السورة: Suratul Baqara

الآية : 135

وَقَالُواْ كُونُواْ هُودًا أَوۡ نَصَٰرَىٰ تَهۡتَدُواْۗ قُلۡ بَلۡ مِلَّةَ إِبۡرَٰهِـۧمَ حَنِيفٗاۖ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

Kuma suka ce: “Ku zama Yahudawa ko Nasara za ku shiriya”. Ka ce: “A’a! (Za mu bi) addinin Ibrahimu ne wanda yake miqe totar, kuma bai zamo daga cikin masu shirka ba.”



السورة: Suratul Baqara

الآية : 136

قُولُوٓاْ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡنَا وَمَآ أُنزِلَ إِلَىٰٓ إِبۡرَٰهِـۧمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطِ وَمَآ أُوتِيَ مُوسَىٰ وَعِيسَىٰ وَمَآ أُوتِيَ ٱلنَّبِيُّونَ مِن رَّبِّهِمۡ لَا نُفَرِّقُ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّنۡهُمۡ وَنَحۡنُ لَهُۥ مُسۡلِمُونَ

Ku ce: “Mun yi imani da Allah da abin da aka saukar mana, da abin da aka saukar wa Ibrahimu da Isma’ila da Ishaqa da Ya’aqubu da jikoki da abin da aka ba wa Musa da Isa da abin da aka ba annabawa duka daga Ubangijinsu, kuma ba ma nuna bambanci tsakanin wani daga cikinsu, kuma mu gare Shi muke miqa wuya.”



السورة: Suratul Baqara

الآية : 137

فَإِنۡ ءَامَنُواْ بِمِثۡلِ مَآ ءَامَنتُم بِهِۦ فَقَدِ ٱهۡتَدَواْۖ وَّإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّمَا هُمۡ فِي شِقَاقٖۖ فَسَيَكۡفِيكَهُمُ ٱللَّهُۚ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

Don haka idan sun yi imani da irin abin da kuka yi imani da shi, to haqiqa sun shiriya, idan kuwa suka juya da baya, to haqiqa su suna cikin savani. To da sannu Allah zai isar maka da su, kuma Shi Mai ji ne, Mai gani



السورة: Suratul Baqara

الآية : 138

صِبۡغَةَ ٱللَّهِ وَمَنۡ أَحۡسَنُ مِنَ ٱللَّهِ صِبۡغَةٗۖ وَنَحۡنُ لَهُۥ عَٰبِدُونَ

Rinin Allah, wane ne kuwa ya fi Allah kyan rini? Kuma mu masu bauta ne a gare Shi



السورة: Suratul Baqara

الآية : 139

قُلۡ أَتُحَآجُّونَنَا فِي ٱللَّهِ وَهُوَ رَبُّنَا وَرَبُّكُمۡ وَلَنَآ أَعۡمَٰلُنَا وَلَكُمۡ أَعۡمَٰلُكُمۡ وَنَحۡنُ لَهُۥ مُخۡلِصُونَ

Ka ce, “Shin za ku yi jayayya da mu ne game da sha’anin Allah, alhalin Shi ne Ubangijinmu kuma Ubangijinku? Kuma ayyukanmu namu ne, ayyukanku kuma naku ne, kuma mu masu tsarkake ayyuka ne gare Shi (Allah)



السورة: Suratul Baqara

الآية : 140

أَمۡ تَقُولُونَ إِنَّ إِبۡرَٰهِـۧمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطَ كَانُواْ هُودًا أَوۡ نَصَٰرَىٰۗ قُلۡ ءَأَنتُمۡ أَعۡلَمُ أَمِ ٱللَّهُۗ وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن كَتَمَ شَهَٰدَةً عِندَهُۥ مِنَ ٱللَّهِۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ

Ko kuma kuna cewa ne, “Lalle Ibrahimu da Isma’ila da Ishaqa da Ya’aqubu da jikoki sun kasance Yahudawa ne ko Nasara?” Ka ce: “Ku ne kuka fi sani ko kuma Allah?” Kuma ba wanda ya fi zalunci kamar wanda ya voye shaidar da take wajensa daga Allah, kuma Allah ba rafkananne ne ba game da abin da kuke aikatawa



السورة: Suratul Baqara

الآية : 141

تِلۡكَ أُمَّةٞ قَدۡ خَلَتۡۖ لَهَا مَا كَسَبَتۡ وَلَكُم مَّا كَسَبۡتُمۡۖ وَلَا تُسۡـَٔلُونَ عَمَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Waccan al’umma ce da ta riga ta wuce, abin da ta aikata mallakarta ne, ku ma abin da kuka aikata naku ne, kuma ba za a tambaye ku game da abin da suka kasance suna aikatawa ba.”