السورة: Suratul Hajji

الآية : 73

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ضُرِبَ مَثَلٞ فَٱسۡتَمِعُواْ لَهُۥٓۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَن يَخۡلُقُواْ ذُبَابٗا وَلَوِ ٱجۡتَمَعُواْ لَهُۥۖ وَإِن يَسۡلُبۡهُمُ ٱلذُّبَابُ شَيۡـٔٗا لَّا يَسۡتَنقِذُوهُ مِنۡهُۚ ضَعُفَ ٱلطَّالِبُ وَٱلۡمَطۡلُوبُ

Ya ku mutane, an ba da misali, to sai ku saurare shi. Lalle waxanda kuke bauta wa ba Allah ba, ba za su tava iya halittar quda ba, ko da sun taru domin (halitta) shi; idan kuma da qudan zai cire musu (su gumakan) wani abu, to ba za su iya qwato shi ba daga wurinsa. Wanda yake nema da wanda ake nema (duka) sun yi rauni!



السورة: Suratun Nur

الآية : 35

۞ٱللَّهُ نُورُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ مَثَلُ نُورِهِۦ كَمِشۡكَوٰةٖ فِيهَا مِصۡبَاحٌۖ ٱلۡمِصۡبَاحُ فِي زُجَاجَةٍۖ ٱلزُّجَاجَةُ كَأَنَّهَا كَوۡكَبٞ دُرِّيّٞ يُوقَدُ مِن شَجَرَةٖ مُّبَٰرَكَةٖ زَيۡتُونَةٖ لَّا شَرۡقِيَّةٖ وَلَا غَرۡبِيَّةٖ يَكَادُ زَيۡتُهَا يُضِيٓءُ وَلَوۡ لَمۡ تَمۡسَسۡهُ نَارٞۚ نُّورٌ عَلَىٰ نُورٖۚ يَهۡدِي ٱللَّهُ لِنُورِهِۦ مَن يَشَآءُۚ وَيَضۡرِبُ ٱللَّهُ ٱلۡأَمۡثَٰلَ لِلنَّاسِۗ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ

Allah ne hasken sammai da qasa[1]. Misalin haskensa tamkar alkuki ne da fitila take a cikinsa; fitilar kuma tana cikin qarau; qaran kuma tamkar tauraro ne na lu’ulu’u, ana kunna ta da man bishiya mai albarka ta zaitun, ita ba daga mahudar rana take ba kuma ba daga mafaxarta ba, kuma manta kamar zai kama da kansa ko da wuta ba ta tava shi ba. Haske kan haske. Allah Yana shiryar da wanda Ya ga dama zuwa ga haskensa. Kuma Allah yana buga misalai ne ga mutane. Allah kuwa Masanin komai ne


1- Kuma shi ne mai haskaka zukatan muminai mai shiryar da su.


السورة: Suratun Nur

الآية : 36

فِي بُيُوتٍ أَذِنَ ٱللَّهُ أَن تُرۡفَعَ وَيُذۡكَرَ فِيهَا ٱسۡمُهُۥ يُسَبِّحُ لَهُۥ فِيهَا بِٱلۡغُدُوِّ وَٱلۡأٓصَالِ

(Hasken) yana cikin wasu xakuna (watau masallatai) waxanda Allah Ya yi umarni a xaukaka, a kuma ambaci sunansa a cikinsu. (Wasu mazaje) suna tasbihi gare Shi a cikinsu safe da yamma



السورة: Suratun Nur

الآية : 39

وَٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَعۡمَٰلُهُمۡ كَسَرَابِۭ بِقِيعَةٖ يَحۡسَبُهُ ٱلظَّمۡـَٔانُ مَآءً حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَهُۥ لَمۡ يَجِدۡهُ شَيۡـٔٗا وَوَجَدَ ٱللَّهَ عِندَهُۥ فَوَفَّىٰهُ حِسَابَهُۥۗ وَٱللَّهُ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

Waxanda kuwa suka kafirta ayyukansu kamar kawalwalniya ne a wani faqo wanda mai jin tsananin qishirwa yake zaton ruwa ne, har lokacin da ya zo gare ta ba zai samu komai ba sai ya sami Allah a wurinsa, sai Ya cika masa hisabinsa. Allah kuwa Mai saurin hisabi ne



السورة: Suratun Nur

الآية : 40

أَوۡ كَظُلُمَٰتٖ فِي بَحۡرٖ لُّجِّيّٖ يَغۡشَىٰهُ مَوۡجٞ مِّن فَوۡقِهِۦ مَوۡجٞ مِّن فَوۡقِهِۦ سَحَابٞۚ ظُلُمَٰتُۢ بَعۡضُهَا فَوۡقَ بَعۡضٍ إِذَآ أَخۡرَجَ يَدَهُۥ لَمۡ يَكَدۡ يَرَىٰهَاۗ وَمَن لَّمۡ يَجۡعَلِ ٱللَّهُ لَهُۥ نُورٗا فَمَا لَهُۥ مِن نُّورٍ

Ko kuma kamar duffai a cikin kogi mai zurfi da raqumin ruwa ya lulluve shi, daga samansa kuma akwai wani raqumin ruwan, daga samansa (kuma) akwai wani hadari. Duffai wasu a kan wasu; idan ya fito da hannunsa ba zai iya ganin sa ba. Wanda kuma Allah bai sanya wa haske ba, to ba shi da wani haske



السورة: Suratul Ankabut

الآية : 41

مَثَلُ ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَوۡلِيَآءَ كَمَثَلِ ٱلۡعَنكَبُوتِ ٱتَّخَذَتۡ بَيۡتٗاۖ وَإِنَّ أَوۡهَنَ ٱلۡبُيُوتِ لَبَيۡتُ ٱلۡعَنكَبُوتِۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ

Misalin waxanda suka riqi wasu iyayen giji ba Allah ba, kamar misalin gizo-gizo ne da ya saqa gida; haqiqa kuwa lalle gidan gizo-gizo shi ya fi kowanne gida rauni, da sun kasance suna sanin (haka)



السورة: Suratul Ankabut

الآية : 42

إِنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ مِن شَيۡءٖۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

Lalle Allah Yana sane da kowane abu da suke bauta wa wanda ba Shi ba. Kuma Shi ne Mabuwayi, Mai hikima



السورة: Suratul Ankabut

الآية : 43

وَتِلۡكَ ٱلۡأَمۡثَٰلُ نَضۡرِبُهَا لِلنَّاسِۖ وَمَا يَعۡقِلُهَآ إِلَّا ٱلۡعَٰلِمُونَ

Waxancan misalan Muna ba da su ne ga mutane; ba kuwa wanda yake hankaltar su sai malamai kawai



السورة: Suratur Rum

الآية : 28

ضَرَبَ لَكُم مَّثَلٗا مِّنۡ أَنفُسِكُمۡۖ هَل لَّكُم مِّن مَّا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُم مِّن شُرَكَآءَ فِي مَا رَزَقۡنَٰكُمۡ فَأَنتُمۡ فِيهِ سَوَآءٞ تَخَافُونَهُمۡ كَخِيفَتِكُمۡ أَنفُسَكُمۡۚ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ

Ya ba ku misali daga kawunanku; shin kuna da wasu abokan tarayya daga bayinku da kuka mallaka a kan abin da Muka arzuta ku (da shi), ku da su ku zama daidai kuke game da wannan; kuna ma jin tsoron su kamar yanda kuke tsoron junanku? Kamar haka Muke rarrabe ayoyin (filla-filla) ga mutanen da suke hankalta



السورة: Suratuz Zumar

الآية : 29

ضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا رَّجُلٗا فِيهِ شُرَكَآءُ مُتَشَٰكِسُونَ وَرَجُلٗا سَلَمٗا لِّرَجُلٍ هَلۡ يَسۡتَوِيَانِ مَثَلًاۚ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

Allah Ya ba da misali na wani namiji (bawa) wanda yake da iyayen giji masu tarayya a kansa masu jayayya (a kan ba shi umarni) da kuma wani namiiji (bawa) da ya kevanta ga wani namiji guda, shin misalinsu za su yi daidai? Dukkan yabo ya tabbata ga Allah. A’a, yawancinsu dai ba su sani ba ne



السورة: Suratul Fat’h

الآية : 29

مُّحَمَّدٞ رَّسُولُ ٱللَّهِۚ وَٱلَّذِينَ مَعَهُۥٓ أَشِدَّآءُ عَلَى ٱلۡكُفَّارِ رُحَمَآءُ بَيۡنَهُمۡۖ تَرَىٰهُمۡ رُكَّعٗا سُجَّدٗا يَبۡتَغُونَ فَضۡلٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِضۡوَٰنٗاۖ سِيمَاهُمۡ فِي وُجُوهِهِم مِّنۡ أَثَرِ ٱلسُّجُودِۚ ذَٰلِكَ مَثَلُهُمۡ فِي ٱلتَّوۡرَىٰةِۚ وَمَثَلُهُمۡ فِي ٱلۡإِنجِيلِ كَزَرۡعٍ أَخۡرَجَ شَطۡـَٔهُۥ فَـَٔازَرَهُۥ فَٱسۡتَغۡلَظَ فَٱسۡتَوَىٰ عَلَىٰ سُوقِهِۦ يُعۡجِبُ ٱلزُّرَّاعَ لِيَغِيظَ بِهِمُ ٱلۡكُفَّارَۗ وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ مِنۡهُم مَّغۡفِرَةٗ وَأَجۡرًا عَظِيمَۢا

Muhammadu Manzon Allah ne. Waxanda kuma suke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, kuma masu tausayin junansu ne; za ka gan su suna ruku’i suna sujjada suna neman falala daga Allah da yardarsa; alamominsu na gurbin sujjada suna bayyana a fuskokinsu. Wannan shi ne misalinsu a cikin Attaura. Misalinsu kuwa a cikin Linjila kamar shuka ce da ta fitar da reshenta sai ya qarfafe ta, sannan ta yi kauri sai ta daidaita a kan tushiyarta ta riqa qayatar da manoma, don Ya cusa wa kafirai haushi. Allah Ya yi wa waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari daga cikinsu alqawarin gafara da lada mai girma



السورة: Suratul Hadid

الآية : 20

ٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا لَعِبٞ وَلَهۡوٞ وَزِينَةٞ وَتَفَاخُرُۢ بَيۡنَكُمۡ وَتَكَاثُرٞ فِي ٱلۡأَمۡوَٰلِ وَٱلۡأَوۡلَٰدِۖ كَمَثَلِ غَيۡثٍ أَعۡجَبَ ٱلۡكُفَّارَ نَبَاتُهُۥ ثُمَّ يَهِيجُ فَتَرَىٰهُ مُصۡفَرّٗا ثُمَّ يَكُونُ حُطَٰمٗاۖ وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِ عَذَابٞ شَدِيدٞ وَمَغۡفِرَةٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَرِضۡوَٰنٞۚ وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَآ إِلَّا مَتَٰعُ ٱلۡغُرُورِ

Ku sani cewa, ita dai rayuwar duniya ba wata aba ba ce sai wasa da sharholiya da qyale-qyale da kuma fariya a tsakaninku da takara wajan nuna yawan dukiya da ‘ya’yaye; ta yi kama da ruwan saman da tsirransa suka bai wa manoma sha’awa, sannan duk ya bushe, sai ka gan shi fatsi-fatsi, sannan kuma ya zama dudduga; a lahira kuwa akwai azaba mai tsanani da gafara daga Allah da kuma yarda. Rayuwar duniya ba komai ba ce sai jin daxi mai ruxi



السورة: Suratul Hashr

الآية : 21

لَوۡ أَنزَلۡنَا هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ عَلَىٰ جَبَلٖ لَّرَأَيۡتَهُۥ خَٰشِعٗا مُّتَصَدِّعٗا مِّنۡ خَشۡيَةِ ٱللَّهِۚ وَتِلۡكَ ٱلۡأَمۡثَٰلُ نَضۡرِبُهَا لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَتَفَكَّرُونَ

Da za Mu saukar da wannan Alqur’ani ga wani dutse, da lalle ka gan shi yana mai qasqantar da kai mai tsattsagewa don tsoron Allah. Waxannan misalan Muna buga wa mutane su ne don su yi tunani



السورة: Suratul Jumu’a

الآية : 5

مَثَلُ ٱلَّذِينَ حُمِّلُواْ ٱلتَّوۡرَىٰةَ ثُمَّ لَمۡ يَحۡمِلُوهَا كَمَثَلِ ٱلۡحِمَارِ يَحۡمِلُ أَسۡفَارَۢاۚ بِئۡسَ مَثَلُ ٱلۡقَوۡمِ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِۚ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Misalin waxanda aka xora wa Attaura[1] sannan ba su xauke ta ba, kamar misalin jaki ne da yake xauke da wagagen littattafai. Misalin mutanen da suka qaryata ayoyin Allah ya munana. Allah kuwa ba Ya shiryar da mutane azzalumai


1- Su ne malaman Yahudawa da Allah ya sanar da su Attaura; ya umarce su su yi aiki da ita.