السورة: Suratun Najm

الآية : 23

إِنۡ هِيَ إِلَّآ أَسۡمَآءٞ سَمَّيۡتُمُوهَآ أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بِهَا مِن سُلۡطَٰنٍۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَمَا تَهۡوَى ٱلۡأَنفُسُۖ وَلَقَدۡ جَآءَهُم مِّن رَّبِّهِمُ ٱلۡهُدَىٰٓ

Su ba komai ba ne face sunaye da kuka sa musu, ku da iyayenku, Allah bai saukar muku da wata hujja ba game da su. Ba abin da suke bi sai zato da son zuciya. Haqiqa kuwa shiriya ta zo musu daga Ubangijinsu



السورة: Suratus Saff 

الآية : 7

وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ وَهُوَ يُدۡعَىٰٓ إِلَى ٱلۡإِسۡلَٰمِۚ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Ba wanda kuma ya fi zalunci kamar wanda ya qaga wa Allah qarya, alhali kuwa shi ana kiran sa zuwa Musulunci. Allah kuma ba Ya shiryar da mutane azzalumai



السورة: Suratun Nazi’at

الآية : 24

فَقَالَ أَنَا۠ رَبُّكُمُ ٱلۡأَعۡلَىٰ

Sai ya ce, “Ni ne ubangijinku mafi girma!”