السورة: Suratul Furqan

الآية : 1

تَبَارَكَ ٱلَّذِي نَزَّلَ ٱلۡفُرۡقَانَ عَلَىٰ عَبۡدِهِۦ لِيَكُونَ لِلۡعَٰلَمِينَ نَذِيرًا

(Allah) Wanda Ya saukar wa Bawansa Alqur’ani don ya zamo mai gargaxi ga talikai albarkatunsa sun yawaita



السورة: Suratul Furqan

الآية : 2

ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلَمۡ يَتَّخِذۡ وَلَدٗا وَلَمۡ يَكُن لَّهُۥ شَرِيكٞ فِي ٱلۡمُلۡكِ وَخَلَقَ كُلَّ شَيۡءٖ فَقَدَّرَهُۥ تَقۡدِيرٗا

(Shi ne) Wanda mulkin sammai da qasa nasa ne, kuma bai riqi wani xa ba, ba kuma Shi da wani abokin tarayya a cikin mulkin, Ya kuma halicci kowanne abu, sannan Ya ajiye shi a irin gwargwadon da ya dace da shi



السورة: Suratul Furqan

الآية : 3

وَٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةٗ لَّا يَخۡلُقُونَ شَيۡـٔٗا وَهُمۡ يُخۡلَقُونَ وَلَا يَمۡلِكُونَ لِأَنفُسِهِمۡ ضَرّٗا وَلَا نَفۡعٗا وَلَا يَمۡلِكُونَ مَوۡتٗا وَلَا حَيَوٰةٗ وَلَا نُشُورٗا

Kuma suka riqi ababen bauta ba Shi ba, ba sa halittar komai, alhali kuwa su ake halittawa, kuma ba sa mallakar cuta ko amfani ga kawunansu, ba sa kuma mallakar kashewa ko rayawa ko tashi (bayan mutuwa)



السورة: Suratul Furqan

الآية : 4

وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّآ إِفۡكٌ ٱفۡتَرَىٰهُ وَأَعَانَهُۥ عَلَيۡهِ قَوۡمٌ ءَاخَرُونَۖ فَقَدۡ جَآءُو ظُلۡمٗا وَزُورٗا

Waxanda kuma suka kafirta suka ce: “Wannan (Alqur’ani) ba komai ba ne sai qarya da ya qage ta kuma wasu mutane daban suka taimake shi a kansa.” To haqiqa sun zo da zalunci da kuma qarya



السورة: Suratul Furqan

الآية : 5

وَقَالُوٓاْ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ ٱكۡتَتَبَهَا فَهِيَ تُمۡلَىٰ عَلَيۡهِ بُكۡرَةٗ وَأَصِيلٗا

Suka kuma ce: “Tatsuniyoyin mutanen farko ne da ya rubuta su, waxanda ake masa shiftar su safe da yamma.”



السورة: Suratul Furqan

الآية : 6

قُلۡ أَنزَلَهُ ٱلَّذِي يَعۡلَمُ ٱلسِّرَّ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّهُۥ كَانَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

Ka ce (da su): “Wanda Yake sane da asirin sammai da qasa Shi Ya saukar da shi. Lalle Shi Ya kasance Mai gafara ne, Mai jin qai.”



السورة: Suratul Furqan

الآية : 7

وَقَالُواْ مَالِ هَٰذَا ٱلرَّسُولِ يَأۡكُلُ ٱلطَّعَامَ وَيَمۡشِي فِي ٱلۡأَسۡوَاقِ لَوۡلَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِ مَلَكٞ فَيَكُونَ مَعَهُۥ نَذِيرًا

Suka kuma ce: “Me ya sa wannan Manzo yake cin abinci kuma yake tafiya cikin kasuwanni? Me ya hana a saukar masa da mala’ika, sai ya zama mai gargaxi tare da shi?



السورة: Suratul Furqan

الآية : 8

أَوۡ يُلۡقَىٰٓ إِلَيۡهِ كَنزٌ أَوۡ تَكُونُ لَهُۥ جَنَّةٞ يَأۡكُلُ مِنۡهَاۚ وَقَالَ ٱلظَّـٰلِمُونَ إِن تَتَّبِعُونَ إِلَّا رَجُلٗا مَّسۡحُورًا

Ko a jefo masa wata taskar dukiya ko ya zama yana da wani lambu wanda daga gare shi zai riqa ci?” Sai azzalumai suka ce “Ba wanda kuke bi sai wani mutum wanda aka yi wa sihiri!”



السورة: Suratul Furqan

الآية : 9

ٱنظُرۡ كَيۡفَ ضَرَبُواْ لَكَ ٱلۡأَمۡثَٰلَ فَضَلُّواْ فَلَا يَسۡتَطِيعُونَ سَبِيلٗا

To ka dubi yadda suka riqa buga maka misali[1], sai suka vata, don haka ba za su iya bin hanyar shiriya ba


1- Watau wani lokaci su ce masa mai sihiri, wani lokaci kuma su ce mawaqi, ko su ce boka, ko mai tavin hankali.


السورة: Suratul Furqan

الآية : 10

تَبَارَكَ ٱلَّذِيٓ إِن شَآءَ جَعَلَ لَكَ خَيۡرٗا مِّن ذَٰلِكَ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ وَيَجۡعَل لَّكَ قُصُورَۢا

Albarkatun (Allah) sun yawaita, wanda idan Ya ga dama sai Ya sanya maka alheri fiye da waxannan: (su ne) gonakai waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, Ya kuma sanya maka maka-makan gidaje



السورة: Suratul Furqan

الآية : 11

بَلۡ كَذَّبُواْ بِٱلسَّاعَةِۖ وَأَعۡتَدۡنَا لِمَن كَذَّبَ بِٱلسَّاعَةِ سَعِيرًا

Ba haka ba ne, sun dai qaryata tashin alqiyama ne; Mun kuwa tanadi (wutar) Sa’ira ga wanda ya qaryata tashin alqiyama



السورة: Suratul Furqan

الآية : 12

إِذَا رَأَتۡهُم مِّن مَّكَانِۭ بَعِيدٖ سَمِعُواْ لَهَا تَغَيُّظٗا وَزَفِيرٗا

Idan (wutar) ta hango su daga wuri mai nisa sai su ji tafarfasa da gurnaninta



السورة: Suratul Furqan

الآية : 13

وَإِذَآ أُلۡقُواْ مِنۡهَا مَكَانٗا ضَيِّقٗا مُّقَرَّنِينَ دَعَوۡاْ هُنَالِكَ ثُبُورٗا

Idan kuwa aka jefa su cikinta a wani wuri quntatacce nata, suna ququnce, sai su riqa kiran hallaka a can



السورة: Suratul Furqan

الآية : 14

لَّا تَدۡعُواْ ٱلۡيَوۡمَ ثُبُورٗا وَٰحِدٗا وَٱدۡعُواْ ثُبُورٗا كَثِيرٗا

(Sai a ce da su): “A yau kada ku kirawo hallaka xaya kawai, ku kirawo hallaka da yawa!”



السورة: Suratul Furqan

الآية : 15

قُلۡ أَذَٰلِكَ خَيۡرٌ أَمۡ جَنَّةُ ٱلۡخُلۡدِ ٱلَّتِي وُعِدَ ٱلۡمُتَّقُونَۚ كَانَتۡ لَهُمۡ جَزَآءٗ وَمَصِيرٗا

Ka ce (da su): “Yanzu wannan ne ya fi alheri, ko kuwa Aljannar dawwama wadda aka yi wa masu taqawa alqawarinta, ta zama sakamako da makoma a gare su?”



السورة: Suratul Furqan

الآية : 16

لَّهُمۡ فِيهَا مَا يَشَآءُونَ خَٰلِدِينَۚ كَانَ عَلَىٰ رَبِّكَ وَعۡدٗا مَّسۡـُٔولٗا

Suna da duk abin da suka ga dama a cikinta, masu dawwama ne. (Wannan kuma) ya kasance alqawari ne abin tambaya a kan Ubangijnka



السورة: Suratul Furqan

الآية : 17

وَيَوۡمَ يَحۡشُرُهُمۡ وَمَا يَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ فَيَقُولُ ءَأَنتُمۡ أَضۡلَلۡتُمۡ عِبَادِي هَـٰٓؤُلَآءِ أَمۡ هُمۡ ضَلُّواْ ٱلسَّبِيلَ

(Ka tuna) kuma ranar da zai tara su da abin da suke bauta wa ba Allah ba, sai Ya ce (da su): “Shin yanzu ku ne kuka vatar da bayina waxannan, ko kuwa su ne suka vace wa hanya don kansu?”



السورة: Suratul Furqan

الآية : 18

قَالُواْ سُبۡحَٰنَكَ مَا كَانَ يَنۢبَغِي لَنَآ أَن نَّتَّخِذَ مِن دُونِكَ مِنۡ أَوۡلِيَآءَ وَلَٰكِن مَّتَّعۡتَهُمۡ وَءَابَآءَهُمۡ حَتَّىٰ نَسُواْ ٱلذِّكۡرَ وَكَانُواْ قَوۡمَۢا بُورٗا

Suka ce: “Tsarki ya tabbata gare Ka, bai zamanto ya dace da mu ba mu riqi wasu majivinta ba Kai ba, sai dai kuma Ka jiyar da su daxi ne tare da iyayensu har suka manta tuna Ka, suka kuwa kasance mutane hallakakku.”



السورة: Suratul Furqan

الآية : 19

فَقَدۡ كَذَّبُوكُم بِمَا تَقُولُونَ فَمَا تَسۡتَطِيعُونَ صَرۡفٗا وَلَا نَصۡرٗاۚ وَمَن يَظۡلِم مِّنكُمۡ نُذِقۡهُ عَذَابٗا كَبِيرٗا

To haqiqa sun qaryata ku game da abin da kuke faxa, to ba za ku samu wata makauta ba, ko kuma wani taimako. Duk wanda kuma ya yi zalunci daga cikinku za Mu xanxana masa azaba mai girma



السورة: Suratul Furqan

الآية : 20

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا قَبۡلَكَ مِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ إِلَّآ إِنَّهُمۡ لَيَأۡكُلُونَ ٱلطَّعَامَ وَيَمۡشُونَ فِي ٱلۡأَسۡوَاقِۗ وَجَعَلۡنَا بَعۡضَكُمۡ لِبَعۡضٖ فِتۡنَةً أَتَصۡبِرُونَۗ وَكَانَ رَبُّكَ بَصِيرٗا

Kuma ba Mu aiko manzanni ba gabaninka sai cewa lalle suna cin abinci kuma suna tafiya cikin kasuwanni. Mun kuwa sanya wasunku su zama fitina ga wasu. Shin za ku yi haquri? Ubangijinka kuwa Ya kasance Mai gani ne



السورة: Suratul Furqan

الآية : 21

۞وَقَالَ ٱلَّذِينَ لَا يَرۡجُونَ لِقَآءَنَا لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡنَا ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ أَوۡ نَرَىٰ رَبَّنَاۗ لَقَدِ ٱسۡتَكۡبَرُواْ فِيٓ أَنفُسِهِمۡ وَعَتَوۡ عُتُوّٗا كَبِيرٗا

Waxanda kuma ba sa tsammanin haxuwa da Mu suka ce: “Me ya hana a saukar mana da mala’iku ko kuma mu ga Ubangijinmu?” Haqiqa lalle sun yi girman kai don (suna) ji da kawunansu, suka kuma yi tsaurin kai babba qwarai da gaske



السورة: Suratul Furqan

الآية : 22

يَوۡمَ يَرَوۡنَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ لَا بُشۡرَىٰ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُجۡرِمِينَ وَيَقُولُونَ حِجۡرٗا مَّحۡجُورٗا

Ranar da za su ga mala’iku[1] a wannan ranar babu wani farin ciki ga masu laifi, za kuma su riqa cewa: “(Albishir daga Allah) haramun ne abin haramtawa ne (a gare su)”


1- Watau ranar mutuwarsu ko a cikin qaburburansu da ranar da za a kora su domin yi musu hisabi.


السورة: Suratul Furqan

الآية : 23

وَقَدِمۡنَآ إِلَىٰ مَا عَمِلُواْ مِنۡ عَمَلٖ فَجَعَلۡنَٰهُ هَبَآءٗ مَّنثُورًا

Muka kuma gabato zuwa ga duk wani aiki da suka yi, sai Muka mai da shi qura abar xaixaitawa



السورة: Suratul Furqan

الآية : 24

أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِ يَوۡمَئِذٍ خَيۡرٞ مُّسۡتَقَرّٗا وَأَحۡسَنُ مَقِيلٗا

‘Yan Aljanna a wannan ranar su suka fi kyakkyawan mazauni kuma suka fi kyawon wurin barcin qailula[1]


1- Domin za a gama hisabi gabanin lokacin azahar, har ‘yan Aljanna za su shige ta su riski lokacin qailula a cikinta.


السورة: Suratul Furqan

الآية : 25

وَيَوۡمَ تَشَقَّقُ ٱلسَّمَآءُ بِٱلۡغَمَٰمِ وَنُزِّلَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ تَنزِيلًا

Kuma (ka tuna) ranar da sama za ta kekkece da girgije, kuma a saukar da mala’iku gungu-gungu



السورة: Suratul Furqan

الآية : 26

ٱلۡمُلۡكُ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡحَقُّ لِلرَّحۡمَٰنِۚ وَكَانَ يَوۡمًا عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ عَسِيرٗا

Mulki tabbatacce a wannan ranar na (Allah) Mai rahama ne. Kuma ta kasance rana ce mawuyaciya ga kafurai



السورة: Suratul Furqan

الآية : 27

وَيَوۡمَ يَعَضُّ ٱلظَّالِمُ عَلَىٰ يَدَيۡهِ يَقُولُ يَٰلَيۡتَنِي ٱتَّخَذۡتُ مَعَ ٱلرَّسُولِ سَبِيلٗا

(Ka tuna) kuma ranar da azzalumi zai riqa cizon yatsunsa yana cewa: “Ina ma na bi hanya tare da Manzo!



السورة: Suratul Furqan

الآية : 28

يَٰوَيۡلَتَىٰ لَيۡتَنِي لَمۡ أَتَّخِذۡ فُلَانًا خَلِيلٗا

“Kaicona ina ma da ban riqi wane aboki ba!



السورة: Suratul Furqan

الآية : 29

لَّقَدۡ أَضَلَّنِي عَنِ ٱلذِّكۡرِ بَعۡدَ إِذۡ جَآءَنِيۗ وَكَانَ ٱلشَّيۡطَٰنُ لِلۡإِنسَٰنِ خَذُولٗا

“Haqiqa ya vatar da ni daga bin Alqur’ani, bayan ya zo mini.” Shaixan kuwa ya kasance mai tavar da mutum ne



السورة: Suratul Furqan

الآية : 30

وَقَالَ ٱلرَّسُولُ يَٰرَبِّ إِنَّ قَوۡمِي ٱتَّخَذُواْ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ مَهۡجُورٗا

Manzo kuma ya ce: “Ya Ubangijina, lalle mutanena sun riqi wannan Alqur’ani abin qaurace wa[1].”


1- Watau ta hanyar guje wa sauraron sa da rashin karanta shi da aiki da koyarwarsa.