السورة: Suratu Hud

الآية : 31

وَلَآ أَقُولُ لَكُمۡ عِندِي خَزَآئِنُ ٱللَّهِ وَلَآ أَعۡلَمُ ٱلۡغَيۡبَ وَلَآ أَقُولُ إِنِّي مَلَكٞ وَلَآ أَقُولُ لِلَّذِينَ تَزۡدَرِيٓ أَعۡيُنُكُمۡ لَن يُؤۡتِيَهُمُ ٱللَّهُ خَيۡرًاۖ ٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا فِيٓ أَنفُسِهِمۡ إِنِّيٓ إِذٗا لَّمِنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

“Ba kuma zan ce da ku ina da taskokin Allah ba, ban kuma san gaibu ba, kuma ba zan ce lalle ni mala’ika ne ba, ba kuma zan ce wa waxanda idanuwanku suke wulaqantawa, Allah ba zai ba su wani alheri ba. Allah ne Ya fi sanin abin da yake zukatansu. Idan na yi haka, to lalle na zamanto daga cikin azzalumai.”



السورة: Suratu Hud

الآية : 32

قَالُواْ يَٰنُوحُ قَدۡ جَٰدَلۡتَنَا فَأَكۡثَرۡتَ جِدَٰلَنَا فَأۡتِنَا بِمَا تَعِدُنَآ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ

Suka ce: “Ya Nuhu, haqiqa ka ja da mu, ka kuma yawaita jayayya da mu; to sai ka zo mana da abin da kake yi mana alqawari da shi (na narko) in ka zamo daga masu gaskiya.”



السورة: Suratu Hud

الآية : 33

قَالَ إِنَّمَا يَأۡتِيكُم بِهِ ٱللَّهُ إِن شَآءَ وَمَآ أَنتُم بِمُعۡجِزِينَ

Ya ce: “Ai Allah ne zai zo muku da shi idan Ya ga dama, ku kuma ba za ku gagara ba



السورة: Suratu Hud

الآية : 34

وَلَا يَنفَعُكُمۡ نُصۡحِيٓ إِنۡ أَرَدتُّ أَنۡ أَنصَحَ لَكُمۡ إِن كَانَ ٱللَّهُ يُرِيدُ أَن يُغۡوِيَكُمۡۚ هُوَ رَبُّكُمۡ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

“Nasihata kuma ba za ta amfane ku ba - ko da na yi nufin yi muku nasihar - idan har da ma can Allah Yana nufin Ya vatar da ku. Shi ne Ubangijinku, kuma wurinsa za ku koma.”



السورة: Suratu Hud

الآية : 35

أَمۡ يَقُولُونَ ٱفۡتَرَىٰهُۖ قُلۡ إِنِ ٱفۡتَرَيۡتُهُۥ فَعَلَيَّ إِجۡرَامِي وَأَنَا۠ بَرِيٓءٞ مِّمَّا تُجۡرِمُونَ

A’a, ko dai cewa suke: “Qagar sa ya yi?” (wato Alqur’ani) Ka ce: “Idan qagar sa na yi, to alhakin qagena yana kaina ne, ni kuma ba ruwana da laifin abin da kuke tabkawa.”



السورة: Suratu Hud

الآية : 36

وَأُوحِيَ إِلَىٰ نُوحٍ أَنَّهُۥ لَن يُؤۡمِنَ مِن قَوۡمِكَ إِلَّا مَن قَدۡ ءَامَنَ فَلَا تَبۡتَئِسۡ بِمَا كَانُواْ يَفۡعَلُونَ

Aka kuma yi wa Nuhu wahayi cewa: “Ba wanda zai yi imani daga mutanenka sai waxanda suka riga suka yi. To kada ka yi baqin ciki game da abin da suke aikatawa



السورة: Suratu Hud

الآية : 37

وَٱصۡنَعِ ٱلۡفُلۡكَ بِأَعۡيُنِنَا وَوَحۡيِنَا وَلَا تُخَٰطِبۡنِي فِي ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ إِنَّهُم مُّغۡرَقُونَ

“Ka kuma sassaqa jirgin ruwa a kan idanunmu da koyarwarmu. Kada kuma ka yi Mini maganar komai game da kafirai. Lalle su nutsar da su za a yi.”



السورة: Suratu Hud

الآية : 38

وَيَصۡنَعُ ٱلۡفُلۡكَ وَكُلَّمَا مَرَّ عَلَيۡهِ مَلَأٞ مِّن قَوۡمِهِۦ سَخِرُواْ مِنۡهُۚ قَالَ إِن تَسۡخَرُواْ مِنَّا فَإِنَّا نَسۡخَرُ مِنكُمۡ كَمَا تَسۡخَرُونَ

Ya kuma riqa sassaqa jirgin, duk sanda kuma wasu manya daga mutanensa suka wuce ta wajensa sai su riqa yi masa ba’a. Ya ce: “Idan kun yi mana ba’a, to lalle mu ma fa (wata rana) za mu yi muku ba’ar kamar yadda kuke mana (yanzu)



السورة: Suratu Hud

الآية : 39

فَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ مَن يَأۡتِيهِ عَذَابٞ يُخۡزِيهِ وَيَحِلُّ عَلَيۡهِ عَذَابٞ مُّقِيمٌ

“To ba da daxewa ba za ku san wanda azaba mai kunyatarwa za ta zo masa, kuma wata azaba madawwamiya ta sauka a kansa.”



السورة: Suratu Hud

الآية : 40

حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَ أَمۡرُنَا وَفَارَ ٱلتَّنُّورُ قُلۡنَا ٱحۡمِلۡ فِيهَا مِن كُلّٖ زَوۡجَيۡنِ ٱثۡنَيۡنِ وَأَهۡلَكَ إِلَّا مَن سَبَقَ عَلَيۡهِ ٱلۡقَوۡلُ وَمَنۡ ءَامَنَۚ وَمَآ ءَامَنَ مَعَهُۥٓ إِلَّا قَلِيلٞ

Har dai zuwa lokacin da umarninmu ya zo, kuma tanderu ya vuvvugo da ruwa, Muka ce: “Ka xauki ma’aurata bibbiyu daga kowace (halitta) a cikinsa (jirgin) haxe da iyalanka in ban da wanda maganar (halakar da shi) ta gabata a kansa, kuma (ka xauki) waxanda suka yi imani.” Ba kuwa waxanda suka yi imani da shi sai ‘yan tsirari



السورة: Suratu Hud

الآية : 41

۞وَقَالَ ٱرۡكَبُواْ فِيهَا بِسۡمِ ٱللَّهِ مَجۡرٜىٰهَا وَمُرۡسَىٰهَآۚ إِنَّ رَبِّي لَغَفُورٞ رَّحِيمٞ

Ya kuma ce: “Ku shiga cikinsa, da sunan Allah ne tafiyarsa da kuma tsayawarsa. Lalle Ubangijina Mai gafara ne, Mai rahama.”



السورة: Suratu Hud

الآية : 42

وَهِيَ تَجۡرِي بِهِمۡ فِي مَوۡجٖ كَٱلۡجِبَالِ وَنَادَىٰ نُوحٌ ٱبۡنَهُۥ وَكَانَ فِي مَعۡزِلٖ يَٰبُنَيَّ ٱرۡكَب مَّعَنَا وَلَا تَكُن مَّعَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Shi kuma (jirgin) yana tafiya da su cikin raquman ruwa kamar duwatsu, Nuhu kuwa sai ya kirawo xansa alhalin ya kasance a ware waje xaya (ya ce): “Kai xana, ka hawo mana tare da mu, kada ka zama tare da kafirai.”



السورة: Suratu Hud

الآية : 43

قَالَ سَـَٔاوِيٓ إِلَىٰ جَبَلٖ يَعۡصِمُنِي مِنَ ٱلۡمَآءِۚ قَالَ لَا عَاصِمَ ٱلۡيَوۡمَ مِنۡ أَمۡرِ ٱللَّهِ إِلَّا مَن رَّحِمَۚ وَحَالَ بَيۡنَهُمَا ٱلۡمَوۡجُ فَكَانَ مِنَ ٱلۡمُغۡرَقِينَ

(Xan) ya ce: “Ai zan fake a wani dutse wanda zai kare ni daga ruwan.” (Annabi Nuhu) ya ce: “Yau kam babu mai kariya daga al’amarin Allah sai dai wanda Ya yi wa rahama kawai.” Sai raqumin ruwa ya shiga tsakaninsu, ya zamanto cikin waxanda aka nutsar (a cikin ruwa)



السورة: Suratu Hud

الآية : 44

وَقِيلَ يَـٰٓأَرۡضُ ٱبۡلَعِي مَآءَكِ وَيَٰسَمَآءُ أَقۡلِعِي وَغِيضَ ٱلۡمَآءُ وَقُضِيَ ٱلۡأَمۡرُ وَٱسۡتَوَتۡ عَلَى ٱلۡجُودِيِّۖ وَقِيلَ بُعۡدٗا لِّلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Aka ce: “Ke qasa, ki haxiye ruwanki, ke kuma sama ki riqe ruwanki, aka kuwa qafar da ruwan, kuma aka gama al’amarin, (jirgin) kuma ya tsaya a kan (dutsen) Judi; aka kuma ce: Halaka ta tabbata ga mutane azzalumai.”



السورة: Suratu Hud

الآية : 45

وَنَادَىٰ نُوحٞ رَّبَّهُۥ فَقَالَ رَبِّ إِنَّ ٱبۡنِي مِنۡ أَهۡلِي وَإِنَّ وَعۡدَكَ ٱلۡحَقُّ وَأَنتَ أَحۡكَمُ ٱلۡحَٰكِمِينَ

Nuhu kuma ya kira Ubangijinsa sai ya ce: “Ya Ubangijina, lalle xana yana daga iyalina, lalle kuma alqawarinka gaskiya ne, kuma Kai ne Ka fi masu hukunci iya hukunci.”



السورة: Suratu Hud

الآية : 46

قَالَ يَٰنُوحُ إِنَّهُۥ لَيۡسَ مِنۡ أَهۡلِكَۖ إِنَّهُۥ عَمَلٌ غَيۡرُ صَٰلِحٖۖ فَلَا تَسۡـَٔلۡنِ مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٌۖ إِنِّيٓ أَعِظُكَ أَن تَكُونَ مِنَ ٱلۡجَٰهِلِينَ

(Allah) Ya ce: Ya Nuhu, lalle shi ba ya daga cikin iyalinka, lalle shi aiki ne marar kyau; to kada ka qara tambaya Ta abin da ba ka da sani a kansa; lalle Ni Ina gargaxin ka da kada ka zamanto cikin jahilai



السورة: Suratu Hud

الآية : 47

قَالَ رَبِّ إِنِّيٓ أَعُوذُ بِكَ أَنۡ أَسۡـَٔلَكَ مَا لَيۡسَ لِي بِهِۦ عِلۡمٞۖ وَإِلَّا تَغۡفِرۡ لِي وَتَرۡحَمۡنِيٓ أَكُن مِّنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

Ya ce: “Ya Ubangijina, lalle ni ina neman tsarinka a kan in tambaye Ka abin da ba ni da sani a kansa, idan kuwa ba Ka yafe mini ba, Ka kuma ji qai na, to zan zamo cikin asararru.”



السورة: Suratu Hud

الآية : 48

قِيلَ يَٰنُوحُ ٱهۡبِطۡ بِسَلَٰمٖ مِّنَّا وَبَرَكَٰتٍ عَلَيۡكَ وَعَلَىٰٓ أُمَمٖ مِّمَّن مَّعَكَۚ وَأُمَمٞ سَنُمَتِّعُهُمۡ ثُمَّ يَمَسُّهُم مِّنَّا عَذَابٌ أَلِيمٞ

Aka ce: Ya Nuhu, ka sauka cikin aminci daga gare Mu da albarka a gare ka da kuma ga al’ummun da suke tare da kai. Wasu al’ummun kuma za Mu jiyar da su daxi, sannan kuma azaba mai raxaxi daga gare Mu ta same su



السورة: Suratu Hud

الآية : 49

تِلۡكَ مِنۡ أَنۢبَآءِ ٱلۡغَيۡبِ نُوحِيهَآ إِلَيۡكَۖ مَا كُنتَ تَعۡلَمُهَآ أَنتَ وَلَا قَوۡمُكَ مِن قَبۡلِ هَٰذَاۖ فَٱصۡبِرۡۖ إِنَّ ٱلۡعَٰقِبَةَ لِلۡمُتَّقِينَ

Waxannan suna daga labaran gaibu da muke yi maka wahayinsu, don kai da mutanenka ba ku san su ba kafin wannan (labarin); sai ka yi haquri; haqiqa kyakkyawan qarshe yana ga masu taqawa



السورة: Suratu Hud

الآية : 50

وَإِلَىٰ عَادٍ أَخَاهُمۡ هُودٗاۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥٓۖ إِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا مُفۡتَرُونَ

Kuma (Mun aiko wa) Adawa xan’uwansu Hudu, ya ce: “Ya ku mutanena, ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta da gaskiya sai shi; ku ba wasu ne ba face masu qaga wa (Allah) qarya



السورة: Suratu Hud

الآية : 51

يَٰقَوۡمِ لَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ أَجۡرًاۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَى ٱلَّذِي فَطَرَنِيٓۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ

“Ya ku mutanena, ba na tambayar ku wani lada game da shi (wannan saqo); ladana dai yana ga wanda ya qagi halittata. Yanzu ba za ku hankalta ba?



السورة: Suratu Hud

الآية : 52

وَيَٰقَوۡمِ ٱسۡتَغۡفِرُواْ رَبَّكُمۡ ثُمَّ تُوبُوٓاْ إِلَيۡهِ يُرۡسِلِ ٱلسَّمَآءَ عَلَيۡكُم مِّدۡرَارٗا وَيَزِدۡكُمۡ قُوَّةً إِلَىٰ قُوَّتِكُمۡ وَلَا تَتَوَلَّوۡاْ مُجۡرِمِينَ

“Kuma ya ku mutanena, ku nemi gafarar Ubangijinku sannan ku tuba gare Shi, zai sauko muku da mamakon ruwan sama, zai kuma qara muku qarfi a kan qarfinku, kada kuma ku ba da baya kuna masu aikata laifi.”



السورة: Suratu Hud

الآية : 53

قَالُواْ يَٰهُودُ مَا جِئۡتَنَا بِبَيِّنَةٖ وَمَا نَحۡنُ بِتَارِكِيٓ ءَالِهَتِنَا عَن قَوۡلِكَ وَمَا نَحۡنُ لَكَ بِمُؤۡمِنِينَ

Suka ce: “Ya kai Hudu ba ka zo mana da wata hujja ba, kuma ba za mu bar abubuwan da muke bauta ba saboda maganarka, ba kuma za mu yi imani da kai ba



السورة: Suratu Hud

الآية : 54

إِن نَّقُولُ إِلَّا ٱعۡتَرَىٰكَ بَعۡضُ ءَالِهَتِنَا بِسُوٓءٖۗ قَالَ إِنِّيٓ أُشۡهِدُ ٱللَّهَ وَٱشۡهَدُوٓاْ أَنِّي بَرِيٓءٞ مِّمَّا تُشۡرِكُونَ

“Ba abin da za mu faxa sai dai kawai (mu ce) wasu abubuwan bautarmu ne suka sa maka tavuwa.” Ya ce: “Ni lalle ina shaidar da Allah, ku ma kuma ku shaida cewa ni lalle ba ruwana da abin da kuke haxa (Allah) da shi



السورة: Suratu Hud

الآية : 55

مِن دُونِهِۦۖ فَكِيدُونِي جَمِيعٗا ثُمَّ لَا تُنظِرُونِ

“Wanda ba Shi (Allah) ba; to sai ku shirya min makirci gaba xayanku, kar kuma ku saurara mini



السورة: Suratu Hud

الآية : 56

إِنِّي تَوَكَّلۡتُ عَلَى ٱللَّهِ رَبِّي وَرَبِّكُمۚ مَّا مِن دَآبَّةٍ إِلَّا هُوَ ءَاخِذُۢ بِنَاصِيَتِهَآۚ إِنَّ رَبِّي عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

“Lalle ni na dogara ga Allah, Ubangijina kuma Ubangijinku. Babu wata dabba face Shi ne Yake riqe da makwarkwaxarta. Lalle Ubangijina a kan tafarki madaidaici Yake



السورة: Suratu Hud

الآية : 57

فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَقَدۡ أَبۡلَغۡتُكُم مَّآ أُرۡسِلۡتُ بِهِۦٓ إِلَيۡكُمۡۚ وَيَسۡتَخۡلِفُ رَبِّي قَوۡمًا غَيۡرَكُمۡ وَلَا تَضُرُّونَهُۥ شَيۡـًٔاۚ إِنَّ رَبِّي عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٍ حَفِيظٞ

“To idan kuka ba da baya, haqiqa na isar muku abin da aka aiko ni da shi zuwa gare ku. Kuma Ubangijina zai iya musanya wasu mutanen ba ku ba, kuma ba za ku cutar da Shi da komai ba. Lalle Ubangijina Mai kula da komai ne.”



السورة: Suratu Hud

الآية : 58

وَلَمَّا جَآءَ أَمۡرُنَا نَجَّيۡنَا هُودٗا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ بِرَحۡمَةٖ مِّنَّا وَنَجَّيۡنَٰهُم مِّنۡ عَذَابٍ غَلِيظٖ

Lokacin kuwa da umarninmu ya zo sai Muka tserar da Hudu shi da waxanda suka ba da gaskiya da shi, saboda wata rahama daga gare mu, Muka kuma tserar da su daga azaba mai gwavi



السورة: Suratu Hud

الآية : 59

وَتِلۡكَ عَادٞۖ جَحَدُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ وَعَصَوۡاْ رُسُلَهُۥ وَٱتَّبَعُوٓاْ أَمۡرَ كُلِّ جَبَّارٍ عَنِيدٖ

Waxancan kuwa su ne Adawa, da suka musanta ayoyin Ubangijinsu, suka kuma sava wa manzanninsa, kuma suka bi umarnin duk wani mai girman kai taqadari



السورة: Suratu Hud

الآية : 60

وَأُتۡبِعُواْ فِي هَٰذِهِ ٱلدُّنۡيَا لَعۡنَةٗ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ أَلَآ إِنَّ عَادٗا كَفَرُواْ رَبَّهُمۡۗ أَلَا بُعۡدٗا لِّعَادٖ قَوۡمِ هُودٖ

Aka kuma biyar musu da la’ana a duniya, haka kuma a ranar alqiyama. Ku saurara! Lalle Adawa kam sun kafirce wa Ubangijinsu. Ku saurara! Halaka ta tabbata ga Adawa mutanen Hudu