لِّتَسۡلُكُواْ مِنۡهَا سُبُلٗا فِجَاجٗا
“Don ku riqa bin manya-manyan hanyoyi a cikinta.”
أَلَمۡ نَجۡعَلِ ٱلۡأَرۡضَ كِفَاتًا
Yanzu ba Mu sanya qasa (ta zama) matattara ba?
أَحۡيَآءٗ وَأَمۡوَٰتٗا
(Ga) rayayyu da matattu[1]?
1- Watau masu rai a cikin gidajensu a bayanta, matatu kuma a binne a cikin qaburburansu a qarqashinta.
وَجَعَلۡنَا فِيهَا رَوَٰسِيَ شَٰمِخَٰتٖ وَأَسۡقَيۡنَٰكُم مَّآءٗ فُرَاتٗا
Muka kuma sanya kafaffun duwatsu dogaye a cikinta, Muka kuma shayar da ku ruwa mai daxi?
أَلَمۡ نَجۡعَلِ ٱلۡأَرۡضَ مِهَٰدٗا
Yanzu ba mu sanya qasa shimfixa ba?
وَٱلۡجِبَالَ أَوۡتَادٗا
Duwatsu kuma turaku?
ثُمَّ شَقَقۡنَا ٱلۡأَرۡضَ شَقّٗا
Sannan Muka tsaga qasa tsagawa
فَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا حَبّٗا
Sai Muka tsiro da qwaya daga cikinta
وَعِنَبٗا وَقَضۡبٗا
Da inabai da ciyayi
وَزَيۡتُونٗا وَنَخۡلٗا
Da zaitun da dabino
وَحَدَآئِقَ غُلۡبٗا
Da gonaki cike da itatuwa
وَفَٰكِهَةٗ وَأَبّٗا
Da kayan marmari da makiyaya
مَّتَٰعٗا لَّكُمۡ وَلِأَنۡعَٰمِكُمۡ
Don jin daxinku da na dabbobinku
وَإِلَى ٱلۡأَرۡضِ كَيۡفَ سُطِحَتۡ
Da kuma qasa yadda aka shimfixa ta?