وَجَعَلۡنَا بَيۡنَهُمۡ وَبَيۡنَ ٱلۡقُرَى ٱلَّتِي بَٰرَكۡنَا فِيهَا قُرٗى ظَٰهِرَةٗ وَقَدَّرۡنَا فِيهَا ٱلسَّيۡرَۖ سِيرُواْ فِيهَا لَيَالِيَ وَأَيَّامًا ءَامِنِينَ
Muka kuma sanya wasu alqaryu mabayyana a tsakaninsu (mutan Saba’u) da alqaryar da Muka sa albarka a cikinta (wato qasar Sham)[1], Muka kuma taqaita zangon tafiya a tsakaninsu (alqaryun; Muka ce): “Ku yi tafiya a cikinsu dare da rana cikin aminci.”
1- Watau Allah () ya sanya wasu fitattun alqaryu da matafiya kan iya hango su daga nesa, wanda hakan ya sauqaqa musu tafiye-tafiyensu.
فَقَالُواْ رَبَّنَا بَٰعِدۡ بَيۡنَ أَسۡفَارِنَا وَظَلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ فَجَعَلۡنَٰهُمۡ أَحَادِيثَ وَمَزَّقۡنَٰهُمۡ كُلَّ مُمَزَّقٍۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّكُلِّ صَبَّارٖ شَكُورٖ
Sai suka ce: “Ya Ubangijinmu, Ka qaddara nisa tsakanin zangunan tafiyarmu,” suka kuwa zalunci kansu, sai Muka mai da su tarihi[1], Muka kuma warwatsa su wuri-wuri. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga duk wani mai yin haquri, mai yin godiya
1- Watau Allah () ya tarwatsa su suka warwatsu a garuruwa daban-daban har haxuwa da junansu ta yi musu wahala.
وَلَقَدۡ صَدَّقَ عَلَيۡهِمۡ إِبۡلِيسُ ظَنَّهُۥ فَٱتَّبَعُوهُ إِلَّا فَرِيقٗا مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Kuma haqiqa Iblisu ya tabbatar da zatonsa a kansu gaskiya ne[1], sai suka bi shi, in ban da wata qungiya ta muminai
1- Watau na cewa zai iya vatar da su ya raba su da gaskiya.
وَمَا كَانَ لَهُۥ عَلَيۡهِم مِّن سُلۡطَٰنٍ إِلَّا لِنَعۡلَمَ مَن يُؤۡمِنُ بِٱلۡأٓخِرَةِ مِمَّنۡ هُوَ مِنۡهَا فِي شَكّٖۗ وَرَبُّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٍ حَفِيظٞ
Shi kuwa ba shi da wani qarfi a kansu, sai dai (Mun yi haka ne) don Mu bayyana wanda yake imani da ranar lahira da kuma wanda yake cikin shakka game da ita. Ubangijinka kuwa Mai kiyaye komai ne
قُلِ ٱدۡعُواْ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ لَا يَمۡلِكُونَ مِثۡقَالَ ذَرَّةٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا لَهُمۡ فِيهِمَا مِن شِرۡكٖ وَمَا لَهُۥ مِنۡهُم مِّن ظَهِيرٖ
Ka ce: “Ku kirawo waxanda kuka riya (cewa su ne iyayen giji) ba Allah ba;” ba sa mallakar wani abu daidai da qwayar zarra a cikin sammai ko a cikin qasa, ba kuma su da wata tarayya a cikinsu, ba Shi kuma da wani mataimaki daga cikinsu
وَلَا تَنفَعُ ٱلشَّفَٰعَةُ عِندَهُۥٓ إِلَّا لِمَنۡ أَذِنَ لَهُۥۚ حَتَّىٰٓ إِذَا فُزِّعَ عَن قُلُوبِهِمۡ قَالُواْ مَاذَا قَالَ رَبُّكُمۡۖ قَالُواْ ٱلۡحَقَّۖ وَهُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡكَبِيرُ
Kuma ceto ba ya amfani a wurinsa sai ga wanda Ya yi wa izinin yin sa. Har idan an cire tsoro daga cikin zukatansu[1], sai su ce: “Me Ubangijinku Ya ce ne?” Suka ce: “Gaskiya Ya faxa, kuma Shi ne Maxaukaki, Mai girma.”
1- Saboda cikar mulkin Allah idan ya yi wata magana mala’iku gaba xaya sukan buga fukafukansu suna masu rusunawa ga maganarsa, suna masu cike da tsoro.