وَلَمَّا وَرَدَ مَآءَ مَدۡيَنَ وَجَدَ عَلَيۡهِ أُمَّةٗ مِّنَ ٱلنَّاسِ يَسۡقُونَ وَوَجَدَ مِن دُونِهِمُ ٱمۡرَأَتَيۡنِ تَذُودَانِۖ قَالَ مَا خَطۡبُكُمَاۖ قَالَتَا لَا نَسۡقِي حَتَّىٰ يُصۡدِرَ ٱلرِّعَآءُۖ وَأَبُونَا شَيۡخٞ كَبِيرٞ
Lokacin da kuma ya iso mashayar ruwa ta Madyana sai ya sami wani gungun mutane suna shayar (da dabbobinsu), ya kuma sami wasu mata su biyu a gefensu suna kare (dabbobinsu); sai ya ce (da su): “Me ya same ku ne?” Sai suka ce: “Mu ai ba ma shayarwa har sai duk makiyaya sun watse, kuma mahaifinmu tsoho ne tukub.”
فَسَقَىٰ لَهُمَا ثُمَّ تَوَلَّىٰٓ إِلَى ٱلظِّلِّ فَقَالَ رَبِّ إِنِّي لِمَآ أَنزَلۡتَ إِلَيَّ مِنۡ خَيۡرٖ فَقِيرٞ
To sai ya shayar musu (da dabbobin nasu), sannan ya koma wurin wata inuwa ya ce: “Ya Ubangijina, lalle ni mabuqacin duk wani alhairi ne da za ka hore mini!”
فَجَآءَتۡهُ إِحۡدَىٰهُمَا تَمۡشِي عَلَى ٱسۡتِحۡيَآءٖ قَالَتۡ إِنَّ أَبِي يَدۡعُوكَ لِيَجۡزِيَكَ أَجۡرَ مَا سَقَيۡتَ لَنَاۚ فَلَمَّا جَآءَهُۥ وَقَصَّ عَلَيۡهِ ٱلۡقَصَصَ قَالَ لَا تَخَفۡۖ نَجَوۡتَ مِنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Sai xayarsu ta zo masa tana tafiya cikin jin kunya ta ce: “Babana yana kiran ka don ya saka maka ladan shayarwar da ka yi mana.” To lokacin da ya zo wurinsa ya kuma ba shi labarin(sa) sai ya ce da shi: “Kada ka ji tsoro, ka tsira daga azzaluman mutane.”
قَالَتۡ إِحۡدَىٰهُمَا يَـٰٓأَبَتِ ٱسۡتَـٔۡجِرۡهُۖ إِنَّ خَيۡرَ مَنِ ٱسۡتَـٔۡجَرۡتَ ٱلۡقَوِيُّ ٱلۡأَمِينُ
Sai xayarsu ta ce: “Babana, ka xauke shi aiki mana; don kuwa lalle ba wanda ya fi dacewa ka xauka aiki sai qaqqarfa, amintacce.”
قَالَ إِنِّيٓ أُرِيدُ أَنۡ أُنكِحَكَ إِحۡدَى ٱبۡنَتَيَّ هَٰتَيۡنِ عَلَىٰٓ أَن تَأۡجُرَنِي ثَمَٰنِيَ حِجَجٖۖ فَإِنۡ أَتۡمَمۡتَ عَشۡرٗا فَمِنۡ عِندِكَۖ وَمَآ أُرِيدُ أَنۡ أَشُقَّ عَلَيۡكَۚ سَتَجِدُنِيٓ إِن شَآءَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ
Sai ya ce da (Musa): “Ina so in aura maka xaya daga ‘ya’yayen nan nawa guda biyu, a kan ka yi min aiki na shekara takwas; to amma idan ka cika goma to wannan raxin kanka ne; ba na kuwa nufin in quntata maka. Za ka same ni kuwa in Allah Ya yarda daga cikin nagartattun mutane.”
قَالَ ذَٰلِكَ بَيۡنِي وَبَيۡنَكَۖ أَيَّمَا ٱلۡأَجَلَيۡنِ قَضَيۡتُ فَلَا عُدۡوَٰنَ عَلَيَّۖ وَٱللَّهُ عَلَىٰ مَا نَقُولُ وَكِيلٞ
(Musa) ya ce: “Wannan tsakanina da kai ne; kowanne xayan lokatan biyu na cika to kada a qware ni; Allah kuwa shaida ne game da abin da muke faxa.”
۞فَلَمَّا قَضَىٰ مُوسَى ٱلۡأَجَلَ وَسَارَ بِأَهۡلِهِۦٓ ءَانَسَ مِن جَانِبِ ٱلطُّورِ نَارٗاۖ قَالَ لِأَهۡلِهِ ٱمۡكُثُوٓاْ إِنِّيٓ ءَانَسۡتُ نَارٗا لَّعَلِّيٓ ءَاتِيكُم مِّنۡهَا بِخَبَرٍ أَوۡ جَذۡوَةٖ مِّنَ ٱلنَّارِ لَعَلَّكُمۡ تَصۡطَلُونَ
To yayin da Musa ya cika lokacinsa ya kuma tafi da iyalinsa, sai ya hango wuta daga gefen (dutsen) Xuri, ya ce: “Lalle na hango wuta, (zan je don) in zo muku da labari daga wurinta ko kuma (in samo muku) wani garwashi na wutar don ku ji xumi.”
فَلَمَّآ أَتَىٰهَا نُودِيَ مِن شَٰطِيِٕ ٱلۡوَادِ ٱلۡأَيۡمَنِ فِي ٱلۡبُقۡعَةِ ٱلۡمُبَٰرَكَةِ مِنَ ٱلشَّجَرَةِ أَن يَٰمُوسَىٰٓ إِنِّيٓ أَنَا ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
To lokacin da ya zo wurinta sai aka yi kira daga gefen kwari na damarsa a wani wuri mai albarka na bishiya, cewa: “Ya Musa, lalle Ni ne Allah Ubangijin talikai!
وَأَنۡ أَلۡقِ عَصَاكَۚ فَلَمَّا رَءَاهَا تَهۡتَزُّ كَأَنَّهَا جَآنّٞ وَلَّىٰ مُدۡبِرٗا وَلَمۡ يُعَقِّبۡۚ يَٰمُوسَىٰٓ أَقۡبِلۡ وَلَا تَخَفۡۖ إِنَّكَ مِنَ ٱلۡأٓمِنِينَ
“Kuma ka jefar da sandarka;” to lokacin da ya gan ta tana girgiza kamar maciji sai ya ba da baya a guje, bai ko waiwaya ba. (Aka ce da shi): “Ya Musa dawo, kada ka ji tsoro; lalle kai kana cikin amintattu
ٱسۡلُكۡ يَدَكَ فِي جَيۡبِكَ تَخۡرُجۡ بَيۡضَآءَ مِنۡ غَيۡرِ سُوٓءٖ وَٱضۡمُمۡ إِلَيۡكَ جَنَاحَكَ مِنَ ٱلرَّهۡبِۖ فَذَٰنِكَ بُرۡهَٰنَانِ مِن رَّبِّكَ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦٓۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَوۡمٗا فَٰسِقِينَ
“Ka sanya hannunka a cikin wuyan rigarka, zai fito fari fat ba tare da wata cuta ba, kuma ka haxe hannunka da kwivinka saboda tsoron (farinta); to biyu xin nan hujjoji ne daga Ubangijinka zuwa ga Fir’auna da mutanensa. Lalle su sun kasance mutane ne fasiqai.”
قَالَ رَبِّ إِنِّي قَتَلۡتُ مِنۡهُمۡ نَفۡسٗا فَأَخَافُ أَن يَقۡتُلُونِ
(Musa) ya ce: “Ya Ubangijina, lalle ni na kashe musu wani mutum, to ina tsoron su kashe ni
وَأَخِي هَٰرُونُ هُوَ أَفۡصَحُ مِنِّي لِسَانٗا فَأَرۡسِلۡهُ مَعِيَ رِدۡءٗا يُصَدِّقُنِيٓۖ إِنِّيٓ أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ
“Kuma xan’uwana Haruna shi ya fi ni fasahar harshe, sai Ka aike shi tare da ni ya zama mataimakina yana gaskata ni; lalle ni ina jin tsoron su qaryata ni.”
قَالَ سَنَشُدُّ عَضُدَكَ بِأَخِيكَ وَنَجۡعَلُ لَكُمَا سُلۡطَٰنٗا فَلَا يَصِلُونَ إِلَيۡكُمَا بِـَٔايَٰتِنَآۚ أَنتُمَا وَمَنِ ٱتَّبَعَكُمَا ٱلۡغَٰلِبُونَ
(Sai Allah) Ya ce: “Za Mu qarfafa dantsenka da xan’uwanka kuma za Mu sanya muku wata hujja, don haka ba za su isa gare ku (da cuta) ba. Da ayoyinmu - ku da waxanda suka bi ku - ku ne masu yin galaba.”
فَلَمَّا جَآءَهُم مُّوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَا بَيِّنَٰتٖ قَالُواْ مَا هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّفۡتَرٗى وَمَا سَمِعۡنَا بِهَٰذَا فِيٓ ءَابَآئِنَا ٱلۡأَوَّلِينَ
To lokacin da Musa ya zo musu da ayoyinmu mabayyana sai suka ce: “Ai wannan ba wani abu ba ne face qagaggen sihiri, mu kuma ba mu tava jin wannan ba a wurin iyayenmu na farko.”
وَقَالَ مُوسَىٰ رَبِّيٓ أَعۡلَمُ بِمَن جَآءَ بِٱلۡهُدَىٰ مِنۡ عِندِهِۦ وَمَن تَكُونُ لَهُۥ عَٰقِبَةُ ٱلدَّارِۚ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلظَّـٰلِمُونَ
Musa kuma ya ce: “Ubangijina (Shi ne) Ya fi sanin wanda ya zo da shiriya daga wurinsa, da kuma wanda kyakkyawan qarshe zai kasance a gare shi; lalle yadda al’amarin yake, azzalumai ba sa rabauta.”
وَقَالَ فِرۡعَوۡنُ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡمَلَأُ مَا عَلِمۡتُ لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرِي فَأَوۡقِدۡ لِي يَٰهَٰمَٰنُ عَلَى ٱلطِّينِ فَٱجۡعَل لِّي صَرۡحٗا لَّعَلِّيٓ أَطَّلِعُ إِلَىٰٓ إِلَٰهِ مُوسَىٰ وَإِنِّي لَأَظُنُّهُۥ مِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ
Fir’auna kuma ya ce: “Ya ku manyan gari, ban san kuna da wani abin bauta ba in ba ni ba, kai ko Hamana, shirya min qonannen tavo sannan ka yi min dogon gini don in hango abin bautar Musa, lalle ni ina tsammanin cewa shi yana cikin maqaryata.”
وَٱسۡتَكۡبَرَ هُوَ وَجُنُودُهُۥ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَظَنُّوٓاْ أَنَّهُمۡ إِلَيۡنَا لَا يُرۡجَعُونَ
Ya kuma yi girman kai shi da rundunoninsa a qasar (Masar) ba da gaskiya ba, suka kuma yi tsammanin cewa su ba za a komar da su zuwa gare Mu ba
فَأَخَذۡنَٰهُ وَجُنُودَهُۥ فَنَبَذۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡيَمِّۖ فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Sai Muka kama shi da rundunoninsa, sannan Muka watsa su a cikin kogi; to ka duba ka ga yadda qarshen azzalumai ya kasance
وَجَعَلۡنَٰهُمۡ أَئِمَّةٗ يَدۡعُونَ إِلَى ٱلنَّارِۖ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ لَا يُنصَرُونَ
Muka kuma mayar da su shugabanni masu kira zuwa ga wuta; ranar alqiyama kuma ba za a taimake su ba
وَأَتۡبَعۡنَٰهُمۡ فِي هَٰذِهِ ٱلدُّنۡيَا لَعۡنَةٗۖ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ هُم مِّنَ ٱلۡمَقۡبُوحِينَ
Muka kuma bi su da la’anta a wannan duniyar; ranar alqiyama kuma suna cikin waxanda za a jefa cikin mummunan hali
وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ مِنۢ بَعۡدِ مَآ أَهۡلَكۡنَا ٱلۡقُرُونَ ٱلۡأُولَىٰ بَصَآئِرَ لِلنَّاسِ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٗ لَّعَلَّهُمۡ يَتَذَكَّرُونَ
Haqiqa kuma Mun bai wa Musa littafin (Attaura) bayan Mun hallaka al’ummu na farko don izina ga mutane da shiriya da rahama ko sa wa’azantu
وَمَا كُنتَ بِجَانِبِ ٱلۡغَرۡبِيِّ إِذۡ قَضَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَى ٱلۡأَمۡرَ وَمَا كُنتَ مِنَ ٱلشَّـٰهِدِينَ
Kai kuma ba ka kasance a gefen (dutsen Xuri) na yamma ba lokacin da Muka yo wahayin manzanci zuwa ga Musa, ba ka kuma kasance cikin mahalarta wurin ba
وَلَٰكِنَّآ أَنشَأۡنَا قُرُونٗا فَتَطَاوَلَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡعُمُرُۚ وَمَا كُنتَ ثَاوِيٗا فِيٓ أَهۡلِ مَدۡيَنَ تَتۡلُواْ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتِنَا وَلَٰكِنَّا كُنَّا مُرۡسِلِينَ
Sai dai cewa Mu Mun halicci al’ummu, sai nisan zamani ya tsawaita a gare su[1]. Kuma ba ka kasance a zaune cikin mutanen Madyana ba[2] kana karanta musu ayoyinmu, sai dai kuma Mu Mun kasance Masu aiko da (manzanni)
1- Watau al’ummun da suka zo bayan Annabi Musa (), sai lokaci ya tsawaita gare su har suka manta alqawarin da suka yi tsakaninsu da Allah; ilimi ya yi qaranci.
2- Watau ba don whayin da Allah () ya yi wa Manzonsa ba, da ba za san labarin abin da ya faru ga Annabi Musa () ba.
وَمَا كُنتَ بِجَانِبِ ٱلطُّورِ إِذۡ نَادَيۡنَا وَلَٰكِن رَّحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَ لِتُنذِرَ قَوۡمٗا مَّآ أَتَىٰهُم مِّن نَّذِيرٖ مِّن قَبۡلِكَ لَعَلَّهُمۡ يَتَذَكَّرُونَ
Kuma ba ka kasance a gefen (dutsen) Xuri ba, lokacin da Muka kirawo (Musa), sai dai wata rahama daga Ubangijinka, don ka gargaxi wasu mutane da mai gargaxi bai zo musu ba gabaninka ko sa wa’azantu
وَلَوۡلَآ أَن تُصِيبَهُم مُّصِيبَةُۢ بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيهِمۡ فَيَقُولُواْ رَبَّنَا لَوۡلَآ أَرۡسَلۡتَ إِلَيۡنَا رَسُولٗا فَنَتَّبِعَ ءَايَٰتِكَ وَنَكُونَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Kuma ba don kada wata masifa ta same su ba saboda abin da suka aikata da kansu sai su riqa cewa: “Ya Ubangijinmu, ina ma da Ka aiko mana da wani manzo, da sai mu bi ayoyinka mu kuma kasance cikin muminai[1]?”
1- Watau da a ce wata azaba ta sauka a kansu saboda yawan savonsu, to da sai su ce, me ya sa Allah bai aiko musu da wani manzo ba wanda zai gargaxe su.
فَلَمَّا جَآءَهُمُ ٱلۡحَقُّ مِنۡ عِندِنَا قَالُواْ لَوۡلَآ أُوتِيَ مِثۡلَ مَآ أُوتِيَ مُوسَىٰٓۚ أَوَلَمۡ يَكۡفُرُواْ بِمَآ أُوتِيَ مُوسَىٰ مِن قَبۡلُۖ قَالُواْ سِحۡرَانِ تَظَٰهَرَا وَقَالُوٓاْ إِنَّا بِكُلّٖ كَٰفِرُونَ
To lokacin da gaskiya ta zo musu daga wajenmu sai suka ce: “Ina ma da an ba shi irin abin da aka bai wa Musa?” Yanzu ashe tun da can ba su kafirce da abin da aka bai wa Musa ba; suka ce: “Su biyun sihiri ne (wato Alqur’ani da Attaura) da suke taimakon juna?” Suka kuma ce: “Lalle mu mun kafirce da su gaba xaya.”
قُلۡ فَأۡتُواْ بِكِتَٰبٖ مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِ هُوَ أَهۡدَىٰ مِنۡهُمَآ أَتَّبِعۡهُ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Ka ce (da su): “To ku zo da wani littafi daga wajen Allah wanda ya fi su nuna hanyar shiriya (wato Alqur’ani da Attaura), zan bi shi idan kun kasance masu gaskiya.”
فَإِن لَّمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَكَ فَٱعۡلَمۡ أَنَّمَا يَتَّبِعُونَ أَهۡوَآءَهُمۡۚ وَمَنۡ أَضَلُّ مِمَّنِ ٱتَّبَعَ هَوَىٰهُ بِغَيۡرِ هُدٗى مِّنَ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ
To idan ba su amsa maka ba, to ka sani cewa ba abin da suke bi sai soye-soyen zukatansu kawai. Ba kuwa wanda ya fi vacewa kamar wanda ya bi son zuciyarsa ba tare da wata shiriya daga Allah ba. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai