وَمَا جَعَلۡنَآ أَصۡحَٰبَ ٱلنَّارِ إِلَّا مَلَـٰٓئِكَةٗۖ وَمَا جَعَلۡنَا عِدَّتَهُمۡ إِلَّا فِتۡنَةٗ لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ لِيَسۡتَيۡقِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَيَزۡدَادَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِيمَٰنٗا وَلَا يَرۡتَابَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَلِيَقُولَ ٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ وَٱلۡكَٰفِرُونَ مَاذَآ أَرَادَ ٱللَّهُ بِهَٰذَا مَثَلٗاۚ كَذَٰلِكَ يُضِلُّ ٱللَّهُ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُۚ وَمَا يَعۡلَمُ جُنُودَ رَبِّكَ إِلَّا هُوَۚ وَمَا هِيَ إِلَّا ذِكۡرَىٰ لِلۡبَشَرِ
Ba Mu kuwa sanya masu tsaron wutar ba sai mala’iku, ba Mu kuma sanya adadinsu ba sai don fitina ga waxanda suka kafirta, don kuma waxanda aka bai wa littafi su sami yaqini, waxanda kuma suka yi imani su qara imani, waxanda aka bai wa littafi da muminai kuma kada su yi tababa, don kuma waxanda suke da raunin imani a zukatansu da kuma kafirai su ce: “Me Allah Yake nufi da yin misali da wannan (adadin)?” Kamar haka Allah Yake vatar da wanda Ya ga dama, Yake kuma shiryar da wanda Ya ga dama. Ba kuma wanda ya san (yawan) rundunar Ubangijinka sai Shi. Ita (Saqara) kuma ba wata abu ba ce face wa’azi ga mutane
كَلَّا وَٱلۡقَمَرِ
A’a. Na rantse da wata
وَٱلَّيۡلِ إِذۡ أَدۡبَرَ
Da kuma dare idan ya ba da baya
وَٱلصُّبۡحِ إِذَآ أَسۡفَرَ
Da kuma asuba idan ta bayyana (da haskenta)
إِنَّهَا لَإِحۡدَى ٱلۡكُبَرِ
Lalle ita (Saqara) tana xaya daga manya-manyan (bala’o’i)
نَذِيرٗا لِّلۡبَشَرِ
Gargaxi ce ga mutane
لِمَن شَآءَ مِنكُمۡ أَن يَتَقَدَّمَ أَوۡ يَتَأَخَّرَ
Ga wanda ya ga dama daga cikinku, ya ci gaba ko ya ci baya
كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا كَسَبَتۡ رَهِينَةٌ
Kowane rai jingina ne ga abin da ya tsuwurwurta[1]
1- Watau jingina ne ga ayyukansu, ko dai su hallakar da shi ko su kuvutar da shi, su ‘yanta shi.
إِلَّآ أَصۡحَٰبَ ٱلۡيَمِينِ
Sai dai ga ma’abota dama[1]
1- Watau waxanda za su karvi littattafan ayyukansu ta hannayensu na dama.
فِي جَنَّـٰتٖ يَتَسَآءَلُونَ
(Su kam suna) cikin gidajen Aljanna suna tambayar juna
عَنِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ
Game da manyan masu laifuka
مَا سَلَكَكُمۡ فِي سَقَرَ
(Suna cewa): “Me ya shigar da ku cikin Saqara?”
قَالُواْ لَمۡ نَكُ مِنَ ٱلۡمُصَلِّينَ
Suka ce: “Ba mu zama daga cikin masallata ba
وَلَمۡ نَكُ نُطۡعِمُ ٱلۡمِسۡكِينَ
“Kuma ba mu kasance muna ciyar da miskini ba
وَكُنَّا نَخُوضُ مَعَ ٱلۡخَآئِضِينَ
“Mun kuma kasance muna kutsawa (cikin varna)[1] tare da masu kutsawa
1- Watau suna faxar qarerayi game da Annabi () da Alqur’ani.
وَكُنَّا نُكَذِّبُ بِيَوۡمِ ٱلدِّينِ
“Kuma mun kasance muna qaryata ranar sakamako
حَتَّىٰٓ أَتَىٰنَا ٱلۡيَقِينُ
“Har mutuwa ta zo mana.”
فَمَا تَنفَعُهُمۡ شَفَٰعَةُ ٱلشَّـٰفِعِينَ
Saboda haka ceton masu ceto ba zai amfane su ba
فَمَا لَهُمۡ عَنِ ٱلتَّذۡكِرَةِ مُعۡرِضِينَ
To me ya same su ne suke bijire wa wa’azi?
كَأَنَّهُمۡ حُمُرٞ مُّسۡتَنفِرَةٞ
Kai ka ce su jakunan jeji ne da aka firgitar
فَرَّتۡ مِن قَسۡوَرَةِۭ
Da suka guje wa zaki
بَلۡ يُرِيدُ كُلُّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُمۡ أَن يُؤۡتَىٰ صُحُفٗا مُّنَشَّرَةٗ
A’a, kowane mutum daga cikinsu yana so ne a ba shi takardu buxaxxu[1] (kafin su bi Annabi)
1- Watau a ba shi buxaxxen littafi wanda zai ba shi labari cewa Annabi Muhammadu () Manzon Allah ne.
كَلَّاۖ بَل لَّا يَخَافُونَ ٱلۡأٓخِرَةَ
Faufau! A’a, su dai ba sa tsoron ranar lahira ne
كَلَّآ إِنَّهُۥ تَذۡكِرَةٞ
Tabbas, lalle shi (Alqur’ani) wa’azi ne
فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ
To duk wanda ya ga dama sai ya wa’azantu
وَمَا يَذۡكُرُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُۚ هُوَ أَهۡلُ ٱلتَّقۡوَىٰ وَأَهۡلُ ٱلۡمَغۡفِرَةِ
Ba sa kuma wa’azantuwa sai idan Allah Ya ga dama. Shi ne Ya cancanci taqawa, kuma Shi ne Ya cancanci yin gafara