السورة: Suratul Baqara

الآية : 110

وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَۚ وَمَا تُقَدِّمُواْ لِأَنفُسِكُم مِّنۡ خَيۡرٖ تَجِدُوهُ عِندَ ٱللَّهِۗ إِنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

Kuma ku tsayar da salla ku kuma ba da zakka; kuma duk abin da kuka aikata na alheri domin kawunanku za ku same shi a wajen Allah. Lalle Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne



السورة: Suratul Baqara

الآية : 184

أَيَّامٗا مَّعۡدُودَٰتٖۚ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوۡ عَلَىٰ سَفَرٖ فَعِدَّةٞ مِّنۡ أَيَّامٍ أُخَرَۚ وَعَلَى ٱلَّذِينَ يُطِيقُونَهُۥ فِدۡيَةٞ طَعَامُ مِسۡكِينٖۖ فَمَن تَطَوَّعَ خَيۡرٗا فَهُوَ خَيۡرٞ لَّهُۥۚ وَأَن تَصُومُواْ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

Waxansu kwanaki ne qididdigaggu. To duk wanda ya kasance marar lafiya a cikinku ko a kan wata tafiya, to (idan ya sha azumi) sai ya rama a waxansu kwanakin na daban. Kuma waxanda za su yi azumi da wahala su ba da fansa ta ciyar da miskini; to duk wanda ya qara (a kan abincin miskini), to wannan alheri ne gare shi. Amma ku yi azumin shi ne ya fi muku alheri, in har kun kusance kuna sani



السورة: Suratul Baqara

الآية : 195

وَأَنفِقُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلَا تُلۡقُواْ بِأَيۡدِيكُمۡ إِلَى ٱلتَّهۡلُكَةِ وَأَحۡسِنُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Kuma ku ciyar da dukiyoyinku a hanyar Allah, kuma kada ku jefa kawunanku zuwa ga halaka, kuma ku kyautata; lalle Allah Yana son masu kyautatawa



السورة: Suratul Baqara

الآية : 215

يَسۡـَٔلُونَكَ مَاذَا يُنفِقُونَۖ قُلۡ مَآ أَنفَقۡتُم مِّنۡ خَيۡرٖ فَلِلۡوَٰلِدَيۡنِ وَٱلۡأَقۡرَبِينَ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِۗ وَمَا تَفۡعَلُواْ مِنۡ خَيۡرٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِهِۦ عَلِيمٞ

Suna tambayar ka, me za su ciyar ne? Ka ce: “Duk abin da za ku ciyar na alheri, to ga mahaifa da dangi mafiya kusanci da marayu da miskinai da matafiyi. Kuma duk abin da kuka aikata na alheri, to lalle Allah Masani ne da shi.”



السورة: Suratul Baqara

الآية : 269

يُؤۡتِي ٱلۡحِكۡمَةَ مَن يَشَآءُۚ وَمَن يُؤۡتَ ٱلۡحِكۡمَةَ فَقَدۡ أُوتِيَ خَيۡرٗا كَثِيرٗاۗ وَمَا يَذَّكَّرُ إِلَّآ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ

Yana bayar da hikima ga wanda Ya ga dama; kuma dukkan wanda aka bai wa hikima, to haqiqa an ba shi alheri mai tarin yawa. Kuma ba wanda yake wa’azantuwa sai ma’abota hankula



السورة: Suratul Baqara

الآية : 272

۞لَّيۡسَ عَلَيۡكَ هُدَىٰهُمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَهۡدِي مَن يَشَآءُۗ وَمَا تُنفِقُواْ مِنۡ خَيۡرٖ فَلِأَنفُسِكُمۡۚ وَمَا تُنفِقُونَ إِلَّا ٱبۡتِغَآءَ وَجۡهِ ٱللَّهِۚ وَمَا تُنفِقُواْ مِنۡ خَيۡرٖ يُوَفَّ إِلَيۡكُمۡ وَأَنتُمۡ لَا تُظۡلَمُونَ

Shiryar da su ba a kanka yake ba, sai dai Allah ne Yake shiryar da wanda Ya ga dama, kuma duk abin da kuka ciyar na alheri, to domin kawunanku ne, kuma ba za ku ciyar ba sai don neman yardar Allah; kuma duk abin da kuka ciyar na alheri, za a cika muku ladansa, alhali kuma ba za a zalunce ku ba



السورة: Suratul Baqara

الآية : 273

لِلۡفُقَرَآءِ ٱلَّذِينَ أُحۡصِرُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ لَا يَسۡتَطِيعُونَ ضَرۡبٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ يَحۡسَبُهُمُ ٱلۡجَاهِلُ أَغۡنِيَآءَ مِنَ ٱلتَّعَفُّفِ تَعۡرِفُهُم بِسِيمَٰهُمۡ لَا يَسۡـَٔلُونَ ٱلنَّاسَ إِلۡحَافٗاۗ وَمَا تُنفِقُواْ مِنۡ خَيۡرٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِهِۦ عَلِيمٌ

Ga mabuqata waxanda aka tsare saboda Allah, ba su da ikon yawatawa a bayan qasa, har wanda ya jahilci halinsu yana zato su mawadata ne saboda kame kai; za ka gane su ne da alamominsu, ba sa naciyar roqar mutane, kuma duk abin da kuka ciyar na alheri, to Allah Yana sane da shi



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 104

وَلۡتَكُن مِّنكُمۡ أُمَّةٞ يَدۡعُونَ إِلَى ٱلۡخَيۡرِ وَيَأۡمُرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِۚ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

A cikinku lalle a sami wata al’umma waxanda suke kira zuwa ga alheri, kuma suke umarni da kyakkyawa, kuma suke hana mummuna. Waxannan su ne masu rabauta



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 114

يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَيَأۡمُرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَيُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡخَيۡرَٰتِۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ مِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

Suna yin imani da Allah da ranar qarshe, kuma suna umarni da kyakkyawan aiki, kuma suna hana mummuna, kuma suna hanzari wajen ayyukan alheri, waxannan kuwa suna cikin salihan bayi



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 115

وَمَا يَفۡعَلُواْ مِنۡ خَيۡرٖ فَلَن يُكۡفَرُوهُۗ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِٱلۡمُتَّقِينَ

Kuma duk abin da suka aikata na alheri, to ba za a hana musu ladansa ba. Kuma Allah Yana sane da masu taqawa



السورة: Suratun Nisa’i

الآية : 36

۞وَٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَلَا تُشۡرِكُواْ بِهِۦ شَيۡـٔٗاۖ وَبِٱلۡوَٰلِدَيۡنِ إِحۡسَٰنٗا وَبِذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱلۡجَارِ ذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡجَارِ ٱلۡجُنُبِ وَٱلصَّاحِبِ بِٱلۡجَنۢبِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِ وَمَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ مَن كَانَ مُخۡتَالٗا فَخُورًا

Kuma ku bauta wa Allah (Shi kaxai), kada ku haxa Shi da komai; kuma ku kyautata wa iyaye da dangi makusanta da marayu da talakawa da maqwabci makusanci da maqwabci na nesa, da abokin da ake tare[1] da kuma matafiyi da bayinku. Lalle Allah ba Ya son duk wanda ya kasance mai taqama, mai yawan fariya


1- Watau wanda tafiya ta haxa mutun da shi ko kuma matarsa.


السورة: Suratu Hud

الآية : 114

وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ طَرَفَيِ ٱلنَّهَارِ وَزُلَفٗا مِّنَ ٱلَّيۡلِۚ إِنَّ ٱلۡحَسَنَٰتِ يُذۡهِبۡنَ ٱلسَّيِّـَٔاتِۚ ذَٰلِكَ ذِكۡرَىٰ لِلذَّـٰكِرِينَ

Ka kuma tsai da salla farkon rana da qarshenta da kuma farkon dare. Lalle kyawawan (ayyuka) suna shafe munana. Wannan tunasarwa ne ga masu tunawa



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 24

أَلَمۡ تَرَ كَيۡفَ ضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا كَلِمَةٗ طَيِّبَةٗ كَشَجَرَةٖ طَيِّبَةٍ أَصۡلُهَا ثَابِتٞ وَفَرۡعُهَا فِي ٱلسَّمَآءِ

Shin ba ka ga yadda Allah Ya ba da misali ba? Daddaxar kalma[1] kamar daddaxar bishiya ce[2] wadda tushenta kafaffe ne (a qasa) reshenta kuma yana sama


1- Daddaxar kalma ita ce kalmar shahada, watau shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah.


2- Daddaxar bishiya kuwa ita ce bishiyar dabino. A nan ana nufin mumini. Kalmar shahada tana kafa tushenta a ciki zuciyar mumini.


السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 25

تُؤۡتِيٓ أُكُلَهَا كُلَّ حِينِۭ بِإِذۡنِ رَبِّهَاۗ وَيَضۡرِبُ ٱللَّهُ ٱلۡأَمۡثَالَ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَتَذَكَّرُونَ

Tana bayar da ‘ya’yanta ko da yaushe da izinin Ubangijinta. Allah kuwa Yana ba da misalai ne ga mutane don su wa’azantu



السورة: Suratun Nahl

الآية : 90

۞إِنَّ ٱللَّهَ يَأۡمُرُ بِٱلۡعَدۡلِ وَٱلۡإِحۡسَٰنِ وَإِيتَآيِٕ ذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَيَنۡهَىٰ عَنِ ٱلۡفَحۡشَآءِ وَٱلۡمُنكَرِ وَٱلۡبَغۡيِۚ يَعِظُكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ

Lalle Allah Yana umarni da yin adalci da kyautatawa da kuma bai wa makusanta (taimako), Yana kuma hana alfasha da mummunan aiki da zalunci. Yana gargaxin ku don ku wa’azantu



السورة: Suratun Nahl

الآية : 125

ٱدۡعُ إِلَىٰ سَبِيلِ رَبِّكَ بِٱلۡحِكۡمَةِ وَٱلۡمَوۡعِظَةِ ٱلۡحَسَنَةِۖ وَجَٰدِلۡهُم بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِٱلۡمُهۡتَدِينَ

Ka yi kira zuwa ga tafarkin Ubangiijnka cikin hikima da kyakkyawan wa’azi, ka kuma yi jayayya da su ta hanyar da ta fi kyau. Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sanin wanda ya vace daga hanyarsa, kuma Shi ne Mafi sanin shiryayyu



السورة: Suratul Hajji

الآية : 77

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱرۡكَعُواْ وَٱسۡجُدُواْۤ وَٱعۡبُدُواْ رَبَّكُمۡ وَٱفۡعَلُواْ ٱلۡخَيۡرَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ۩

Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi ruku’i kuma ku yi sujjada, ku kuma bauta wa Ubangijinku, kuma ku aikata alheri don ku rabauta



السورة: Suratun Nur

الآية : 26

ٱلۡخَبِيثَٰتُ لِلۡخَبِيثِينَ وَٱلۡخَبِيثُونَ لِلۡخَبِيثَٰتِۖ وَٱلطَّيِّبَٰتُ لِلطَّيِّبِينَ وَٱلطَّيِّبُونَ لِلطَّيِّبَٰتِۚ أُوْلَـٰٓئِكَ مُبَرَّءُونَ مِمَّا يَقُولُونَۖ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَرِزۡقٞ كَرِيمٞ

Miyagun mata da miyagun maganganu sun dace da miyagun maza. Kuma miyagun maza da miyagun maganganu sun dace ne da miyagun mata. Tsarkakan mata da tsarkakan maganganu sun dace da tsarkakan maza. Kuma tsarkakan maza da tsakakan maganganu sun dace da tsarkakan mata. Su waxannan (tsarkaka) kuwa wankakakku ne daga abin da suke faxa (na qage a kansu), suna da (sakamakon) gafara da arziki mai girma



السورة: Suratu Faxir

الآية : 10

مَن كَانَ يُرِيدُ ٱلۡعِزَّةَ فَلِلَّهِ ٱلۡعِزَّةُ جَمِيعًاۚ إِلَيۡهِ يَصۡعَدُ ٱلۡكَلِمُ ٱلطَّيِّبُ وَٱلۡعَمَلُ ٱلصَّـٰلِحُ يَرۡفَعُهُۥۚ وَٱلَّذِينَ يَمۡكُرُونَ ٱلسَّيِّـَٔاتِ لَهُمۡ عَذَابٞ شَدِيدٞۖ وَمَكۡرُ أُوْلَـٰٓئِكَ هُوَ يَبُورُ

Wanda ya zamanto yana nufin xaukaka, to xaukaka gaba xayanta ta Allah ce. Daxaxan kalmomi[1] zuwa wurinsa suke hawa, kyakkyawan aiki kuwa shi yake xaukaka shi. Waxanda kuwa suke shirya makirci suna da (sakamakon) azaba mai tsanani, kuma makircin waxannan shi ne yake lalacewa


1- Watau kamar kalmar shahada da karatun Alqur’ani da ambaton Allah.


السورة: Suratu Fussilat

الآية : 33

وَمَنۡ أَحۡسَنُ قَوۡلٗا مِّمَّن دَعَآ إِلَى ٱللَّهِ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا وَقَالَ إِنَّنِي مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

Wane ne ya fi kyakkyawar magana fiye da wanda ya yi kira zuwa ga Allah ya kuma yi aiki nagari, kuma ya ce: “Lalle ni ina daga cikin Musulmi?”



السورة: Suratul Muzzammil

الآية : 20

۞إِنَّ رَبَّكَ يَعۡلَمُ أَنَّكَ تَقُومُ أَدۡنَىٰ مِن ثُلُثَيِ ٱلَّيۡلِ وَنِصۡفَهُۥ وَثُلُثَهُۥ وَطَآئِفَةٞ مِّنَ ٱلَّذِينَ مَعَكَۚ وَٱللَّهُ يُقَدِّرُ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَۚ عَلِمَ أَن لَّن تُحۡصُوهُ فَتَابَ عَلَيۡكُمۡۖ فَٱقۡرَءُواْ مَا تَيَسَّرَ مِنَ ٱلۡقُرۡءَانِۚ عَلِمَ أَن سَيَكُونُ مِنكُم مَّرۡضَىٰ وَءَاخَرُونَ يَضۡرِبُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ يَبۡتَغُونَ مِن فَضۡلِ ٱللَّهِ وَءَاخَرُونَ يُقَٰتِلُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۖ فَٱقۡرَءُواْ مَا تَيَسَّرَ مِنۡهُۚ وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَقۡرِضُواْ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنٗاۚ وَمَا تُقَدِّمُواْ لِأَنفُسِكُم مِّنۡ خَيۡرٖ تَجِدُوهُ عِندَ ٱللَّهِ هُوَ خَيۡرٗا وَأَعۡظَمَ أَجۡرٗاۚ وَٱسۡتَغۡفِرُواْ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمُۢ

Lalle Ubangijinka Yana sane da cewa kai kana tsayawa qasa da kashi biyu cikin uku na dare, da kuma rabinsa, da kuma xaya bisa ukunsa, kai da wata jama’ar da take tare da kai. Allah ne kuma Yake qaddara dare da rana. Ya san kuma cewa, ba za ku iya qididdige (sa’o’insa) ba, don haka sai Ya yafe muku; to sai ku karanta abin da ya sauqaqa daga Alqur’ani. Ya san cewa daga cikinku akwai waxanda za su kasance marasa lafiya, waxansu kuma suna tafiya a bayan qasa don fatauci suna neman falala daga Allah, waxansu kuma suna yin yaqi saboda Allah; to sai ku karanta abin da ya sauqaqa daga gare shi (Alqur’ani). Ku kuma tsayar da salla, ku kuma ba da zakka, kuma ku bai wa Allah rance kyakkyawa[1]. Kuma abin da kuka gabatar wa kanku na wani alheri, to za ku same shi wurin Allah, shi ya fi alheri ya kuma fi girman lada. Ku kuma nemi gafarar Allah; lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai


1- Watau su ciyar da dukiyoyinsu don Allah wuraren da suka dace.


السورة: Suratuz Zalzala

الآية : 7

فَمَن يَعۡمَلۡ مِثۡقَالَ ذَرَّةٍ خَيۡرٗا يَرَهُۥ

To duk wanda ya yi aikin alheri daidai da zarra zai gan shi