السورة: Suratul Anfal

الآية : 1

يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡأَنفَالِۖ قُلِ ٱلۡأَنفَالُ لِلَّهِ وَٱلرَّسُولِۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَصۡلِحُواْ ذَاتَ بَيۡنِكُمۡۖ وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

Suna tambayar ka game da ganimomi[1]; ka ce (da su): “Ganimomi na Allah ne da kuma Manzo; saboda haka ku kiyaye dokokin Allah, ku kuma gyara tsakaninku, kuma ku bi Allah da Manzonsa, idan kun kasance muminai.”


1- Watau tambayar da sahabbai suka yi wa Annabi () game da hukuncin ganimar yaqin Badar.


السورة: Suratul Anfal

الآية : 2

إِنَّمَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِرَ ٱللَّهُ وَجِلَتۡ قُلُوبُهُمۡ وَإِذَا تُلِيَتۡ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُهُۥ زَادَتۡهُمۡ إِيمَٰنٗا وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ

Muminai na haqiqa (su ne) kaxai waxanda idan aka ambaci Allah, sai zukatansu su raurawa, idan kuma aka karanta musu ayoyinsa, sai su qara musu imani, kuma ga Ubangijinsu ne kawai suke dogara



السورة: Suratul Anfal

الآية : 3

ٱلَّذِينَ يُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ

Waxanda suke tsayar da salla kuma suke ciyarwa daga abin da muka arzurta su



السورة: Suratul Anfal

الآية : 4

أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ حَقّٗاۚ لَّهُمۡ دَرَجَٰتٌ عِندَ رَبِّهِمۡ وَمَغۡفِرَةٞ وَرِزۡقٞ كَرِيمٞ

Waxannan su ne muminai na haqiqa. Suna da muqamai a wurin Ubangijinsu da kuma gafara da arziki na karamci



السورة: Suratul Anfal

الآية : 5

كَمَآ أَخۡرَجَكَ رَبُّكَ مِنۢ بَيۡتِكَ بِٱلۡحَقِّ وَإِنَّ فَرِيقٗا مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ لَكَٰرِهُونَ

Kamar yadda Ubangijinka Ya fitar da kai daga gidanka (na Madina) da gaskiya, alhali lalle wata jama’a daga muminai tabbas suna qin (haka)



السورة: Suratul Anfal

الآية : 6

يُجَٰدِلُونَكَ فِي ٱلۡحَقِّ بَعۡدَ مَا تَبَيَّنَ كَأَنَّمَا يُسَاقُونَ إِلَى ٱلۡمَوۡتِ وَهُمۡ يَنظُرُونَ

Suna jayayya da kai game da abin da yake tabbas, kai ka ce ana kora su ne wajen mutuwa, alhali kuwa suna kallo



السورة: Suratul Anfal

الآية : 7

وَإِذۡ يَعِدُكُمُ ٱللَّهُ إِحۡدَى ٱلطَّآئِفَتَيۡنِ أَنَّهَا لَكُمۡ وَتَوَدُّونَ أَنَّ غَيۡرَ ذَاتِ ٱلشَّوۡكَةِ تَكُونُ لَكُمۡ وَيُرِيدُ ٱللَّهُ أَن يُحِقَّ ٱلۡحَقَّ بِكَلِمَٰتِهِۦ وَيَقۡطَعَ دَابِرَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

(Ka tuna) kuma lokacin da Allah Ya yi muku alqawarin xayar jama’an nan guda biyu (na abokan gaba)[1] cewa, lalle taku ce, sai kuka riqa fatan marar wahalar ce za ta zama taku, alhali kuwa Allah Yana nufin Ya tabbatar da gaskiya da kalmominsa, Ya kuma tumvuke tushen kafirai


1- Watau ko dai su yi nasarar rutsawa da kayan ayarin fataken Quraishawa, ko kuma su haxu da rundunar mayaqan Makka.


السورة: Suratul Anfal

الآية : 8

لِيُحِقَّ ٱلۡحَقَّ وَيُبۡطِلَ ٱلۡبَٰطِلَ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡمُجۡرِمُونَ

Don (kuma) Ya tabbatar da gaskiya, Ya kuma lalata varna ko da kuwa kafirai sun qi (hakan)



السورة: Suratul Anfal

الآية : 9

إِذۡ تَسۡتَغِيثُونَ رَبَّكُمۡ فَٱسۡتَجَابَ لَكُمۡ أَنِّي مُمِدُّكُم بِأَلۡفٖ مِّنَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ مُرۡدِفِينَ

Ku tuna lokacin da kuke neman taimakon Ubangijinku, sai Ya amsa muku cewa: “Ni zan kawo muku xauki na mala’iku dubu masu bibiyar juna.”



السورة: Suratul Anfal

الآية : 10

وَمَا جَعَلَهُ ٱللَّهُ إِلَّا بُشۡرَىٰ وَلِتَطۡمَئِنَّ بِهِۦ قُلُوبُكُمۡۚ وَمَا ٱلنَّصۡرُ إِلَّا مِنۡ عِندِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ

Kuma (wannan taimakon) Allah bai sanya shi ba, sai don albishir a gare ku, don kuma zukatanku su nutsu da shi. Babu kuma wata nasara sai daga wurin Allah. Lalle Allah Mabuwayi ne Mai hikima



السورة: Suratul Anfal

الآية : 11

إِذۡ يُغَشِّيكُمُ ٱلنُّعَاسَ أَمَنَةٗ مِّنۡهُ وَيُنَزِّلُ عَلَيۡكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ لِّيُطَهِّرَكُم بِهِۦ وَيُذۡهِبَ عَنكُمۡ رِجۡزَ ٱلشَّيۡطَٰنِ وَلِيَرۡبِطَ عَلَىٰ قُلُوبِكُمۡ وَيُثَبِّتَ بِهِ ٱلۡأَقۡدَامَ

(Ku kuma tuna) lokacin da gyangyaxi yake kwashe ku (Allah) Yana Mai amintar da ku (daga tunanin abokan gaba), Ya kuma riqa saukar da ruwa daga sama don Ya tsarkake ku da shi, Ya kuma tafiyar muku da waswasin shaixan, don kuma Ya qarfafa zukatanku Ya kuma tabbatar da dugaduganku da shi



السورة: Suratul Anfal

الآية : 12

إِذۡ يُوحِي رَبُّكَ إِلَى ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ أَنِّي مَعَكُمۡ فَثَبِّتُواْ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْۚ سَأُلۡقِي فِي قُلُوبِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱلرُّعۡبَ فَٱضۡرِبُواْ فَوۡقَ ٱلۡأَعۡنَاقِ وَٱضۡرِبُواْ مِنۡهُمۡ كُلَّ بَنَانٖ

(Ka kuma tuna) lokacin da Ubangijinka Yake wahayi zuwa ga mala’iku cewa: “Lalle Ni ina tare da ku, saboda haka ku qarfafa wa waxanda suka yi imani gwiwa. Da sannu zan jefa tsoro cikin zukatan waxanda suka kafirce, saboda haka ku doki wuyansu, kuma ku doki dukkanin gavovin hannaye da qafafu.”



السورة: Suratul Anfal

الآية : 13

ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ شَآقُّواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥۚ وَمَن يُشَاقِقِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَإِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

Wannan kuwa saboda sun sava wa Allah da Manzonsa. Duk wanda kuwa ya sava wa Allah da Manzonsa to lalle Allah Mai tsananin uquba ne



السورة: Suratul Anfal

الآية : 14

ذَٰلِكُمۡ فَذُوقُوهُ وَأَنَّ لِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابَ ٱلنَّارِ

Wannan (uqubar) sai ku xanxane ta (a duniya), kuma ba shakka kafirai suna da azabar wuta



السورة: Suratul Anfal

الآية : 15

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا لَقِيتُمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ زَحۡفٗا فَلَا تُوَلُّوهُمُ ٱلۡأَدۡبَارَ

Ya ku waxanda suka yi imani, idan kuka haxu da cincirindon waxanda suka kafirta, to kada ku ba su baya



السورة: Suratul Anfal

الآية : 16

وَمَن يُوَلِّهِمۡ يَوۡمَئِذٖ دُبُرَهُۥٓ إِلَّا مُتَحَرِّفٗا لِّقِتَالٍ أَوۡ مُتَحَيِّزًا إِلَىٰ فِئَةٖ فَقَدۡ بَآءَ بِغَضَبٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَمَأۡوَىٰهُ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

Duk kuwa wanda ya ba su baya a wannan ranar idan dai ba wanda ya gudu da niyyar juyowa ya kai xauki ko kuma mai niyyar haxuwa da wata jama’a (ta mayaqa) ba, to haqiqa ya komo da fushin Allah, kuma makomarsa Jahannama ce; wannan makoma kuwa ta munana



السورة: Suratul Anfal

الآية : 17

فَلَمۡ تَقۡتُلُوهُمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ قَتَلَهُمۡۚ وَمَا رَمَيۡتَ إِذۡ رَمَيۡتَ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ رَمَىٰ وَلِيُبۡلِيَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ مِنۡهُ بَلَآءً حَسَنًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ

Saboda haka ba ku kuka kashe su ba, Allah ne Ya kashe su[1]. Kuma ba ka jefa ba lokacin da ka jefa, sai dai Allah ne Ya jefa[2]. Don kuma Ya jarrabi muminai da kyakkyawar jarrabawa[3]. Lalle Allah Mai ji ne Masani


1- Domin komai ya faru ne da taimakonsa da agajinsa.


2- Watau shi ma Annabi () da ya xauki qasa da tafin hannunsa ya watsa ta a fuskokin kafirai ta kuma cika musu ido, to a haqiqa ba shi ne ya yi wannan jifan ba, Allah ne ya yi.


3- Domin su yi masa godiya a kan ni’imominsa.


السورة: Suratul Anfal

الآية : 18

ذَٰلِكُمۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ مُوهِنُ كَيۡدِ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Waccan (jarraba ku da aka yi gaskiya ne), kuma lalle Allah Mai raunana makircin kafirai ne



السورة: Suratul Anfal

الآية : 19

إِن تَسۡتَفۡتِحُواْ فَقَدۡ جَآءَكُمُ ٱلۡفَتۡحُۖ وَإِن تَنتَهُواْ فَهُوَ خَيۡرٞ لَّكُمۡۖ وَإِن تَعُودُواْ نَعُدۡ وَلَن تُغۡنِيَ عَنكُمۡ فِئَتُكُمۡ شَيۡـٔٗا وَلَوۡ كَثُرَتۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Idan kuna neman zuwan hukunci ne (watau azaba), to haqiqa hukuncin ya zo muku. Idan kuka daina to shi ya fi muku alheri, idan kuma kuka koma, to za Mu koma, jama’arku kuma ba za ta amfana muku komai ba, komai yawanta kuwa, lalle kuma Allah Yana tare da muminai



السورة: Suratul Anfal

الآية : 20

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَلَا تَوَلَّوۡاْ عَنۡهُ وَأَنتُمۡ تَسۡمَعُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku bi Allah da Manzonsa kada kuma ku ba shi baya alhali kuwa kuna ji



السورة: Suratul Anfal

الآية : 21

وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ قَالُواْ سَمِعۡنَا وَهُمۡ لَا يَسۡمَعُونَ

Kada kuma ku zama kamar waxanda suka ce: “Mun ji,” alhalin kuwa su ba sa ji



السورة: Suratul Anfal

الآية : 22

۞إِنَّ شَرَّ ٱلدَّوَآبِّ عِندَ ٱللَّهِ ٱلصُّمُّ ٱلۡبُكۡمُ ٱلَّذِينَ لَا يَعۡقِلُونَ

Lalle mafi sharrin masu tafiya a bayan qasa a wurin Allah (su ne) kurame (ga jin gaskiya) bebaye (ga faxar gaskiya) waxanda ba sa hankalta



السورة: Suratul Anfal

الآية : 23

وَلَوۡ عَلِمَ ٱللَّهُ فِيهِمۡ خَيۡرٗا لَّأَسۡمَعَهُمۡۖ وَلَوۡ أَسۡمَعَهُمۡ لَتَوَلَّواْ وَّهُم مُّعۡرِضُونَ

Da Allah Ya san da akwai wani alheri a tare da su, to da Ya jiyar da su (gaskiya); da kuma Ya jiyar da su xin ma, to da kuwa sun ba da baya suna masu bijirewa



السورة: Suratul Anfal

الآية : 24

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱسۡتَجِيبُواْ لِلَّهِ وَلِلرَّسُولِ إِذَا دَعَاكُمۡ لِمَا يُحۡيِيكُمۡۖ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَحُولُ بَيۡنَ ٱلۡمَرۡءِ وَقَلۡبِهِۦ وَأَنَّهُۥٓ إِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku amsa kiran Allah da na Manzo idan ya yi kiran ku ga abin da zai raya ku; kuma ku sani cewa, lalle Allah Yana kange tsakanin mutum da zuciyarsa, kuma lalle wurinsa ne za a tattara ku



السورة: Suratul Anfal

الآية : 25

وَٱتَّقُواْ فِتۡنَةٗ لَّا تُصِيبَنَّ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنكُمۡ خَآصَّةٗۖ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

Ku kiyayi fitinar da ba kawai waxanda suka yi zalunci za ta shafa ba, kuma ku sani cewa lalle Allah Mai tsananin uquba ne



السورة: Suratul Anfal

الآية : 26

وَٱذۡكُرُوٓاْ إِذۡ أَنتُمۡ قَلِيلٞ مُّسۡتَضۡعَفُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ تَخَافُونَ أَن يَتَخَطَّفَكُمُ ٱلنَّاسُ فَـَٔاوَىٰكُمۡ وَأَيَّدَكُم بِنَصۡرِهِۦ وَرَزَقَكُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

Kuma ku tuna lokacin da kuke ‘yan tsirari masu rauni a bayan qasa, kuna tsoron kada wasu mutane su fauce ku, sai Ya tattara ku (a Madina) Ya kuma qarfafa ku da taimakonsa, Ya kuma arzuta ku da tsarkakan abubuwa don ku godiya



السورة: Suratul Anfal

الآية : 27

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَخُونُواْ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَ وَتَخُونُوٓاْ أَمَٰنَٰتِكُمۡ وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku ha’inci Allah da Manzo, (kada) kuma ku ha’inci amanoninku alhali kuna sane



السورة: Suratul Anfal

الآية : 28

وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَآ أَمۡوَٰلُكُمۡ وَأَوۡلَٰدُكُمۡ فِتۡنَةٞ وَأَنَّ ٱللَّهَ عِندَهُۥٓ أَجۡرٌ عَظِيمٞ

Kuma ku sani cewa, dukiyoyinku da ‘ya’yanku fitina ne, Allah kuma lalle a wurinsa lada mai girma yake



السورة: Suratul Anfal

الآية : 29

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِن تَتَّقُواْ ٱللَّهَ يَجۡعَل لَّكُمۡ فُرۡقَانٗا وَيُكَفِّرۡ عَنكُمۡ سَيِّـَٔاتِكُمۡ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡۗ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ

Ya ku waxanda suka yi imani, idan kuka kiyaye dokokin Allah, to zai sanya muku (hanyar) tsira Ya kuma kankare muku munanan ayyukanku kuma Ya gafarta muku. Allah kuwa Ma’abocin babbar falala ne



السورة: Suratul Anfal

الآية : 30

وَإِذۡ يَمۡكُرُ بِكَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِيُثۡبِتُوكَ أَوۡ يَقۡتُلُوكَ أَوۡ يُخۡرِجُوكَۚ وَيَمۡكُرُونَ وَيَمۡكُرُ ٱللَّهُۖ وَٱللَّهُ خَيۡرُ ٱلۡمَٰكِرِينَ

Kuma ka tuna lokacin da waxanda suka kafirta suke qulla maka makirci don su tsare ka ko kuma su kashe ka ko su kore ka. Suna kuma shirya makirci Allah kuma Yana mayar musu sakamakon makircinsu. Allah kuma (Shi ne) Ya fi masu makirci iya (sakayyar) makirci[1]


1- Wannan bayani ne game da makircin da shugabannin Quraishawa suka shirya wa Annabi () a Makka kafin ya yi hijira zuwa Madina.