فَٱسۡتَخَفَّ قَوۡمَهُۥ فَأَطَاعُوهُۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَوۡمٗا فَٰسِقِينَ
Sai ya yi wasa da hankalin mutanensa sai suka bi shi. Lalle su sun kasance mutane ne fasiqai
فَلَمَّآ ءَاسَفُونَا ٱنتَقَمۡنَا مِنۡهُمۡ فَأَغۡرَقۡنَٰهُمۡ أَجۡمَعِينَ
To lokacin da suka fusata Mu sai Muka saukar musu da uquba, Muka nutsar da su ga baki xaya
فَجَعَلۡنَٰهُمۡ سَلَفٗا وَمَثَلٗا لِّلۡأٓخِرِينَ
Sai Muka sanya su ja-gaba (wajen hallakarwa), kuma wa’azi ga na baya
۞وَلَمَّا ضُرِبَ ٱبۡنُ مَرۡيَمَ مَثَلًا إِذَا قَوۡمُكَ مِنۡهُ يَصِدُّونَ
Lokacin da kuwa aka buga misali da (Isa) xan Maryamu, sai ga mutanenka suna ta annashawa game da shi[1]
1- Watau lokacin da Abdullahi xan Az-Ziba’ara ya ji faxar Allah cewa, waxanda aka bautawa ba Allah ba za su shiga wuta tare da masu bautarsu, sai ya ce, to idan haka ne Annabi Isa ma zai shiga wuta, wannan magana tasa ta faranta wa mushirikai rai sosai.
وَقَالُوٓاْ ءَأَٰلِهَتُنَا خَيۡرٌ أَمۡ هُوَۚ مَا ضَرَبُوهُ لَكَ إِلَّا جَدَلَۢاۚ بَلۡ هُمۡ قَوۡمٌ خَصِمُونَ
Suka kuma ce: “Yanzu ababen bautar mu ne suka fi ko kuwa shi (Isa)?” Ba su buga maka misali da shi ba sai don son jayayya. Ba shakka su dai mutane ne masu tsananin jayayya
إِنۡ هُوَ إِلَّا عَبۡدٌ أَنۡعَمۡنَا عَلَيۡهِ وَجَعَلۡنَٰهُ مَثَلٗا لِّبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ
Shi (Isa) ba wani ba ne face bawa ne da Muka yi masa ni’ima, Muka kuma sanya shi abin buga misali ga Bani-Isra’ila
وَلَوۡ نَشَآءُ لَجَعَلۡنَا مِنكُم مَّلَـٰٓئِكَةٗ فِي ٱلۡأَرۡضِ يَخۡلُفُونَ
Da kuma za Mu ga dama tabbas da Mun sanya mala’iku ne za su maye gurbinku a bayan qasa
وَإِنَّهُۥ لَعِلۡمٞ لِّلسَّاعَةِ فَلَا تَمۡتَرُنَّ بِهَا وَٱتَّبِعُونِۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ
Lalle kuma shi (Isa) alama ce ta zuwan alqiyama[1], kada ku yi shakka game da ita, kuma ku bi Ni. Wannan ita ce hanya madaidaiciya
1- Watau lokacin da zai sauko daga sama ta biyu a qarshen zamani, kamar yadda tarin hadisan Annabi () suka tabbatar.
وَلَا يَصُدَّنَّكُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُۖ إِنَّهُۥ لَكُمۡ عَدُوّٞ مُّبِينٞ
Kada kuma Shaixan ya kange ku; lalle shi maqiyi ne mai bayyana (qiyyaya) a gare ku
وَلَمَّا جَآءَ عِيسَىٰ بِٱلۡبَيِّنَٰتِ قَالَ قَدۡ جِئۡتُكُم بِٱلۡحِكۡمَةِ وَلِأُبَيِّنَ لَكُم بَعۡضَ ٱلَّذِي تَخۡتَلِفُونَ فِيهِۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
Lokacin da kuma Isa ya zo da hujjoji bayyanannu ya ce: “Haqiqa na zo muku da hikima, don kuma in bayyana muku sashin da kuke sassavawa cikinsa; to ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku bi ni
إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ رَبِّي وَرَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُوهُۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ
“Lalle Allah Shi ne Ubangijina kuma Ubangijinku, sai ku bauta masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya.”
فَٱخۡتَلَفَ ٱلۡأَحۡزَابُ مِنۢ بَيۡنِهِمۡۖ فَوَيۡلٞ لِّلَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنۡ عَذَابِ يَوۡمٍ أَلِيمٍ
Sai qungiyoyi suka sassava a tsakaninsu[1]; don haka tsananin azabar yini mai raxaxi ya tabbata ga waxanda suka yi zalunci
1- Wasu suka ce shi Allah ne; wasu kuma suka ce xan Allah ne; wasu kuma suka ce shi da mahaifiyarsa duka alloli ne.
هَلۡ يَنظُرُونَ إِلَّا ٱلسَّاعَةَ أَن تَأۡتِيَهُم بَغۡتَةٗ وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ
Ba abin da suke jira sai alqiyama kawai ta zo musu kwatsam, alhali ba tare da sun sani ba
ٱلۡأَخِلَّآءُ يَوۡمَئِذِۭ بَعۡضُهُمۡ لِبَعۡضٍ عَدُوٌّ إِلَّا ٱلۡمُتَّقِينَ
Masoya a wannan ranar maqiyan juna ne sai masu taqawa kaxai
يَٰعِبَادِ لَا خَوۡفٌ عَلَيۡكُمُ ٱلۡيَوۡمَ وَلَآ أَنتُمۡ تَحۡزَنُونَ
Ya ku bayina, babu wani tsoro gare ku a yau, kuma ba za ku yi baqin ciki ba
ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَكَانُواْ مُسۡلِمِينَ
(Su ne) waxanda suka yi imani da ayoyinmu, suka kuma kasance Musulmi
ٱدۡخُلُواْ ٱلۡجَنَّةَ أَنتُمۡ وَأَزۡوَٰجُكُمۡ تُحۡبَرُونَ
(Za a ce da su): “Ku shiga Aljanna ku da matanku, za a faranta muku rai.”
يُطَافُ عَلَيۡهِم بِصِحَافٖ مِّن ذَهَبٖ وَأَكۡوَابٖۖ وَفِيهَا مَا تَشۡتَهِيهِ ٱلۡأَنفُسُ وَتَلَذُّ ٱلۡأَعۡيُنُۖ وَأَنتُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Ana zagayawa tsakaninsu da akusa na zinari da kofuna; a cikinta kuma akwai (duk) abin da rayuka suke sha’awa, idanuwa kuma suke jin daxin (ganinsu); ku kuma a cikinta madawwama ne
وَتِلۡكَ ٱلۡجَنَّةُ ٱلَّتِيٓ أُورِثۡتُمُوهَا بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Waccan kuma ita ce Aljannar da aka gadar muku ita saboda abin da kuka kasance kuma aikatawa
لَكُمۡ فِيهَا فَٰكِهَةٞ كَثِيرَةٞ مِّنۡهَا تَأۡكُلُونَ
A cikinta kuna da `ya`yan itatuwa na marmari masu yawa, daga gare su kuma za ku riqa ci
إِنَّ ٱلۡمُجۡرِمِينَ فِي عَذَابِ جَهَنَّمَ خَٰلِدُونَ
Lalle masu manyan laifuka suna cikin azabar (wutar) Jahannama suna masu dawwama
لَا يُفَتَّرُ عَنۡهُمۡ وَهُمۡ فِيهِ مُبۡلِسُونَ
Ba a yanke musu ita (azabar), su kuwa masu yanke qaunar (fita) ne daga cikinta
وَمَا ظَلَمۡنَٰهُمۡ وَلَٰكِن كَانُواْ هُمُ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Ba Mu kuwa zalunce su ba, sai dai su ne suka kasance azzalumai
وَنَادَوۡاْ يَٰمَٰلِكُ لِيَقۡضِ عَلَيۡنَا رَبُّكَۖ قَالَ إِنَّكُم مَّـٰكِثُونَ
Suka kuma yi kiran: “Ya (kai mai tsaron wuta) Maliku, Ubangijinka Ya kashe mu mana!” Ya ce: “Lalle ku masu dawwama ne.”
لَقَدۡ جِئۡنَٰكُم بِٱلۡحَقِّ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَكُمۡ لِلۡحَقِّ كَٰرِهُونَ
Haqiqa Mun zo muku da gaskiya sai dai kuma mafiya yawanku masu qin gaskiya ne
أَمۡ أَبۡرَمُوٓاْ أَمۡرٗا فَإِنَّا مُبۡرِمُونَ
A’a, sun dai shirya wani makirci ne, Mu ma lalle Masu yin namu shirin ne
أَمۡ يَحۡسَبُونَ أَنَّا لَا نَسۡمَعُ سِرَّهُمۡ وَنَجۡوَىٰهُمۚ بَلَىٰ وَرُسُلُنَا لَدَيۡهِمۡ يَكۡتُبُونَ
Ko suna tsammanin cewa Mu ba Ma jin asirinsu da ganawarsu ne? Ba haka ba ne, manzanninmu suna tare da su suna rubutawa
قُلۡ إِن كَانَ لِلرَّحۡمَٰنِ وَلَدٞ فَأَنَا۠ أَوَّلُ ٱلۡعَٰبِدِينَ
Ka ce: “Idan da (Allah) Mai rahama zai zamanto Yana da xa, to ni ne farkon masu bauta[1].”
1- Watau shi ne farkon masu bauta wa wannan xan, domin kuwa ya zama wani sashi ne na Allah.
سُبۡحَٰنَ رَبِّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ رَبِّ ٱلۡعَرۡشِ عَمَّا يَصِفُونَ
Tsarki ya tabbata ga Ubangijin sammai da qasa, Ubangiijn Al’arshi game da abin da suke siffantawa
فَذَرۡهُمۡ يَخُوضُواْ وَيَلۡعَبُواْ حَتَّىٰ يُلَٰقُواْ يَوۡمَهُمُ ٱلَّذِي يُوعَدُونَ
Sai ka bar su su yi ta kutse suna wasanni, har su haxu da ranar da ake alqawarta musu