نٓۚ وَٱلۡقَلَمِ وَمَا يَسۡطُرُونَ
NUN[1]. (Allah ya ce): Na rantse da alqalami da abin da (mala’iku) suke rubutawa
1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.
مَآ أَنتَ بِنِعۡمَةِ رَبِّكَ بِمَجۡنُونٖ
Kai ba mahaukaci ba ne saboda ni’imar Ubangijinka
وَإِنَّ لَكَ لَأَجۡرًا غَيۡرَ مَمۡنُونٖ
Kuma lalle tabbas kana da lada marar yankewa
وَإِنَّكَ لَعَلَىٰ خُلُقٍ عَظِيمٖ
Lalle kuma kai kana kan halaye masu girma
فَسَتُبۡصِرُ وَيُبۡصِرُونَ
To ba da daxewa ba za ka gani, su ma kuma su gani
بِأَييِّكُمُ ٱلۡمَفۡتُونُ
Wane ne daga cikinku mahaukaci?
إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِٱلۡمُهۡتَدِينَ
Lalle Ubangijinka Shi Ya fi sanin wanda ya kauce wa hanyarsa kuma Shi Ya fi sanin shiryayyu
فَلَا تُطِعِ ٱلۡمُكَذِّبِينَ
Saboda haka kada ka bi masu qaryatawa
وَدُّواْ لَوۡ تُدۡهِنُ فَيُدۡهِنُونَ
Sun yi burin da za ka sassauto, sai su ma su sassauto[1]
1- Watau ya daina aibata gumakansu da bautarsu, sai su ma su daina sukan sa da addininsa.
وَلَا تُطِعۡ كُلَّ حَلَّافٖ مَّهِينٍ
Kada kuma ka bi duk wani mai yawan rantsuwa, wulaqantacce
هَمَّازٖ مَّشَّآءِۭ بِنَمِيمٖ
Mai yawan yin zunxe, mai yawan yawo da annamimanci
مَّنَّاعٖ لِّلۡخَيۡرِ مُعۡتَدٍ أَثِيمٍ
Mai yawan hana alheri, mai ta’addanci, mai yawan savo
عُتُلِّۭ بَعۡدَ ذَٰلِكَ زَنِيمٍ
Mai busasshiyar zuciya, bayan wannan kuma marar asali ne
أَن كَانَ ذَا مَالٖ وَبَنِينَ
Don ya kasance mai dukiya da ‘ya’ya
إِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِ ءَايَٰتُنَا قَالَ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Idan ana karanta masa ayoyinmu sai ya ce: “Tatsuniyoyin mutanen farko ne.”
سَنَسِمُهُۥ عَلَى ٱلۡخُرۡطُومِ
Ba da daxewa ba za Mu yi masa alama a kan hancinsa
إِنَّا بَلَوۡنَٰهُمۡ كَمَا بَلَوۡنَآ أَصۡحَٰبَ ٱلۡجَنَّةِ إِذۡ أَقۡسَمُواْ لَيَصۡرِمُنَّهَا مُصۡبِحِينَ
Lalle Mu Mun jarrabe su (wato mutanen Makka) kamar yadda Muka jarrabi ma’abota gona, lokacin da suka rantse cewa, lalle tabbas za su girbe ta da asussuba
وَلَا يَسۡتَثۡنُونَ
Ba sa kuma togaciya (da faxar insha Allah)
فَطَافَ عَلَيۡهَا طَآئِفٞ مِّن رَّبِّكَ وَهُمۡ نَآئِمُونَ
Sai wani bala’i daga Ubangijinka ya kewaye ta alhali su suna bacci
فَأَصۡبَحَتۡ كَٱلصَّرِيمِ
Sai ta wayi gari (baqi qirin) kamar duhun dare
فَتَنَادَوۡاْ مُصۡبِحِينَ
Sai suka kirawo junansu da asussuba
أَنِ ٱغۡدُواْ عَلَىٰ حَرۡثِكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰرِمِينَ
Cewa: “Ku yi sammako ga amfanin gonarku idan kun kasance masu yin girbi.”
فَٱنطَلَقُواْ وَهُمۡ يَتَخَٰفَتُونَ
Sai suka tafi alhali suna yi wa junansu raxa
أَن لَّا يَدۡخُلَنَّهَا ٱلۡيَوۡمَ عَلَيۡكُم مِّسۡكِينٞ
Cewa: “Lalle a yau kada wani miskini ya shigar muku cikinta.”
وَغَدَوۡاْ عَلَىٰ حَرۡدٖ قَٰدِرِينَ
Suka kuwa yi sammako suna masu zaton su masu iko ne a kan hana (mabuqata)
فَلَمَّا رَأَوۡهَا قَالُوٓاْ إِنَّا لَضَآلُّونَ
To lokacin da suka gan ta sai suka ce: “Lalle mu tabbas mun yi vatan kai
بَلۡ نَحۡنُ مَحۡرُومُونَ
“A’a, mu dai an hana mu ne kawai.”
قَالَ أَوۡسَطُهُمۡ أَلَمۡ أَقُل لَّكُمۡ لَوۡلَا تُسَبِّحُونَ
Sai wanda ya fi su kirki ya ce: “Ban gaya muku ya kamata ku tsarkake Allah ba?”
قَالُواْ سُبۡحَٰنَ رَبِّنَآ إِنَّا كُنَّا ظَٰلِمِينَ
Suka ce, “Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu, lalle mu mun kasance azzalumai.”
فَأَقۡبَلَ بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ يَتَلَٰوَمُونَ
Sai sashinsu ya fuskanci sashi suna zargin juna