السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 24

۞قَٰلَ أَوَلَوۡ جِئۡتُكُم بِأَهۡدَىٰ مِمَّا وَجَدتُّمۡ عَلَيۡهِ ءَابَآءَكُمۡۖ قَالُوٓاْ إِنَّا بِمَآ أُرۡسِلۡتُم بِهِۦ كَٰفِرُونَ

Ya ce (da su: “Yanzu za ku yi koyi da su) ko da na zo muku da abin da ya fi zama shiriya a kan abin da kuka sami iyayenku a kansa?” Suka ce: “Lalle mu masu kafirce wa abin da aka aiko ku da shi ne.”



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 25

فَٱنتَقَمۡنَا مِنۡهُمۡۖ فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُكَذِّبِينَ

Sai Muka saka musu da azaba; to duba ka ga yadda qarshen masu qaryatawa ya kasance



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 26

وَإِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِيمُ لِأَبِيهِ وَقَوۡمِهِۦٓ إِنَّنِي بَرَآءٞ مِّمَّا تَعۡبُدُونَ

Kuma ka tuna lokacin da Ibrahimu ya ce da Babansa da mutanensa: “Lalle ni ba ruwana da abin da kuke bautawa



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 27

إِلَّا ٱلَّذِي فَطَرَنِي فَإِنَّهُۥ سَيَهۡدِينِ

“Sai dai wanda Ya halicce ni, to lalle Shi ne Zai shirye ni.”



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 28

وَجَعَلَهَا كَلِمَةَۢ بَاقِيَةٗ فِي عَقِبِهِۦ لَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ

Ya kuma sanya ta (kalmar Tauhidi ta zama) kalma ce mai wanzuwa a cikin zuri’arsa don (mutanen Makka) su komo (kan hanya).”



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 29

بَلۡ مَتَّعۡتُ هَـٰٓؤُلَآءِ وَءَابَآءَهُمۡ حَتَّىٰ جَآءَهُمُ ٱلۡحَقُّ وَرَسُولٞ مُّبِينٞ

A’a, Na jiyar da waxannan daxi tare da iyayensu ne har gaskiya ta zo musu da wani manzo mai bayyanawa



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 30

وَلَمَّا جَآءَهُمُ ٱلۡحَقُّ قَالُواْ هَٰذَا سِحۡرٞ وَإِنَّا بِهِۦ كَٰفِرُونَ

Yayin da gaskiyar ta zo musu sai suka ce: “Wannan sihiri ne, kuma lalle mu masu kafirce masa ne.”



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 31

وَقَالُواْ لَوۡلَا نُزِّلَ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانُ عَلَىٰ رَجُلٖ مِّنَ ٱلۡقَرۡيَتَيۡنِ عَظِيمٍ

Suka kuma ce: “Me ya hana a saukar da wannan Alqur’ani ga wani babban mutum, daga alqaryun nan guda biyu?”



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 32

أَهُمۡ يَقۡسِمُونَ رَحۡمَتَ رَبِّكَۚ نَحۡنُ قَسَمۡنَا بَيۡنَهُم مَّعِيشَتَهُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۚ وَرَفَعۡنَا بَعۡضَهُمۡ فَوۡقَ بَعۡضٖ دَرَجَٰتٖ لِّيَتَّخِذَ بَعۡضُهُم بَعۡضٗا سُخۡرِيّٗاۗ وَرَحۡمَتُ رَبِّكَ خَيۡرٞ مِّمَّا يَجۡمَعُونَ

Yanzu su ne suke raba rahamar Ubangijinka (ta annabci)? Mu ne Muka raba musu arzikinsu a rayuwar duniya. Muka kuma xaukaka darajojin sashinsu a kan sashi, don wani sashin ya riqi wani sashi mai yi masa hidima. Rahamar Ubangijinka kuma ita ta fi abin da suke tarawa (na duniya)



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 33

وَلَوۡلَآ أَن يَكُونَ ٱلنَّاسُ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ لَّجَعَلۡنَا لِمَن يَكۡفُرُ بِٱلرَّحۡمَٰنِ لِبُيُوتِهِمۡ سُقُفٗا مِّن فِضَّةٖ وَمَعَارِجَ عَلَيۡهَا يَظۡهَرُونَ

Ba don kuma kada mutane su zama iri xaya ba, da sai Mu sanya wa waxanda suke kafirce wa (Allah) Mai rahama rufi na azurfa a gidajensu, da kuma matattakala (irinta), da za su riqa hawa ta kansu



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 34

وَلِبُيُوتِهِمۡ أَبۡوَٰبٗا وَسُرُرًا عَلَيۡهَا يَتَّكِـُٔونَ

Kuma (Mu sanya wa) gidajen nasu qofofi da gadaje da za su riqa kishingixa a kansu



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 35

وَزُخۡرُفٗاۚ وَإِن كُلُّ ذَٰلِكَ لَمَّا مَتَٰعُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۚ وَٱلۡأٓخِرَةُ عِندَ رَبِّكَ لِلۡمُتَّقِينَ

Kuma (Mu sanya musu) zinariya. Duk waxannan ba komai ba ne sai xan jin daxin rayuwar duniya. Lahira kuma a wurin Ubangijinka ta masu taqawa ce



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 36

وَمَن يَعۡشُ عَن ذِكۡرِ ٱلرَّحۡمَٰنِ نُقَيِّضۡ لَهُۥ شَيۡطَٰنٗا فَهُوَ لَهُۥ قَرِينٞ

Wanda kuwa ya zama mai dundumi game da ambaton (Allah) Mai rahama, to za Mu haxa shi da Shaixan ya zama shi ne abokinsa



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 37

وَإِنَّهُمۡ لَيَصُدُّونَهُمۡ عَنِ ٱلسَّبِيلِ وَيَحۡسَبُونَ أَنَّهُم مُّهۡتَدُونَ

Lalle kuma su (shaixanun) tabbas suna kange su daga tafarki nagari, su kuma suna zato cewa lalle su shiryayyu ne



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 38

حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَنَا قَالَ يَٰلَيۡتَ بَيۡنِي وَبَيۡنَكَ بُعۡدَ ٱلۡمَشۡرِقَيۡنِ فَبِئۡسَ ٱلۡقَرِينُ

Har zuwa lokacin da suka zo mana (wato mutumin da shaixaninsa) sai ya ce: “Ina ma a ce tsakanina da kai akwai nisan gabas da yamma; to tir da aboki irinka.”



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 39

وَلَن يَنفَعَكُمُ ٱلۡيَوۡمَ إِذ ظَّلَمۡتُمۡ أَنَّكُمۡ فِي ٱلۡعَذَابِ مُشۡتَرِكُونَ

(Allah Ya ce da su): “A yau tun da kun riga kun yi zalunci zamantowarku tare a cikin azaba ba zai amfane ku ba



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 40

أَفَأَنتَ تُسۡمِعُ ٱلصُّمَّ أَوۡ تَهۡدِي ٱلۡعُمۡيَ وَمَن كَانَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ

Yanzu kai ka iya jiyar da kurame, ko kuma ka iya shiryar da makafi da wanda ya kasance cikin vata mabayyani?



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 41

فَإِمَّا نَذۡهَبَنَّ بِكَ فَإِنَّا مِنۡهُم مُّنتَقِمُونَ

To idan Muka karvi ranka, to lalle Mu Masu yi musu uquba ne



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 42

أَوۡ نُرِيَنَّكَ ٱلَّذِي وَعَدۡنَٰهُمۡ فَإِنَّا عَلَيۡهِم مُّقۡتَدِرُونَ

Ko kuma Muka nuna maka irin abin da muka yi musu alqawarin narko da shi, to lalle Mu Masu iko ne a kansu



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 43

فَٱسۡتَمۡسِكۡ بِٱلَّذِيٓ أُوحِيَ إِلَيۡكَۖ إِنَّكَ عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

To ka riqe abin da aka yi maka wahayinsa; lalle kai kana kan hanya madaidaiciya



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 44

وَإِنَّهُۥ لَذِكۡرٞ لَّكَ وَلِقَوۡمِكَۖ وَسَوۡفَ تُسۡـَٔلُونَ

Kuma lalle shi (Alqur’ani) xaukaka ce a gare ka da mutanenka; ba da daxewa ba kuma za a tambaye ku (game da haqqinsa)



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 45

وَسۡـَٔلۡ مَنۡ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ مِن رُّسُلِنَآ أَجَعَلۡنَا مِن دُونِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ءَالِهَةٗ يُعۡبَدُونَ

Ka tambayi waxanda Muka aiko gabaninka daga manzanninmu, shin Mun sanya wasu ababen bauta da ake bauta musu ba (Allah) Mai rahama ba?



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 46

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَآ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ فَقَالَ إِنِّي رَسُولُ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Haqiqa kuma Mun aiko Musa da ayoyinmu zuwa ga Fir’auna da manyan fadawansa, sai ya ce: “Lalle ni Manzo ne na Ubangijin talikai.”



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 47

فَلَمَّا جَآءَهُم بِـَٔايَٰتِنَآ إِذَا هُم مِّنۡهَا يَضۡحَكُونَ

To lokacin da ya zo musu da ayoyinmu sai ga su suna yi musu dariya



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 48

وَمَا نُرِيهِم مِّنۡ ءَايَةٍ إِلَّا هِيَ أَكۡبَرُ مِنۡ أُخۡتِهَاۖ وَأَخَذۡنَٰهُم بِٱلۡعَذَابِ لَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ

Ba Mu kuma nuna musu wata aya ba sai wadda take ta fi `yar’uwarta girma; Muka kuma kama su da azaba don su dawo (kan hanya)



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 49

وَقَالُواْ يَـٰٓأَيُّهَ ٱلسَّاحِرُ ٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ بِمَا عَهِدَ عِندَكَ إِنَّنَا لَمُهۡتَدُونَ

Suka kuma ce: “Ya kai wannan mai sihiri, ka roqa mana Ubangijinka da abin da Ya yi maka wahayinsa (Ya yaye mana azaba), lalle mu tabbas za mu shiriya.”



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 50

فَلَمَّا كَشَفۡنَا عَنۡهُمُ ٱلۡعَذَابَ إِذَا هُمۡ يَنكُثُونَ

To lokacin da Muka yaye musu azabar sai ga su suna warware alqawari



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 51

وَنَادَىٰ فِرۡعَوۡنُ فِي قَوۡمِهِۦ قَالَ يَٰقَوۡمِ أَلَيۡسَ لِي مُلۡكُ مِصۡرَ وَهَٰذِهِ ٱلۡأَنۡهَٰرُ تَجۡرِي مِن تَحۡتِيٓۚ أَفَلَا تُبۡصِرُونَ

Fir’auna kuma ya yi shela a cikin mutanensa ya ce: “Ya ku mutanena, yanzu mulkin Misra ba nawa ba ne, kuma ga qoramu suna ta kwarara ta qarqashina, ko ba kwa gani ne?



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 52

أَمۡ أَنَا۠ خَيۡرٞ مِّنۡ هَٰذَا ٱلَّذِي هُوَ مَهِينٞ وَلَا يَكَادُ يُبِينُ

“A’a, ni na fi wannan wulaqantaccen wanda da qyar yake iya bayani



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 53

فَلَوۡلَآ أُلۡقِيَ عَلَيۡهِ أَسۡوِرَةٞ مِّن ذَهَبٍ أَوۡ جَآءَ مَعَهُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ مُقۡتَرِنِينَ

“To me ya hana a saukar masa da warawarai na zinare, ko kuma wasu mala’iku su zo tare da shi suna masu dafa masa baya?”