السورة: Suratul An’am

الآية : 1

ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَجَعَلَ ٱلظُّلُمَٰتِ وَٱلنُّورَۖ ثُمَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِرَبِّهِمۡ يَعۡدِلُونَ

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah Wanda Ya halicci sammai da qasa, kuma Ya halicci duffai da haske; sannan waxanda suka kafirta suna daidaita Ubangijinsu da (wasu)



السورة: Suratul An’am

الآية : 2

هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَكُم مِّن طِينٖ ثُمَّ قَضَىٰٓ أَجَلٗاۖ وَأَجَلٞ مُّسَمًّى عِندَهُۥۖ ثُمَّ أَنتُمۡ تَمۡتَرُونَ

Shi ne Wanda Ya halicce ku daga tavo, sannan Ya yanka (muku) ajali; da kuma wani ajalin sananne a wurinsa; sannan sai ga shi kuna jayayya



السورة: Suratul An’am

الآية : 3

وَهُوَ ٱللَّهُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَفِي ٱلۡأَرۡضِ يَعۡلَمُ سِرَّكُمۡ وَجَهۡرَكُمۡ وَيَعۡلَمُ مَا تَكۡسِبُونَ

Kuma Shi ne Allah a cikin sammai da kuma cikin qasa; Yana sane da abin da kuke voyewa da abin da kuke bayyanawa, kuma Yana sane da abin da kuke aikatawa



السورة: Suratul An’am

الآية : 4

وَمَا تَأۡتِيهِم مِّنۡ ءَايَةٖ مِّنۡ ءَايَٰتِ رَبِّهِمۡ إِلَّا كَانُواْ عَنۡهَا مُعۡرِضِينَ

Kuma babu wata aya cikin ayoyin Ubangijinsu da za ta zo musu, face sai sun kasance masu bijire mata



السورة: Suratul An’am

الآية : 5

فَقَدۡ كَذَّبُواْ بِٱلۡحَقِّ لَمَّا جَآءَهُمۡ فَسَوۡفَ يَأۡتِيهِمۡ أَنۢبَـٰٓؤُاْ مَا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ

To haqiqa sun qaryata gaskiya lokacin da ta zo musu; don haka da sannu labaran abin da suka kasance suna izgili da shi zai zo musu



السورة: Suratul An’am

الآية : 6

أَلَمۡ يَرَوۡاْ كَمۡ أَهۡلَكۡنَا مِن قَبۡلِهِم مِّن قَرۡنٖ مَّكَّنَّـٰهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مَا لَمۡ نُمَكِّن لَّكُمۡ وَأَرۡسَلۡنَا ٱلسَّمَآءَ عَلَيۡهِم مِّدۡرَارٗا وَجَعَلۡنَا ٱلۡأَنۡهَٰرَ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهِمۡ فَأَهۡلَكۡنَٰهُم بِذُنُوبِهِمۡ وَأَنشَأۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِمۡ قَرۡنًا ءَاخَرِينَ

Shin ba su ga yawan al’ummun da Muka halakar a gabaninsu ba, waxanda Muka kafa su a banqasa suka yi qarfi irin kafawar da ba Mu yi muku ba[1], kuma Muka aiko musu da ruwan sama a kai a kai, kuma Muka sanya qoramu suna gudana ta qarqashinsu, sai Muka hallakar da su saboda zunubansu, kuma bayan shuxewarsu Muka halicci wata sabuwar al’ummar daban?


1- Allah ya ba su qarfin jiki da yawan dukiya da ‘ya’ya. Dubi Suratur Rum aya ta 9-10 da Suratus Saba’i aya ta 45.


السورة: Suratul An’am

الآية : 7

وَلَوۡ نَزَّلۡنَا عَلَيۡكَ كِتَٰبٗا فِي قِرۡطَاسٖ فَلَمَسُوهُ بِأَيۡدِيهِمۡ لَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٞ

Kuma in da Mun saukar maka da wani littafin a rubuce a takardu, har suka tava shi da hannayensu, lalle da waxanda suka kafirta sun ce: “Wannan ba komai ba ne, face sihiri bayyananne.”



السورة: Suratul An’am

الآية : 8

وَقَالُواْ لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡهِ مَلَكٞۖ وَلَوۡ أَنزَلۡنَا مَلَكٗا لَّقُضِيَ ٱلۡأَمۡرُ ثُمَّ لَا يُنظَرُونَ

Kuma suka ce: “Don me ba a saukar masa da mala’ika ba?” Da kuwa Mun saukar da mala’ikan, to da ta faru ta qare (an hallaka su), sannan ba za a saurara musu ba



السورة: Suratul An’am

الآية : 9

وَلَوۡ جَعَلۡنَٰهُ مَلَكٗا لَّجَعَلۡنَٰهُ رَجُلٗا وَلَلَبَسۡنَا عَلَيۡهِم مَّا يَلۡبِسُونَ

Kuma in da Mun yo shi mala’ika ne, to lalle da Mun mayar da shi mutum, kuma da lalle Mun rikitar da su kamar yadda suka rikitar da kansu



السورة: Suratul An’am

الآية : 10

وَلَقَدِ ٱسۡتُهۡزِئَ بِرُسُلٖ مِّن قَبۡلِكَ فَحَاقَ بِٱلَّذِينَ سَخِرُواْ مِنۡهُم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ

Kuma haqiqa an yi wa waxansu manzanni da suka gabace ka izgili, sai sakamakon abin da suka kasance suna yin izgili da shi ya sauka kan masu izgilin



السورة: Suratul An’am

الآية : 11

قُلۡ سِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ ثُمَّ ٱنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُكَذِّبِينَ

Ka ce: “Ku yi tafiya a bayan qasa, sannan ku duba ku ga, yaya qarshen lamarin masu qaryatawa ya kasance?”



السورة: Suratul An’am

الآية : 12

قُل لِّمَن مَّا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ قُل لِّلَّهِۚ كَتَبَ عَلَىٰ نَفۡسِهِ ٱلرَّحۡمَةَۚ لَيَجۡمَعَنَّكُمۡ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ لَا رَيۡبَ فِيهِۚ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ فَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ

Ka ce: “Abin da yake cikin sammai da qasa na wane ne?” Ka ce: “Na Allah ne.” Ya wajabta wa kansa yin rahama. Lalle tabbas zai tattara ku zuwa ranar tashin alqiyama wadda babu kokwanto game da ita. Waxanda suka yi hasarar kawunansu ba za su yi imani ba



السورة: Suratul An’am

الآية : 13

۞وَلَهُۥ مَا سَكَنَ فِي ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِۚ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

“Kuma abin da ya nutsu a cikin dare ko rana nasa ne, kuma Shi ne Mai ji, Mai yawan sani.”



السورة: Suratul An’am

الآية : 14

قُلۡ أَغَيۡرَ ٱللَّهِ أَتَّخِذُ وَلِيّٗا فَاطِرِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَهُوَ يُطۡعِمُ وَلَا يُطۡعَمُۗ قُلۡ إِنِّيٓ أُمِرۡتُ أَنۡ أَكُونَ أَوَّلَ مَنۡ أَسۡلَمَۖ وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

Ka ce: “Shin yanzu wanin Allah ne zan riqa a matsayin majivinci, alhalin Shi ne Ya halicci sammai da qasa, kuma Shi Yake ciyarwa, ba a ciyar da Shi?” Ka ce: “Lalle ni an umarce ni da in zamo farkon mai miqa wuya; kuma lalle kada ka kasance daga masu shirka.”



السورة: Suratul An’am

الآية : 15

قُلۡ إِنِّيٓ أَخَافُ إِنۡ عَصَيۡتُ رَبِّي عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٖ

Ka ce: “Lalle ni ina jin tsoron azabar rana mai girma, idan na sava wa Ubangijina.”



السورة: Suratul An’am

الآية : 16

مَّن يُصۡرَفۡ عَنۡهُ يَوۡمَئِذٖ فَقَدۡ رَحِمَهُۥۚ وَذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡمُبِينُ

Wanda duk aka kawar masa da (azaba) a wannan rana, to haqiqa (Allah) Ya ji qan sa. Kuma wannan Shi ne rabo mabayyani



السورة: Suratul An’am

الآية : 17

وَإِن يَمۡسَسۡكَ ٱللَّهُ بِضُرّٖ فَلَا كَاشِفَ لَهُۥٓ إِلَّا هُوَۖ وَإِن يَمۡسَسۡكَ بِخَيۡرٖ فَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Kuma idan Allah Ya shafe ka da wata cuta, to ba wanda ya isa ya yaye ta sai Shi; kuma idan Ya shafe ka da wani alheri, to Shi Mai iko ne a kan komai



السورة: Suratul An’am

الآية : 18

وَهُوَ ٱلۡقَاهِرُ فَوۡقَ عِبَادِهِۦۚ وَهُوَ ٱلۡحَكِيمُ ٱلۡخَبِيرُ

Kuma Shi ne Mai rinjaye a kan bayinsa. Kuma Shi Mai hikima ne, Masani



السورة: Suratul An’am

الآية : 19

قُلۡ أَيُّ شَيۡءٍ أَكۡبَرُ شَهَٰدَةٗۖ قُلِ ٱللَّهُۖ شَهِيدُۢ بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡۚ وَأُوحِيَ إِلَيَّ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانُ لِأُنذِرَكُم بِهِۦ وَمَنۢ بَلَغَۚ أَئِنَّكُمۡ لَتَشۡهَدُونَ أَنَّ مَعَ ٱللَّهِ ءَالِهَةً أُخۡرَىٰۚ قُل لَّآ أَشۡهَدُۚ قُلۡ إِنَّمَا هُوَ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞ وَإِنَّنِي بَرِيٓءٞ مِّمَّا تُشۡرِكُونَ

Ka ce: “Mene ne mafi girman shaida?” Ka ce; “Allah Shi ne shaida tsakanina da ku. Kuma an saukar mini wannan Alqur’anin ne don in yi muku gargaxi da shi da kuma duk wanda zai isa zuwa gare shi. Yanzu kuwa za ku shaida cewa, lalle akwai waxansu allolin tare da Allah?” Ka ce: “Ni kam ba zan shaida ba.” Ka ce: “Allah Shi Xaya ne, kuma lalle ni ba ruwana da dukkan abin da kuke haxa Allah da shi.”



السورة: Suratul An’am

الآية : 20

ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَعۡرِفُونَهُۥ كَمَا يَعۡرِفُونَ أَبۡنَآءَهُمُۘ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ فَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ

Waxanda Muka ba su Littafi sun san shi kamar yadda suka san ‘ya’yansu. Waxanda suka yi hasarar kawunansu, to su kam ba za su tava yin imani ba



السورة: Suratul An’am

الآية : 21

وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ كَذَّبَ بِـَٔايَٰتِهِۦٓۚ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلظَّـٰلِمُونَ

Kuma ba mafi zalunci fiye da wanda ya qirqiri qarya ya jingina wa Allah, ko kuma ya qaryata ayoyinsa. Haqiqar lamarin dai su azzalumai ba za su tava rabauta ba



السورة: Suratul An’am

الآية : 22

وَيَوۡمَ نَحۡشُرُهُمۡ جَمِيعٗا ثُمَّ نَقُولُ لِلَّذِينَ أَشۡرَكُوٓاْ أَيۡنَ شُرَكَآؤُكُمُ ٱلَّذِينَ كُنتُمۡ تَزۡعُمُونَ

Kuma (ka tuna) ranar da za Mu tattara su gaba xaya, sannan Mu ce da waxanda suka yi shirka: “Ina abokan tarayyarku waxanda kuka kasance kuna riyawa?”



السورة: Suratul An’am

الآية : 23

ثُمَّ لَمۡ تَكُن فِتۡنَتُهُمۡ إِلَّآ أَن قَالُواْ وَٱللَّهِ رَبِّنَا مَا كُنَّا مُشۡرِكِينَ

Sannan fitinarsu ba ta zamo komai ba, face cewar da suka yi: “Wallahi, ya Ubangijinmu, ba mu kasance masu yin shirka ba!”



السورة: Suratul An’am

الآية : 24

ٱنظُرۡ كَيۡفَ كَذَبُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡۚ وَضَلَّ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ

Duba ka ga yadda suka yi wa kansu qarya. Kuma abin da suka kasance suna qirqira ya vace musu



السورة: Suratul An’am

الآية : 25

وَمِنۡهُم مَّن يَسۡتَمِعُ إِلَيۡكَۖ وَجَعَلۡنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ أَكِنَّةً أَن يَفۡقَهُوهُ وَفِيٓ ءَاذَانِهِمۡ وَقۡرٗاۚ وَإِن يَرَوۡاْ كُلَّ ءَايَةٖ لَّا يُؤۡمِنُواْ بِهَاۖ حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءُوكَ يُجَٰدِلُونَكَ يَقُولُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّآ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ

Kuma daga cikinsu akwai wanda yake sauraren ka; kuma Mun sanya murafai a zukatansu, ta yadda ba za su iya fahimtar sa ba, haka kuma a kunnuwansu akwai wata toshiya. Kuma in da za su ga kowace irin aya ce, ba za su yi imani da ita ba. Har ma idan sun zo maka suna jayayya da kai, (sai) waxanda suka kafirta su riqa cewa: “Ai wannan ba komai ba ne face tatsuniyoyin mutanen farko.”



السورة: Suratul An’am

الآية : 26

وَهُمۡ يَنۡهَوۡنَ عَنۡهُ وَيَنۡـَٔوۡنَ عَنۡهُۖ وَإِن يُهۡلِكُونَ إِلَّآ أَنفُسَهُمۡ وَمَا يَشۡعُرُونَ

Kuma suna hana (mutane) sauraren sa (Alqur’ani), kuma su kansu suna qara nesanta da shi; kuma ba kowa suke hallakarwa ba face kawunansu, sai dai su ba sa jin hakan



السورة: Suratul An’am

الآية : 27

وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذۡ وُقِفُواْ عَلَى ٱلنَّارِ فَقَالُواْ يَٰلَيۡتَنَا نُرَدُّ وَلَا نُكَذِّبَ بِـَٔايَٰتِ رَبِّنَا وَنَكُونَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Da kuma za ka ga lokacin da ake tsayar da su a gaban wuta, sai su ce: “Kaiconmu, ina ma da za a mayar da mu (duniya), to da ba za mu sake qaryata ayoyin Ubangijinmu ba, kuma za mu zamanto cikin muminai.”



السورة: Suratul An’am

الآية : 28

بَلۡ بَدَا لَهُم مَّا كَانُواْ يُخۡفُونَ مِن قَبۡلُۖ وَلَوۡ رُدُّواْ لَعَادُواْ لِمَا نُهُواْ عَنۡهُ وَإِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ

A’a, ba haka ba ne, abin da suke voyewa a da shi ne ya bayyana a gare su[1]; kuma in da za a mayar da su, to da sun koma kan abin da aka hana su. Kuma lalle su tabbas maqaryata ne


1- A duniya suna voye gaskiyar manzancin Annabi () duk da cewa sun san gaskiyarsa.


السورة: Suratul An’am

الآية : 29

وَقَالُوٓاْ إِنۡ هِيَ إِلَّا حَيَاتُنَا ٱلدُّنۡيَا وَمَا نَحۡنُ بِمَبۡعُوثِينَ

Kuma suka ce: “Ba wata (rayuwa) sai rayuwarmu ta duniya, kuma mu ba waxanda za a sake tashin mu ba ne.”



السورة: Suratul An’am

الآية : 30

وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذۡ وُقِفُواْ عَلَىٰ رَبِّهِمۡۚ قَالَ أَلَيۡسَ هَٰذَا بِٱلۡحَقِّۚ قَالُواْ بَلَىٰ وَرَبِّنَاۚ قَالَ فَذُوقُواْ ٱلۡعَذَابَ بِمَا كُنتُمۡ تَكۡفُرُونَ

Kuma in da za ka ga lokacin da aka tsayar da su a gaban Ubangjinsu; ya ce: “Shin ashe wannan ba gaskiya ne ba?” Sai su ce: “Gaskiya ne, muna rantsuwa da Ubangijinmu.” Sai Ya ce: “To ku xanxani azaba saboda abin da kuka kasance kuna yi na kafirci.”