إِذۡ قَالَتِ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَٰمَرۡيَمُ إِنَّ ٱللَّهَ يُبَشِّرُكِ بِكَلِمَةٖ مِّنۡهُ ٱسۡمُهُ ٱلۡمَسِيحُ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ وَجِيهٗا فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ وَمِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ
Ka tuna lokacin da mala’iku suka ce: “Ya ke Maryamu, lalle Allah Yana yi miki albishir da wata kalma daga gare shi, sunansa Almasihu Isa xan Maryamu, mai daraja a duniya da lahira, kuma yana cikin bayi makusanta
وَيُكَلِّمُ ٱلنَّاسَ فِي ٱلۡمَهۡدِ وَكَهۡلٗا وَمِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ
“Kuma zai riqa yi wa mutane magana tun yana cikin shimfixar jego da kuma lokacin da ya zama dattijo, kuma yana cikin salihan bayi.”
قَالَتۡ رَبِّ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي وَلَدٞ وَلَمۡ يَمۡسَسۡنِي بَشَرٞۖ قَالَ كَذَٰلِكِ ٱللَّهُ يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُۚ إِذَا قَضَىٰٓ أَمۡرٗا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ
Sai ta ce: “Ya Ubangijina, ta yaya zan sami xa alhalin wani namiji bai kusance ni ba?” Sai ya ce: “Kamar haka ne Allah Yake halittar abin da Ya ga dama. Idan Ya yi zartar da wani al’amari, sai Ya ce da shi: “Kasance” Nan take sai ya kasance
وَيُعَلِّمُهُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ
“Kuma zai sanar da shi rubutu da hikima da Attaura da Linjila
وَرَسُولًا إِلَىٰ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ أَنِّي قَدۡ جِئۡتُكُم بِـَٔايَةٖ مِّن رَّبِّكُمۡ أَنِّيٓ أَخۡلُقُ لَكُم مِّنَ ٱلطِّينِ كَهَيۡـَٔةِ ٱلطَّيۡرِ فَأَنفُخُ فِيهِ فَيَكُونُ طَيۡرَۢا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۖ وَأُبۡرِئُ ٱلۡأَكۡمَهَ وَٱلۡأَبۡرَصَ وَأُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۖ وَأُنَبِّئُكُم بِمَا تَأۡكُلُونَ وَمَا تَدَّخِرُونَ فِي بُيُوتِكُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لَّكُمۡ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ
“Kuma zai aiko shi a matsayin Manzo ga Banu Isra’ila (yana mai cewa): “Lalle ni na zo muku da wata aya daga Ubangijinku; lalle ni zan riqa mulmula muku tavo a siffar tsuntsu, sai in yi busa a cikinsa sai ya zama tsuntsu da izinin Allah; kuma zan warkar da wanda aka haifa makaho da mai cutar albaras, kuma in rayar da matattu da izinin Allah; kuma zan riqa ba ku labarin abin da kuke ci da abin da kuke ajiyewa a gidajenku. Lalle a cikin hakan akwai aya a gare ku in har kun kasance muminai
وَمُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيَّ مِنَ ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَلِأُحِلَّ لَكُم بَعۡضَ ٱلَّذِي حُرِّمَ عَلَيۡكُمۡۚ وَجِئۡتُكُم بِـَٔايَةٖ مِّن رَّبِّكُمۡ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
“Kuma zan zama mai gaskata abin da ya gabace ni na Attaura, kuma don in halatta muku sashin abubuwan da aka haramta muku. Kuma na zo muku da wata aya daga Ubangijinku, don haka ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku yi mini biyayya
إِنَّ ٱللَّهَ رَبِّي وَرَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُوهُۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ
“Lalle Allah Shi ne Ubangijina kuma Ubangijinku, don haka ku bautata masa Shi kaxai. Wannan shi ne tafarki madaidaici.”
۞فَلَمَّآ أَحَسَّ عِيسَىٰ مِنۡهُمُ ٱلۡكُفۡرَ قَالَ مَنۡ أَنصَارِيٓ إِلَى ٱللَّهِۖ قَالَ ٱلۡحَوَارِيُّونَ نَحۡنُ أَنصَارُ ٱللَّهِ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَٱشۡهَدۡ بِأَنَّا مُسۡلِمُونَ
To yayin da Isa ya ga alamun kafirci a tare da su sai ya ce: “Su wane ne za su taimake ni wajen kira zuwa ga Allah?” Sai Hawariyawa suka ce: “Mu ne mataimaka addinin Allah, mun yi imani da Allah, kuma ka ba da shaida cewa, mu Musulmai ne
رَبَّنَآ ءَامَنَّا بِمَآ أَنزَلۡتَ وَٱتَّبَعۡنَا ٱلرَّسُولَ فَٱكۡتُبۡنَا مَعَ ٱلشَّـٰهِدِينَ
“Ya Ubangijinmu, mun yi imani da abin da Ka saukar, kuma mun yi xa’a ga Manzo, don haka Ka rubuta mu tare da masu shaida.”
وَمَكَرُواْ وَمَكَرَ ٱللَّهُۖ وَٱللَّهُ خَيۡرُ ٱلۡمَٰكِرِينَ
Sai suka shirya makirci, sai Allah Ya mayar musu da martani game da makircinsu; kuma Allah Shi ne Fiyayyen masu mayar da martanin makirci
إِذۡ قَالَ ٱللَّهُ يَٰعِيسَىٰٓ إِنِّي مُتَوَفِّيكَ وَرَافِعُكَ إِلَيَّ وَمُطَهِّرُكَ مِنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَجَاعِلُ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوكَ فَوۡقَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِۖ ثُمَّ إِلَيَّ مَرۡجِعُكُمۡ فَأَحۡكُمُ بَيۡنَكُمۡ فِيمَا كُنتُمۡ فِيهِ تَخۡتَلِفُونَ
Kuma ka tuna lokacin da Allah Ya ce: “Ya kai Isa, lalle Ni Mai karvar ranka ne, kuma Ni Mai xaukaka ka ne zuwa gare Ni, kuma zan tsarkake ka daga (cutarwar) waxanda suka kafirta, kuma zan xora waxanda suka bi ka a kan waxanda suka kafirta har zuwa ranar tashin alqiyama; sannan zuwa gare Ni ne makomarku take, sai In yi hukunci a tsakaninku game da abin da kuke savani a kansa
فَأَمَّا ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَأُعَذِّبُهُمۡ عَذَابٗا شَدِيدٗا فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ وَمَا لَهُم مِّن نَّـٰصِرِينَ
Amma waxanda suka kafirce, zan yi musu azaba mai tsanani a duniya da lahira, kuma ba su da wasu mataimaka.”
وَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ فَيُوَفِّيهِمۡ أُجُورَهُمۡۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Amma kuma waxanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyuka nagari, to (Allah) zai cika musu ladansu. Kuma Allah ba Ya son azzalumai
ذَٰلِكَ نَتۡلُوهُ عَلَيۡكَ مِنَ ٱلۡأٓيَٰتِ وَٱلذِّكۡرِ ٱلۡحَكِيمِ
“Wannan (labarin) Muna karanta maka shi ne daga ayoyi da kuma Alkur’ani mai hikima.”
إِنَّ مَثَلَ عِيسَىٰ عِندَ ٱللَّهِ كَمَثَلِ ءَادَمَۖ خَلَقَهُۥ مِن تُرَابٖ ثُمَّ قَالَ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ
Lalle misalin Isa a wurin Allah kamar misalin Adamu ne; Ya halicce shi daga turvaya, sannan Ya ce da shi: “Kasance.” nan take sai ya kasance
ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَلَا تَكُن مِّنَ ٱلۡمُمۡتَرِينَ
Gaskiya ce daga wajen Ubangijinka, don haka kar ka kasance cikin masu yin kokwanto
فَمَنۡ حَآجَّكَ فِيهِ مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَكَ مِنَ ٱلۡعِلۡمِ فَقُلۡ تَعَالَوۡاْ نَدۡعُ أَبۡنَآءَنَا وَأَبۡنَآءَكُمۡ وَنِسَآءَنَا وَنِسَآءَكُمۡ وَأَنفُسَنَا وَأَنفُسَكُمۡ ثُمَّ نَبۡتَهِلۡ فَنَجۡعَل لَّعۡنَتَ ٱللَّهِ عَلَى ٱلۡكَٰذِبِينَ
To duk wanda ya yi jayayya da kai cikin lamarinsa (Isa) bayan abin da ya zo maka na ilimi, to ka ce: “Ku zo mu kirawo ‘ya’yanmu da ‘ya’yanku da matanmu da matanku da mu kanmu da ku kanku, sannan mu qasqantar da kawunanmu cikin addu’a don mu roqi tsinuwar Allah ta tabbata a kan maqaryata”
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلۡقَصَصُ ٱلۡحَقُّۚ وَمَا مِنۡ إِلَٰهٍ إِلَّا ٱللَّهُۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Lalle wannan shi ne ba da labari na gaskiya. Kuma babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah. Kuma lalle Allah Shi ne Mabuwayi, Mai hikima
فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمُۢ بِٱلۡمُفۡسِدِينَ
To idan sun ba da baya, to lalle Allah Yana sane da mavarnata
قُلۡ يَـٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ تَعَالَوۡاْ إِلَىٰ كَلِمَةٖ سَوَآءِۭ بَيۡنَنَا وَبَيۡنَكُمۡ أَلَّا نَعۡبُدَ إِلَّا ٱللَّهَ وَلَا نُشۡرِكَ بِهِۦ شَيۡـٔٗا وَلَا يَتَّخِذَ بَعۡضُنَا بَعۡضًا أَرۡبَابٗا مِّن دُونِ ٱللَّهِۚ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَقُولُواْ ٱشۡهَدُواْ بِأَنَّا مُسۡلِمُونَ
Ka ce: “Ya ku Ma’abota Littafi, ku taho ga wata kalma mai daidaitawa tsakaninmu da ku cewa, kar mu bauta wa kowa sai Allah, kuma kar mu haxa Shi da wani, kuma kada wani sashi a cikinmu ya riqi wani sashi a matsayin abin bauta ba Allah ba.” Idan kuwa sun ba da baya, to ku ce: “Ku shaida cewa, lalle mu Musulmi ne.”
يَـٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لِمَ تُحَآجُّونَ فِيٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَمَآ أُنزِلَتِ ٱلتَّوۡرَىٰةُ وَٱلۡإِنجِيلُ إِلَّا مِنۢ بَعۡدِهِۦٓۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ
Ya ku Ma’abota Littafi, don me kuke yin jayayya game da Ibrahimu, alhalin ba a saukar da Attaura da Linjila ba sai bayan shuxewarsa? Yanzu ba za ku hankalta ba?
هَـٰٓأَنتُمۡ هَـٰٓؤُلَآءِ حَٰجَجۡتُمۡ فِيمَا لَكُم بِهِۦ عِلۡمٞ فَلِمَ تُحَآجُّونَ فِيمَا لَيۡسَ لَكُم بِهِۦ عِلۡمٞۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ
Ga ku nan ku waxannan kun yi jayayya kan abin da kuke da ilimi a kai, to don me kuma kuke jayayya a kan abin da ba ku da ilimi a kansa? Kuma Allah Yana sane ku ba ku sani ba
مَا كَانَ إِبۡرَٰهِيمُ يَهُودِيّٗا وَلَا نَصۡرَانِيّٗا وَلَٰكِن كَانَ حَنِيفٗا مُّسۡلِمٗا وَمَا كَانَ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ
Ibrahimu bai tava zama Bayahude ba, sannan bai tava zama Banasare ba, sai dai ya kasance mai barin varna ne, Musulmi, kuma bai kasance xaya daga cikin mushirikai ba
إِنَّ أَوۡلَى ٱلنَّاسِ بِإِبۡرَٰهِيمَ لَلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُ وَهَٰذَا ٱلنَّبِيُّ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْۗ وَٱللَّهُ وَلِيُّ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Lalle mafi kusancin mutane da Ibrahimu su ne waxanda suka bi shi, sai kuma wannan Annabin, da kuma waxanda suka yi Imani. Kuma Allah shi ne Majivincin al’amuran muminai
وَدَّت طَّآئِفَةٞ مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ لَوۡ يُضِلُّونَكُمۡ وَمَا يُضِلُّونَ إِلَّآ أَنفُسَهُمۡ وَمَا يَشۡعُرُونَ
Wata qungiya daga cikin Ma’abota Littatafi sun yi burin ina ma sun vatar da ku, kuma ba za su vatar da kowa ba sai kawunansu, amma ba sa sanin hakan
يَـٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لِمَ تَكۡفُرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَأَنتُمۡ تَشۡهَدُونَ
Ya ku Ma’abota Littafi, don me kuke kafirce wa ayoyin Allah, alhalin ku kuna shaidawa (cewa gaskiya ne)?
يَـٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لِمَ تَلۡبِسُونَ ٱلۡحَقَّ بِٱلۡبَٰطِلِ وَتَكۡتُمُونَ ٱلۡحَقَّ وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Ya ku Ma’abota Littafi, don me kuke cakuxa gaskiya da qarya, kuma kuke voye gaskiya, alhalin ku kuna sane?
وَقَالَت طَّآئِفَةٞ مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ ءَامِنُواْ بِٱلَّذِيٓ أُنزِلَ عَلَى ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَجۡهَ ٱلنَّهَارِ وَٱكۡفُرُوٓاْ ءَاخِرَهُۥ لَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ
Kuma wata qungiya cikin Ma’abota Littafi suka ce: “Ku yi imani mana da abin da aka saukar wa waxanda suka yi imani a farkon yini, kuma ku kafirce a qarshen yini, mai yiwuwa ne su dawo (daga rakiyar addininsu)
وَلَا تُؤۡمِنُوٓاْ إِلَّا لِمَن تَبِعَ دِينَكُمۡ قُلۡ إِنَّ ٱلۡهُدَىٰ هُدَى ٱللَّهِ أَن يُؤۡتَىٰٓ أَحَدٞ مِّثۡلَ مَآ أُوتِيتُمۡ أَوۡ يُحَآجُّوكُمۡ عِندَ رَبِّكُمۡۗ قُلۡ إِنَّ ٱلۡفَضۡلَ بِيَدِ ٱللَّهِ يُؤۡتِيهِ مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٞ
“Kuma kada ku amince da kowa sai wanda ya bi addininku.” Ka ce: “Lalle shiriya ita ce shiriyar Allah, domin kar (ku yarda a ce) an ba wani mutum irin abin da aka ba ku, ko kuma ku ba su dama su yi jayayya da ku a wajen Ubangijinku.” Ka ce: “Lalle falala a hannun Allah take, Yana bayar da ita ga wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mai yalwa ne, Mai yawan sani
يَخۡتَصُّ بِرَحۡمَتِهِۦ مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ
“Yana kevantar wanda Ya ga dama da rahamarsa, kuma Allah Ma’abocin falala ne wadda take mai girma.”