السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 31

قُل لِّعِبَادِيَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ يُقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُنفِقُواْ مِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ سِرّٗا وَعَلَانِيَةٗ مِّن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَ يَوۡمٞ لَّا بَيۡعٞ فِيهِ وَلَا خِلَٰلٌ

Ka ce da bayina waxanda suka yi imani, su tsayar da salla kuma su ciyar daga abin da Muka arzuta su da shi, a voye da sarari tun kafin zuwan ranar da babu ciniki a cikinta, kuma babu abota



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 32

ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجَ بِهِۦ مِنَ ٱلثَّمَرَٰتِ رِزۡقٗا لَّكُمۡۖ وَسَخَّرَ لَكُمُ ٱلۡفُلۡكَ لِتَجۡرِيَ فِي ٱلۡبَحۡرِ بِأَمۡرِهِۦۖ وَسَخَّرَ لَكُمُ ٱلۡأَنۡهَٰرَ

Allah ne Wanda Ya halicci sammai da qasa, Ya kuma saukar da ruwa daga sama, sai Ya fitar da ‘ya’yan itace don arzuta ku; Ya kuma hore muku jiragen ruwa don ku yi tafiya a cikin kogi da umarninsa, Ya kuma hore muku qoramu



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 33

وَسَخَّرَ لَكُمُ ٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَ دَآئِبَيۡنِۖ وَسَخَّرَ لَكُمُ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ

Ya kuma hore muku rana da wata tutur; Ya kuma hore muku dare da rana



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 34

وَءَاتَىٰكُم مِّن كُلِّ مَا سَأَلۡتُمُوهُۚ وَإِن تَعُدُّواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ لَا تُحۡصُوهَآۗ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَظَلُومٞ كَفَّارٞ

Ya kuma ba ku daga duk abin da kuka roqe Shi. In da za ku qirga ni’imomin Allah to ba za ku iya qididdige su ba. Lalle mutum mai yawan zalunci ne mai yawan butulci



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 35

وَإِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِيمُ رَبِّ ٱجۡعَلۡ هَٰذَا ٱلۡبَلَدَ ءَامِنٗا وَٱجۡنُبۡنِي وَبَنِيَّ أَن نَّعۡبُدَ ٱلۡأَصۡنَامَ

(Ka tuna) kuma lokacin da Ibrahimu ya ce: “Ya Ubangijina, Ka sanya wannan gari (Makka) ya zama amintacce, kuma Ka nesantar da ni da ‘ya’yana daga bauta wa gumaka



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 36

رَبِّ إِنَّهُنَّ أَضۡلَلۡنَ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلنَّاسِۖ فَمَن تَبِعَنِي فَإِنَّهُۥ مِنِّيۖ وَمَنۡ عَصَانِي فَإِنَّكَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

“Ya Ubangijina, lalle su (gumakan) sun vatar da mutane masu yawa; wanda kuwa ya bi ni to lalle shi yana tare da ni; wanda kuma ya sava mini to lalle Kai Mai gafara ne, Mai jin qai.”



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 37

رَّبَّنَآ إِنِّيٓ أَسۡكَنتُ مِن ذُرِّيَّتِي بِوَادٍ غَيۡرِ ذِي زَرۡعٍ عِندَ بَيۡتِكَ ٱلۡمُحَرَّمِ رَبَّنَا لِيُقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ فَٱجۡعَلۡ أَفۡـِٔدَةٗ مِّنَ ٱلنَّاسِ تَهۡوِيٓ إِلَيۡهِمۡ وَٱرۡزُقۡهُم مِّنَ ٱلثَّمَرَٰتِ لَعَلَّهُمۡ يَشۡكُرُونَ

“Ya Ubangijinmu, lalle ni na zaunar da wasu daga zuriyata a wani kwari wanda ba a shuka a cikinsa[1] kusa da Xakinka mai alfarma; ya Ubangijinmu don su tsai da salla, to Ka sanya zukatan mutane su riqa karkatowa zuwa gare su, kuma Ka arzuta su da ‘ya’yan itace don su gode (maka)


1- Watau kuyangarsa Hajara () da xansa Isma’ilu (). Ya zaunar da su garin Makka da izinin Allah ().


السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 38

رَبَّنَآ إِنَّكَ تَعۡلَمُ مَا نُخۡفِي وَمَا نُعۡلِنُۗ وَمَا يَخۡفَىٰ عَلَى ٱللَّهِ مِن شَيۡءٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا فِي ٱلسَّمَآءِ

“Ya Ubangijinmu, lalle Kai Ka san abin da muke voyewa da abin da muke bayyanawa. Babu wani abu a cikin qasa ko a cikin sama da zai vuya ga Allah



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 39

ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي وَهَبَ لِي عَلَى ٱلۡكِبَرِ إِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَۚ إِنَّ رَبِّي لَسَمِيعُ ٱلدُّعَآءِ

“Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda Ya ba ni Isma’ila da Is’haqa a cikin halin tsufa. Lalle Ubangijina tabbas Mai jin roqo ne



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 40

رَبِّ ٱجۡعَلۡنِي مُقِيمَ ٱلصَّلَوٰةِ وَمِن ذُرِّيَّتِيۚ رَبَّنَا وَتَقَبَّلۡ دُعَآءِ

“Ya Ubangijina, Ka sanya ni in zama mai tsayar da salla da kuma zuriyata. Ya Ubangijinmu, Ka karvi addu’ata



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 41

رَبَّنَا ٱغۡفِرۡ لِي وَلِوَٰلِدَيَّ وَلِلۡمُؤۡمِنِينَ يَوۡمَ يَقُومُ ٱلۡحِسَابُ

“Ya Ubangijinmu Ka gafarta mini, ni da iyayena da kuma muminai ranar da hisabi zai kankama.”



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 42

وَلَا تَحۡسَبَنَّ ٱللَّهَ غَٰفِلًا عَمَّا يَعۡمَلُ ٱلظَّـٰلِمُونَۚ إِنَّمَا يُؤَخِّرُهُمۡ لِيَوۡمٖ تَشۡخَصُ فِيهِ ٱلۡأَبۡصَٰرُ

Kada ka yi tsammanin Allah ba Shi da masaniyar abin da azzalumai suke aikatawa. Yana dai saurara musu ne kawai zuwa ranar da idanuwa za su fito zuru-zuru



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 43

مُهۡطِعِينَ مُقۡنِعِي رُءُوسِهِمۡ لَا يَرۡتَدُّ إِلَيۡهِمۡ طَرۡفُهُمۡۖ وَأَفۡـِٔدَتُهُمۡ هَوَآءٞ

Suna masu gaggawa masu xage da kawunansu sama ba sa qiftawa; zukatansu kuma fanko ne (don tsananin firgita)



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 44

وَأَنذِرِ ٱلنَّاسَ يَوۡمَ يَأۡتِيهِمُ ٱلۡعَذَابُ فَيَقُولُ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ رَبَّنَآ أَخِّرۡنَآ إِلَىٰٓ أَجَلٖ قَرِيبٖ نُّجِبۡ دَعۡوَتَكَ وَنَتَّبِعِ ٱلرُّسُلَۗ أَوَلَمۡ تَكُونُوٓاْ أَقۡسَمۡتُم مِّن قَبۡلُ مَا لَكُم مِّن زَوَالٖ

Kuma ka gargaxi mutane game da ranar da azaba za ta zo musu, sai waxanda suka yi kafirci su ce: “Ya Ubangijinmu, Ka saurara mana zuwa xan lokaci qanqani, za mu amsa kiranka kuma mu bi manzanni.” (Sai a ce da su): “A da ba ku ne kuka yi rantsuwa ba cewa ba za ku gushe ba?



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 45

وَسَكَنتُمۡ فِي مَسَٰكِنِ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ وَتَبَيَّنَ لَكُمۡ كَيۡفَ فَعَلۡنَا بِهِمۡ وَضَرَبۡنَا لَكُمُ ٱلۡأَمۡثَالَ

“Kuka kuma zauna a gidajen waxanda suka zalunci kawunansu, kuma irin yadda Muka yi musu ya bayyana a gare ku, Muka kuma ba ku misalai!”



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 46

وَقَدۡ مَكَرُواْ مَكۡرَهُمۡ وَعِندَ ٱللَّهِ مَكۡرُهُمۡ وَإِن كَانَ مَكۡرُهُمۡ لِتَزُولَ مِنۡهُ ٱلۡجِبَالُ

Haqiqa kuma sun shirya makircinsu, sakamakon makircinsu kuma yana wurin Allah, ko da kuwa duwatsu za su gushe don makircinsu



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 47

فَلَا تَحۡسَبَنَّ ٱللَّهَ مُخۡلِفَ وَعۡدِهِۦ رُسُلَهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٞ ذُو ٱنتِقَامٖ

To kada ka yi tsammanin Allah Mai sava wa manzanninsa alqawarinsa ne. Lalle Allah Mabuwayi ne Ma’abocin uquba



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 48

يَوۡمَ تُبَدَّلُ ٱلۡأَرۡضُ غَيۡرَ ٱلۡأَرۡضِ وَٱلسَّمَٰوَٰتُۖ وَبَرَزُواْ لِلَّهِ ٱلۡوَٰحِدِ ٱلۡقَهَّارِ

(Ka tuna) ranar da za a sake qasa ba (wannan) qasar ba, da kuma sammai (ba waxannan samman ba. Halittu) kuma suka fito (daga cikin qasa) a gaban Allah Makaxaici, Mai rinjaye



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 49

وَتَرَى ٱلۡمُجۡرِمِينَ يَوۡمَئِذٖ مُّقَرَّنِينَ فِي ٱلۡأَصۡفَادِ

Kuma za ka ga masu laifi a wannan ranar a ququmce cikin maruruwa



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 50

سَرَابِيلُهُم مِّن قَطِرَانٖ وَتَغۡشَىٰ وُجُوهَهُمُ ٱلنَّارُ

Rigunansu na (tafasasshen) man qaxiran ne[1], kuma wuta za ta lulluve fuskokinsu


1- Qaxiran, wani baqin mai ne kamar kwalta, mai saurin kamawa da wuta, mai kuma xan karen wari.


السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 51

لِيَجۡزِيَ ٱللَّهُ كُلَّ نَفۡسٖ مَّا كَسَبَتۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

(An yi musu haka ne) don Allah Ya saka wa kowanne rai da gwargwadon abin da ya aikata. Lalle Allah Mai saurin hisabi ne



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 52

هَٰذَا بَلَٰغٞ لِّلنَّاسِ وَلِيُنذَرُواْ بِهِۦ وَلِيَعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَا هُوَ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞ وَلِيَذَّكَّرَ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ

Wannan (Alqur’ani) saqo ne ga mutane don kuma a gargaxe su da shi, kuma su san cewa Shi Allah Xaya ne, don kuma ma’abota hankali su wa’azantu