السورة: Suratus Sajda

الآية : 18

أَفَمَن كَانَ مُؤۡمِنٗا كَمَن كَانَ فَاسِقٗاۚ لَّا يَسۡتَوُۥنَ

Yanzu wanda ya zamanto mumini ya zama kamar wanda ya kasance fasiqi? Ai ba za su zama daidai ba



السورة: Suratus Sajda

الآية : 19

أَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ فَلَهُمۡ جَنَّـٰتُ ٱلۡمَأۡوَىٰ نُزُلَۢا بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Amma waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, to suna da gidajen Aljanna na makoma, (wannan) liyafa ce saboda abin da suka kasance suna aikatawa



السورة: Suratus Sajda

الآية : 20

وَأَمَّا ٱلَّذِينَ فَسَقُواْ فَمَأۡوَىٰهُمُ ٱلنَّارُۖ كُلَّمَآ أَرَادُوٓاْ أَن يَخۡرُجُواْ مِنۡهَآ أُعِيدُواْ فِيهَا وَقِيلَ لَهُمۡ ذُوقُواْ عَذَابَ ٱلنَّارِ ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ

Amma kuma waxanda suka fice daga biyayyar Allah, to makomarsu wuta ce; ko da yaushe suka yi niyyar fitowa daga gare ta sai a mayar da su a cikinta a kuma ce da su: “Ku xanxani azabar wuta wadda kuka kasance kuna qaryatawa.”



السورة: Suratus Sajda

الآية : 21

وَلَنُذِيقَنَّهُم مِّنَ ٱلۡعَذَابِ ٱلۡأَدۡنَىٰ دُونَ ٱلۡعَذَابِ ٱلۡأَكۡبَرِ لَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ

Kuma tabbas lalle za Mu xanxana musu (wani abu) daga azabar da ta fi qanqanta (ta duniya) kafin azabar da ta fi girma (ta lahira) don su dawo (daga vata)



السورة: Suratus Sajda

الآية : 22

وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن ذُكِّرَ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِۦ ثُمَّ أَعۡرَضَ عَنۡهَآۚ إِنَّا مِنَ ٱلۡمُجۡرِمِينَ مُنتَقِمُونَ

Wane ne kuma mafi zalunci fiye da wanda aka yi wa wa’azi da ayoyin Ubangijinsa sannan ya bijire musu? Lalle Mu Masu saka wa masu manyan laifuka ne



السورة: Suratus Sajda

الآية : 23

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ فَلَا تَكُن فِي مِرۡيَةٖ مِّن لِّقَآئِهِۦۖ وَجَعَلۡنَٰهُ هُدٗى لِّبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ

Haqiqa kuma Mu Mun bai wa Musa Littafi, to kada ka kasance (kai Manzo) cikin kokwanto na saduwa da shi (Musan)[1]. Kuma Mun sanya shi ya zamanto shiriya ga Banu-Isra’ila


1- Watau haxuwar Annabi Muhammad () da Annabi Musa () a daren mi’iraji.


السورة: Suratus Sajda

الآية : 24

وَجَعَلۡنَا مِنۡهُمۡ أَئِمَّةٗ يَهۡدُونَ بِأَمۡرِنَا لَمَّا صَبَرُواْۖ وَكَانُواْ بِـَٔايَٰتِنَا يُوقِنُونَ

Muka kuma sanya shugabanni daga cikinsu waxanda suke shiryuwa da umarninmu yayin da suka yi haquri, suka kuma kasance suna sakankancewa da ayoyinmu



السورة: Suratus Sajda

الآية : 25

إِنَّ رَبَّكَ هُوَ يَفۡصِلُ بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فِيمَا كَانُواْ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ

Lalle Ubangijinka Shi ne zai yi hukunci a tsakaninsu ranar alqiyama game da abin da suka kasance suna sassavawa a kansa



السورة: Suratus Sajda

الآية : 26

أَوَلَمۡ يَهۡدِ لَهُمۡ كَمۡ أَهۡلَكۡنَا مِن قَبۡلِهِم مِّنَ ٱلۡقُرُونِ يَمۡشُونَ فِي مَسَٰكِنِهِمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٍۚ أَفَلَا يَسۡمَعُونَ

Yanzu ba su gane wa idanunsu ba al’ummu nawa Muka hallakar a gabaninsu waxanda suke ta zirga-zirga tsakankanin gidajensu? Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi; to me ya sa ba sa sauraro ne?



السورة: Suratus Sajda

الآية : 27

أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّا نَسُوقُ ٱلۡمَآءَ إِلَى ٱلۡأَرۡضِ ٱلۡجُرُزِ فَنُخۡرِجُ بِهِۦ زَرۡعٗا تَأۡكُلُ مِنۡهُ أَنۡعَٰمُهُمۡ وَأَنفُسُهُمۡۚ أَفَلَا يُبۡصِرُونَ

Ko kuwa ba sa gani cewa Mu Muke koro ruwa zuwa ga qeqasasshiyar qasa, sai Mu fitar da tsirrai da shi, waxanda dabbobinsu da su kansu suke ci daga gare shi? To me ya sa ba sa lura ne?



السورة: Suratus Sajda

الآية : 28

وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلۡفَتۡحُ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Suna kuma cewa: “Yaushe ne (ranar) wannan hukuncin idan kun kasance masu gaskiya?



السورة: Suratus Sajda

الآية : 29

قُلۡ يَوۡمَ ٱلۡفَتۡحِ لَا يَنفَعُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِيمَٰنُهُمۡ وَلَا هُمۡ يُنظَرُونَ

Ka ce: “Ranar hukuncin, waxanda suka kafirce, imaninsu ba zai amfane su ba, kuma ba ma za a saurara musu ba.”



السورة: Suratus Sajda

الآية : 30

فَأَعۡرِضۡ عَنۡهُمۡ وَٱنتَظِرۡ إِنَّهُم مُّنتَظِرُونَ

To ka rabu da su, ka kuma saurara, lalle su ma masu sauraro ne



السورة: Suratul Ahzab

الآية : 1

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ ٱتَّقِ ٱللَّهَ وَلَا تُطِعِ ٱلۡكَٰفِرِينَ وَٱلۡمُنَٰفِقِينَۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمٗا

Ya kai wannan Annabi, ka kiyaye dokokin Allah, kada ka yi wa kafirai da munafukai xa’a. Lalle Allah Ya kasance Masani ne, Mai hikima



السورة: Suratul Ahzab

الآية : 2

وَٱتَّبِعۡ مَا يُوحَىٰٓ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٗا

Kuma ka bi abin da ake yi maka wahayinsa daga Ubangijinka. Lalle Allah Ya kasance Masanin abin da kuke aikatawa ne



السورة: Suratul Ahzab

الآية : 3

وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِيلٗا

Ka kuma dogara ga Allah. Allah kuwa Ya isa wakili



السورة: Suratul Ahzab

الآية : 4

مَّا جَعَلَ ٱللَّهُ لِرَجُلٖ مِّن قَلۡبَيۡنِ فِي جَوۡفِهِۦۚ وَمَا جَعَلَ أَزۡوَٰجَكُمُ ٱلَّـٰٓـِٔي تُظَٰهِرُونَ مِنۡهُنَّ أُمَّهَٰتِكُمۡۚ وَمَا جَعَلَ أَدۡعِيَآءَكُمۡ أَبۡنَآءَكُمۡۚ ذَٰلِكُمۡ قَوۡلُكُم بِأَفۡوَٰهِكُمۡۖ وَٱللَّهُ يَقُولُ ٱلۡحَقَّ وَهُوَ يَهۡدِي ٱلسَّبِيلَ

Allah bai sanya wa wani mutum zuciya biyu ba a cikinsa. Kuma bai sanya matanku waxanda kuke yi musu zihari[1] (su zama) iyayenku ba. Bai kuma sanya ‘ya’yan riqonku (su zama) ‘ya’yanku ba[2]. Wannan magana ce da kuke yi da bakunanku; Allah kuwa Yana faxar gaskiya ne, kuma Shi ne Yake shiryarwa ga hanya (ta gaskiya)


1- Zihari, shi ne miji ya kwatanta matarsa da mahaifiyarsa wajen haramci. Wannan wata al’ada ce ta Larabawa a jahiliyya da Musulunci ya haramta ta.


2- Gabanin zuwa Musulunci Larabawa sukan mayar da ‘ya’yansu na riqo kamar ‘ya’yan da suka haifa wajen hukunce-hukunce. Sai Allah ya haramta aikata haka.


السورة: Suratul Ahzab

الآية : 5

ٱدۡعُوهُمۡ لِأٓبَآئِهِمۡ هُوَ أَقۡسَطُ عِندَ ٱللَّهِۚ فَإِن لَّمۡ تَعۡلَمُوٓاْ ءَابَآءَهُمۡ فَإِخۡوَٰنُكُمۡ فِي ٱلدِّينِ وَمَوَٰلِيكُمۡۚ وَلَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٞ فِيمَآ أَخۡطَأۡتُم بِهِۦ وَلَٰكِن مَّا تَعَمَّدَتۡ قُلُوبُكُمۡۚ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمًا

Ku danganta su (‘ya’yan riqo) ga iyayensu maza shi ne adalci a wurin Allah. Amma idan ba ku san iyayensu maza ba, to ‘yan’uwanku ne a addini, kuma bararrun bayinku ne. Babu kuma laifi a kanku game da abin da kuka yi kuskuren yin sa, sai dai abin da zukatanku suka yi gangancin (aikatawa). Allah kuwa Ya kasance Mai gafara ne, Mai jin qai



السورة: Suratul Ahzab

الآية : 6

ٱلنَّبِيُّ أَوۡلَىٰ بِٱلۡمُؤۡمِنِينَ مِنۡ أَنفُسِهِمۡۖ وَأَزۡوَٰجُهُۥٓ أُمَّهَٰتُهُمۡۗ وَأُوْلُواْ ٱلۡأَرۡحَامِ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلَىٰ بِبَعۡضٖ فِي كِتَٰبِ ٱللَّهِ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُهَٰجِرِينَ إِلَّآ أَن تَفۡعَلُوٓاْ إِلَىٰٓ أَوۡلِيَآئِكُم مَّعۡرُوفٗاۚ كَانَ ذَٰلِكَ فِي ٱلۡكِتَٰبِ مَسۡطُورٗا

Annabi shi ya fi cancanta ga muminai fiye da kansu[1]; matansa kuma iyayensu ne. Dangi na zumunta kuma shashinsu ya fi kusanci daga wani shashi[2] a cikin Littafin Allah daga kusancin muminai da masu hijira, sai dai idan za ku aikata wani alheri ne ga masoyanku (muminai). Wannan ya kasance a rubuce a cikin Lauhul Mahafuzu


1- Watau shi ya fi cancanta su qaunace shi fiye da kawunansu.


2- Watau dangi na zumunci su ne suka fi cancanta su ci gadon junansu.


السورة: Suratul Ahzab

الآية : 7

وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِنَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مِيثَٰقَهُمۡ وَمِنكَ وَمِن نُّوحٖ وَإِبۡرَٰهِيمَ وَمُوسَىٰ وَعِيسَى ٱبۡنِ مَرۡيَمَۖ وَأَخَذۡنَا مِنۡهُم مِّيثَٰقًا غَلِيظٗا

Kuma (ka tuna) lokacin da Muka riqi alqawura daga annabawa (na isar da aike), kuma daga gare ka, kuma daga Nuhu da Ibrahimu da Musa da Isa xan Maryamu; Muka kuma riqi alqawari mai kauri daga gare su



السورة: Suratul Ahzab

الآية : 8

لِّيَسۡـَٔلَ ٱلصَّـٰدِقِينَ عَن صِدۡقِهِمۡۚ وَأَعَدَّ لِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابًا أَلِيمٗا

Don (Allah) Ya tambayi masu gaskiya game da gaskiyarsu[1], Ya kuma tanadi azaba mai raxaxi ga kafirai


1- Watau ya tambati annabawa ko sun isar da saqon da ya aiko su da shi.


السورة: Suratul Ahzab

الآية : 9

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَةَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ إِذۡ جَآءَتۡكُمۡ جُنُودٞ فَأَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ رِيحٗا وَجُنُودٗا لَّمۡ تَرَوۡهَاۚ وَكَانَ ٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرًا

Ya ku waxanda suka yi imani, ku tuna ni’imar Allah a gare ku lokacin da wasu rundunoni (na gangankon kafurai) suka zo muku, sai Muka aiko musu iska da wasu rundunoni da ba ku gan su ba[1]. Allah kuwa Ya kasance Mai ganin abin da kuke aikatawa ne


1- Watau su ne rundunonin kafiran Quraishawa da qawayensu waxanda suka nufo Madina a shekara ta 5 don su yaqi Musulmi, amma Allah ya karya su.


السورة: Suratul Ahzab

الآية : 10

إِذۡ جَآءُوكُم مِّن فَوۡقِكُمۡ وَمِنۡ أَسۡفَلَ مِنكُمۡ وَإِذۡ زَاغَتِ ٱلۡأَبۡصَٰرُ وَبَلَغَتِ ٱلۡقُلُوبُ ٱلۡحَنَاجِرَ وَتَظُنُّونَ بِٱللَّهِ ٱلظُّنُونَا۠

A lokacin da suka zo muku ta samanku da qasanku, da kuma yayin da idanuwa suka kauce wa (ganin komai sai maqiya), zukatanku kuma suka cika da tsoro kuka riqa zace-zace game da Allah



السورة: Suratul Ahzab

الآية : 11

هُنَالِكَ ٱبۡتُلِيَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَزُلۡزِلُواْ زِلۡزَالٗا شَدِيدٗا

A nan ne fa aka jarrabi muminai, aka kuma girgiza su girgizawa mai tsanani



السورة: Suratul Ahzab

الآية : 12

وَإِذۡ يَقُولُ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ وَٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ مَّا وَعَدَنَا ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥٓ إِلَّا غُرُورٗا

Kuma (ka tuna) lokacin da munafukai da waxanda suke da cuta a zukatansu suke cewa: “Allah da Manzonsa ba wani alqawarin da suka yi mana sai na ruxi.”



السورة: Suratul Ahzab

الآية : 13

وَإِذۡ قَالَت طَّآئِفَةٞ مِّنۡهُمۡ يَـٰٓأَهۡلَ يَثۡرِبَ لَا مُقَامَ لَكُمۡ فَٱرۡجِعُواْۚ وَيَسۡتَـٔۡذِنُ فَرِيقٞ مِّنۡهُمُ ٱلنَّبِيَّ يَقُولُونَ إِنَّ بُيُوتَنَا عَوۡرَةٞ وَمَا هِيَ بِعَوۡرَةٍۖ إِن يُرِيدُونَ إِلَّا فِرَارٗا

Kuma (ka tuna) lokacin da wata jama’a daga cikinsu ta ce: “Ya ku mutanen Yasriba[1], ba ku da wurin zama, sai ku koma.” Wata qungiya kuma daga cikinsu tana neman izinin Annabi da cewa: “Lalle gidajenmu tsirara tuqwi suke,” alhali kuwa ba tsirara tuqwi suke ba; ba abin da suke nufi sai gudu


1- Yasrib, tsohon sunan Madina ne tun gabanin Musulunci. Annabi ya canja shi zuwa Madina.


السورة: Suratul Ahzab

الآية : 14

وَلَوۡ دُخِلَتۡ عَلَيۡهِم مِّنۡ أَقۡطَارِهَا ثُمَّ سُئِلُواْ ٱلۡفِتۡنَةَ لَأٓتَوۡهَا وَمَا تَلَبَّثُواْ بِهَآ إِلَّا يَسِيرٗا

Da kuwa za a shigo musu ta kowane vangare sannan a neme su da yin fitinar (komawa ga kafirci), to Wallahi da sun aikata (hakan) ba kuwa za su jinkirta da shi ba (wato kafircin) sai xan lokacin qanqani



السورة: Suratul Ahzab

الآية : 15

وَلَقَدۡ كَانُواْ عَٰهَدُواْ ٱللَّهَ مِن قَبۡلُ لَا يُوَلُّونَ ٱلۡأَدۡبَٰرَۚ وَكَانَ عَهۡدُ ٱللَّهِ مَسۡـُٔولٗا

Tun da can kuwa haqiqa sun yi wa Allah alqawarin (cewa) ba za su ba da baya ba. Alqawarin Allah kuwa ya kasance abin tambaya ne



السورة: Suratul Ahzab

الآية : 16

قُل لَّن يَنفَعَكُمُ ٱلۡفِرَارُ إِن فَرَرۡتُم مِّنَ ٱلۡمَوۡتِ أَوِ ٱلۡقَتۡلِ وَإِذٗا لَّا تُمَتَّعُونَ إِلَّا قَلِيلٗا

Ka ce: “In kuna guje wa mutuwa ne ko kisa, to gudun ba zai amfane ku ba, a yayin nan kuwa ba za a jiyar da ku wani daxi ba sai xan kaxan.”



السورة: Suratul Ahzab

الآية : 17

قُلۡ مَن ذَا ٱلَّذِي يَعۡصِمُكُم مِّنَ ٱللَّهِ إِنۡ أَرَادَ بِكُمۡ سُوٓءًا أَوۡ أَرَادَ بِكُمۡ رَحۡمَةٗۚ وَلَا يَجِدُونَ لَهُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ وَلِيّٗا وَلَا نَصِيرٗا

Ka ce: “Wane ne zai kare ku daga Allah idan Ya nufe ku da wani mummunan abu ko kuma Ya nufe ku da wata rahama?” Ba kuma za su sama wa kansu wani majivinci ko mai taimako ba in ba Allah ba