السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 75

۞وَمِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ مَنۡ إِن تَأۡمَنۡهُ بِقِنطَارٖ يُؤَدِّهِۦٓ إِلَيۡكَ وَمِنۡهُم مَّنۡ إِن تَأۡمَنۡهُ بِدِينَارٖ لَّا يُؤَدِّهِۦٓ إِلَيۡكَ إِلَّا مَا دُمۡتَ عَلَيۡهِ قَآئِمٗاۗ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَالُواْ لَيۡسَ عَلَيۡنَا فِي ٱلۡأُمِّيِّـۧنَ سَبِيلٞ وَيَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ

Kuma daga cikin Ma’abota Littafi akwai wanda in da za ka ba shi amana ta dukiya mai yawa, zai dawo maka da ita, daga cikinsu kuwa akwai wanda idan da za ka ba shi amana ta dinare xaya, ba zai dawo maka da shi ba, sai fa idan ka tashi tsaye a kansa. Wannan kuwa saboda sun ce: “Babu wani laifi a kanmu (don mun ci dukiyar) bobayin mutane.” Kuma suna faxin qarya su jingina wa Allah, alhalin su suna sane



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 76

بَلَىٰۚ مَنۡ أَوۡفَىٰ بِعَهۡدِهِۦ وَٱتَّقَىٰ فَإِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُتَّقِينَ

Ba haka ba ne, duk wanda ya cika alqawarinsa, kuma ya tsare dokar Allah, to lalle Allah Yana son masu taqawa



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 77

إِنَّ ٱلَّذِينَ يَشۡتَرُونَ بِعَهۡدِ ٱللَّهِ وَأَيۡمَٰنِهِمۡ ثَمَنٗا قَلِيلًا أُوْلَـٰٓئِكَ لَا خَلَٰقَ لَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ وَلَا يُكَلِّمُهُمُ ٱللَّهُ وَلَا يَنظُرُ إِلَيۡهِمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَلَا يُزَكِّيهِمۡ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Lalle waxanda suke musanya alqawarin Allah da rantse-rantsensu da wani xan farashi qanqani, waxannan ba su da wani rabo a lahira, kuma Allah ba zai yi musu magana ba, kuma ba zai dube su (duba na rahama) ba a ranar alqiyama, kuma ba zai tsarkake su ba, kuma suna da azaba mai raxaxi



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 78

وَإِنَّ مِنۡهُمۡ لَفَرِيقٗا يَلۡوُۥنَ أَلۡسِنَتَهُم بِٱلۡكِتَٰبِ لِتَحۡسَبُوهُ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَمَا هُوَ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَيَقُولُونَ هُوَ مِنۡ عِندِ ٱللَّهِ وَمَا هُوَ مِنۡ عِندِ ٱللَّهِۖ وَيَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ

Kuma lalle daga cikinsu akwai wani vangare da suke karkatar da harshensu lokacin karanta Littafin (Attaura), don ku yi zaton yana cikin Littafin, alhali kuwa ba ya cikin Littafin, kuma za su riqa cewa, shi (wahayi ne saukakke) daga wurin Allah, alhalin kuwa ba daga wurin Allah yake ba, kuma za su riqa faxar qarya suna jingina wa Allah, alhalin suna sane



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 79

مَا كَانَ لِبَشَرٍ أَن يُؤۡتِيَهُ ٱللَّهُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحُكۡمَ وَٱلنُّبُوَّةَ ثُمَّ يَقُولَ لِلنَّاسِ كُونُواْ عِبَادٗا لِّي مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَٰكِن كُونُواْ رَبَّـٰنِيِّـۧنَ بِمَا كُنتُمۡ تُعَلِّمُونَ ٱلۡكِتَٰبَ وَبِمَا كُنتُمۡ تَدۡرُسُونَ

Bai dace ba ga wani mutum wanda Allah zai ba shi littafi da hukunci da annabci, sannan ya ce wa mutane: “Ku zama bayina ba na Allah ba,” sai dai (ya ce): “Ku zamo malamai na Allah saboda abin da kuke karantarwa na littafi, kuma saboda abin da kuka kasance kuna karantawa.”



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 80

وَلَا يَأۡمُرَكُمۡ أَن تَتَّخِذُواْ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ أَرۡبَابًاۚ أَيَأۡمُرُكُم بِٱلۡكُفۡرِ بَعۡدَ إِذۡ أَنتُم مُّسۡلِمُونَ

Kuma ba zai umarce ku da ku riqi mala’iku ko annabawa a matsayin iyayengiji ba; yanzu zai umarce ku da kafirci ne bayan kuna Musulmi?



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 81

وَإِذۡ أَخَذَ ٱللَّهُ مِيثَٰقَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ لَمَآ ءَاتَيۡتُكُم مِّن كِتَٰبٖ وَحِكۡمَةٖ ثُمَّ جَآءَكُمۡ رَسُولٞ مُّصَدِّقٞ لِّمَا مَعَكُمۡ لَتُؤۡمِنُنَّ بِهِۦ وَلَتَنصُرُنَّهُۥۚ قَالَ ءَأَقۡرَرۡتُمۡ وَأَخَذۡتُمۡ عَلَىٰ ذَٰلِكُمۡ إِصۡرِيۖ قَالُوٓاْ أَقۡرَرۡنَاۚ قَالَ فَٱشۡهَدُواْ وَأَنَا۠ مَعَكُم مِّنَ ٱلشَّـٰهِدِينَ

Kuma ka tuna lokacin da Allah Ya yi alqawari da annabawa cewa: “Duk irin abin da Na ba ku na littafi da wata hikima, sannan sai wani Manzo ya zo muku mai gaskata abin da yake tare da ku, to lalle ku yi imani da shi, kuma lalle ku taimake shi.” Ya ce: “Shin kun yarda da hakan, kuma kun xauki alqawarina a kan hakan?” Suka ce: “Mun yarda da haka.” Ya ce: “To ku shaida, kuma Ni ma Ina tare da ku cikin masu shaidawa.”



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 82

فَمَن تَوَلَّىٰ بَعۡدَ ذَٰلِكَ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ

To duk wanda ya juya baya bayan wannan, to waxannan su ne fasiqai



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 83

أَفَغَيۡرَ دِينِ ٱللَّهِ يَبۡغُونَ وَلَهُۥٓ أَسۡلَمَ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ طَوۡعٗا وَكَرۡهٗا وَإِلَيۡهِ يُرۡجَعُونَ

To shin yanzu wani addini suke nema ba na Allah ba, alhalin duk wanda yake cikin sammai da qasa gare Shi ne ya miqa wuya yana so ko yana qi, kuma zuwa gare Shi za a komar da su?



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 84

قُلۡ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَمَآ أُنزِلَ عَلَيۡنَا وَمَآ أُنزِلَ عَلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطِ وَمَآ أُوتِيَ مُوسَىٰ وَعِيسَىٰ وَٱلنَّبِيُّونَ مِن رَّبِّهِمۡ لَا نُفَرِّقُ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّنۡهُمۡ وَنَحۡنُ لَهُۥ مُسۡلِمُونَ

Ka ce: “Mun yi imani da Allah da abin da aka saukar mana da kuma abin da aka saukar wa Ibrahim da Isma’ila da Ishaq da Ya’aqub da jikokin (Ya’aqub), da abin da aka ba wa Musa da Isa da abin da aka ba wa annabawa daga Ubangijinsu; ba ma nuna bambanci a kan xaya daga cikinsu, kuma mu muna masu miqa wuya gare Shi.”



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 85

وَمَن يَبۡتَغِ غَيۡرَ ٱلۡإِسۡلَٰمِ دِينٗا فَلَن يُقۡبَلَ مِنۡهُ وَهُوَ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

Duk kuma wanda ya nemi (bin) wani addini ba Musulunci ba, to har abada ba za a karva daga gare shi ba, kuma shi a lahira yana cikin hasararru



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 86

كَيۡفَ يَهۡدِي ٱللَّهُ قَوۡمٗا كَفَرُواْ بَعۡدَ إِيمَٰنِهِمۡ وَشَهِدُوٓاْ أَنَّ ٱلرَّسُولَ حَقّٞ وَجَآءَهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُۚ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Ta yaya Allah zai shiryar da mutanen da suka kafirta bayan imaninsu, kuma bayan sun shaida cewa, Manzon gaskiya ne, kuma hujjoji sun zo musu? Allah kuwa ba Ya shiryar da mutane azzalumai



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 87

أُوْلَـٰٓئِكَ جَزَآؤُهُمۡ أَنَّ عَلَيۡهِمۡ لَعۡنَةَ ٱللَّهِ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ وَٱلنَّاسِ أَجۡمَعِينَ

Waxannan sakamakonsu (shi ne), lalle la’antar Allah za ta tabbata a kansu da ta mala’iku da mutane gaba xaya



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 88

خَٰلِدِينَ فِيهَا لَا يُخَفَّفُ عَنۡهُمُ ٱلۡعَذَابُ وَلَا هُمۡ يُنظَرُونَ

Suna masu dawwama a cikinta, ba za a sassauta musu azaba ba, kuma ba za a jinkirta musu ba



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 89

إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ وَأَصۡلَحُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ

Sai fa waxanda suka sake tuba bayan haka, kuma suka gyara (ayyukansu), to lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 90

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بَعۡدَ إِيمَٰنِهِمۡ ثُمَّ ٱزۡدَادُواْ كُفۡرٗا لَّن تُقۡبَلَ تَوۡبَتُهُمۡ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلضَّآلُّونَ

Lalle waxanda suka kafirta bayan imaninsu, sannan suka qara zurfi cikin kafirci, to ba za a karvi tubansu ba, kuma waxannan su ne vatattu



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 91

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَمَاتُواْ وَهُمۡ كُفَّارٞ فَلَن يُقۡبَلَ مِنۡ أَحَدِهِم مِّلۡءُ ٱلۡأَرۡضِ ذَهَبٗا وَلَوِ ٱفۡتَدَىٰ بِهِۦٓۗ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ وَمَا لَهُم مِّن نَّـٰصِرِينَ

Lalle waxanda suka kafirta, kuma suka mutu alhali suna kafirai, to ba za a tava karvar cikin qasa na zinare daga xayansu ba, ko da zai fanshi kansa da shi. Waxannan suna da wata azaba mai raxaxi kuma ba su da wasu mataimaka



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 92

لَن تَنَالُواْ ٱلۡبِرَّ حَتَّىٰ تُنفِقُواْ مِمَّا تُحِبُّونَۚ وَمَا تُنفِقُواْ مِن شَيۡءٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِهِۦ عَلِيمٞ

Ba za ku tava dacewa da aiki na alheri ba har sai kun ciyar daga abin da kuke so, kuma abin da duk kuka ciyar kowane iri ne, to lalle Allah Yana sane da shi