُم مِّنۡهُ شَرَابٞ وَمِنۡهُ شَجَرٞ فِيهِ تُسِيمُونَ
Shi ne wanda Ya saukar da ruwa daga sama; daga gare shi ne kuke sha, daga gare shi ne kuma bishiyoyi suke (sha) wanda da su ne kuke kiwon (dabbobinku)
يُنۢبِتُ لَكُم بِهِ ٱلزَّرۡعَ وَٱلزَّيۡتُونَ وَٱلنَّخِيلَ وَٱلۡأَعۡنَٰبَ وَمِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ
Da shi (ruwan) Yake tsiro muku da shuke-shuke da zaitun da dabinai da inabai da kuma kowanne irin ‘ya’yan itace. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya ga mutanen da suke tunani
وَسَخَّرَ لَكُمُ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ وَٱلنُّجُومُ مُسَخَّرَٰتُۢ بِأَمۡرِهِۦٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ
Ya kuma hore muku dare da rana da kuma wata; taurari ma ababen horewa ne da umarninsa. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutane masu hankali
وَمَا ذَرَأَ لَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُخۡتَلِفًا أَلۡوَٰنُهُۥٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَذَّكَّرُونَ
Da kuma abubuwan da Ya halitta muku a qasa masu launi iri daban-daban. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya ga mutanen da suke wa’azantuwa
وَهُوَ ٱلَّذِي سَخَّرَ ٱلۡبَحۡرَ لِتَأۡكُلُواْ مِنۡهُ لَحۡمٗا طَرِيّٗا وَتَسۡتَخۡرِجُواْ مِنۡهُ حِلۡيَةٗ تَلۡبَسُونَهَاۖ وَتَرَى ٱلۡفُلۡكَ مَوَاخِرَ فِيهِ وَلِتَبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِهِۦ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ
Shi ne kuma wanda Ya hore muku kogi don ku ci daddaxan nama mai taushi daga gare shi, ku kuma riqa fito da kayan ado daga cikinsa waxanda kuke xaurawa, kuma ka ga jiragen ruwa suna keta shi don kuma ku nema daga falalarsa (Ubangiji) don kuma ku riqa godiya
وَأَلۡقَىٰ فِي ٱلۡأَرۡضِ رَوَٰسِيَ أَن تَمِيدَ بِكُمۡ وَأَنۡهَٰرٗا وَسُبُلٗا لَّعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ
Ya kuma sanya wa qasa turaku don kada ta riqa tangal-tangal da ku da kuma qoramu da hanyoyi don ku riqa gane (inda kuka dosa)
وَعَلَٰمَٰتٖۚ وَبِٱلنَّجۡمِ هُمۡ يَهۡتَدُونَ
Da kuma alamomin (hanya). Da kuma taurari ne suke gane (inda suka dosa)
أَفَمَن يَخۡلُقُ كَمَن لَّا يَخۡلُقُۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
Yanzu wanda Yake halitta (zai yi) daidai da wanda ba ya halitta? Yanzo ba kwa wa’a zantu ba?
وَإِن تَعُدُّواْ نِعۡمَةَ ٱللَّهِ لَا تُحۡصُوهَآۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَغَفُورٞ رَّحِيمٞ
Idan kuma da za ku qirga ni’imar Allah to ba za ku iya qididdige ta ba. Lalle Allah tabbas Mai gafara ne, Mai jin qai
وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا تُسِرُّونَ وَمَا تُعۡلِنُونَ
Allah kuma Ya san abin da kuke voyewa da abin da kuke bayyanawa
وَٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَا يَخۡلُقُونَ شَيۡـٔٗا وَهُمۡ يُخۡلَقُونَ
Waxannan kuma suke bauta wa ba Allah ba, ba sa iya halittar komai, su ne ma ake halittar su
أَمۡوَٰتٌ غَيۡرُ أَحۡيَآءٖۖ وَمَا يَشۡعُرُونَ أَيَّانَ يُبۡعَثُونَ
Matattu ne su ba rayayyu ba; ba sa kuma sanin sanda za a tashe su