السورة: Suratul Baqara

الآية : 102

وَٱتَّبَعُواْ مَا تَتۡلُواْ ٱلشَّيَٰطِينُ عَلَىٰ مُلۡكِ سُلَيۡمَٰنَۖ وَمَا كَفَرَ سُلَيۡمَٰنُ وَلَٰكِنَّ ٱلشَّيَٰطِينَ كَفَرُواْ يُعَلِّمُونَ ٱلنَّاسَ ٱلسِّحۡرَ وَمَآ أُنزِلَ عَلَى ٱلۡمَلَكَيۡنِ بِبَابِلَ هَٰرُوتَ وَمَٰرُوتَۚ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِنۡ أَحَدٍ حَتَّىٰ يَقُولَآ إِنَّمَا نَحۡنُ فِتۡنَةٞ فَلَا تَكۡفُرۡۖ فَيَتَعَلَّمُونَ مِنۡهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِۦ بَيۡنَ ٱلۡمَرۡءِ وَزَوۡجِهِۦۚ وَمَا هُم بِضَآرِّينَ بِهِۦ مِنۡ أَحَدٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَيَتَعَلَّمُونَ مَا يَضُرُّهُمۡ وَلَا يَنفَعُهُمۡۚ وَلَقَدۡ عَلِمُواْ لَمَنِ ٱشۡتَرَىٰهُ مَا لَهُۥ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنۡ خَلَٰقٖۚ وَلَبِئۡسَ مَا شَرَوۡاْ بِهِۦٓ أَنفُسَهُمۡۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ

Sai suka bi abin da shexanu suke karantawa a (zamanin) mulkin Sulaimanu; kuma Sulaimanu bai kafirta ba, sai dai shexanun su ne suka kafirta; suna koya wa mutane tsafi da abin da aka saukar wa mala’iku biyu, Haruta da Maruta, a garin Babila. Kuma ba sa koya wa wani (tsafin) har sai sun faxa masa cewa: “Mu fa jarraba ce, don haka kada ka kafirta”. Sai (mutane) suka riqa koyo daga wajensu su biyu abin da suke raba tsakanin miji da matarsa da shi. Kuma ba za su iya cutar da wani da shi ba sai da izinin Allah. Sai su koyi abin da zai cutar da su kuma ba zai amfane su ba. Kuma haqiqa sun san cewa, tabbas duk wanda ya zavi (sihiri) ba shi da wani rabo a lahira. Kuma lalle tir da abin da suka sayar da kawunansu da shi, da a ce sun san (haqiqanin makomarsu)



السورة: Suratul An’am

الآية : 71

قُلۡ أَنَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُنَا وَلَا يَضُرُّنَا وَنُرَدُّ عَلَىٰٓ أَعۡقَابِنَا بَعۡدَ إِذۡ هَدَىٰنَا ٱللَّهُ كَٱلَّذِي ٱسۡتَهۡوَتۡهُ ٱلشَّيَٰطِينُ فِي ٱلۡأَرۡضِ حَيۡرَانَ لَهُۥٓ أَصۡحَٰبٞ يَدۡعُونَهُۥٓ إِلَى ٱلۡهُدَى ٱئۡتِنَاۗ قُلۡ إِنَّ هُدَى ٱللَّهِ هُوَ ٱلۡهُدَىٰۖ وَأُمِرۡنَا لِنُسۡلِمَ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Ka ce: “Shin yanzu ma riqa bauta wa wani wanda ba Allah ba, abin da ba zai amfane mu ba, kuma ba zai cutar da mu ba, mu koma gidan jiya (kafirai) bayan kuwa Allah Ya shiryar da mu, (mu koma) kamar wanda shaixanu suka vatar da shi yana ta ximuwa a bayan qasa, ga shi da wasu abokai suna kiran sa zuwa ga shiriya, (suna cewa): “Ka zo (mu bi tafarkin shiriya)[1].” Ka ce: “Lalle shiriyar Allah fa ita kaxai ce shiriya; kuma mu an umarce mu da mu miqa wuya ne kaxai ga Ubangijin talikai


1- Misali ne na wanda ya saki Musulunci ya kama shirka ko vata, ya zama kamar mutumin da aljanu suka xauke shi suka tafi da shi suka jefar da shi a qurgurmin daji. Don haka ya yi nisan da ba zai ji kira ba, balle ya gane hanyar dawowa.


السورة: Suratul An’am

الآية : 112

وَكَذَٰلِكَ جَعَلۡنَا لِكُلِّ نَبِيٍّ عَدُوّٗا شَيَٰطِينَ ٱلۡإِنسِ وَٱلۡجِنِّ يُوحِي بَعۡضُهُمۡ إِلَىٰ بَعۡضٖ زُخۡرُفَ ٱلۡقَوۡلِ غُرُورٗاۚ وَلَوۡ شَآءَ رَبُّكَ مَا فَعَلُوهُۖ فَذَرۡهُمۡ وَمَا يَفۡتَرُونَ

Kuma kamar haka ne Muka sanya wa kowane annabi maqiya daga shaixanun mutane da aljannu, sashinsu yana kimsa wa wani sashi qayataccen zance, don ruxi. Kuma da Ubangijinka Ya ga dama da ba su aikata haka ba; don haka ka qyale su da irin abin da suke qagowa



السورة: Suratul An’am

الآية : 121

وَلَا تَأۡكُلُواْ مِمَّا لَمۡ يُذۡكَرِ ٱسۡمُ ٱللَّهِ عَلَيۡهِ وَإِنَّهُۥ لَفِسۡقٞۗ وَإِنَّ ٱلشَّيَٰطِينَ لَيُوحُونَ إِلَىٰٓ أَوۡلِيَآئِهِمۡ لِيُجَٰدِلُوكُمۡۖ وَإِنۡ أَطَعۡتُمُوهُمۡ إِنَّكُمۡ لَمُشۡرِكُونَ

Kuma kada ku ci daga abin da ba a ambaci sunan Allah a kansa ba, kuma lalle shi tabbas fasiqanci ne. Haqiqa shaixanu tabbas suna kimsa wa masoyansu, don su yi jayayya da ku; idan kuwa kuka bi su to lalle tabbas ku mushirikai ne



السورة: Suratul A’araf

الآية : 27

يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ لَا يَفۡتِنَنَّكُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ كَمَآ أَخۡرَجَ أَبَوَيۡكُم مِّنَ ٱلۡجَنَّةِ يَنزِعُ عَنۡهُمَا لِبَاسَهُمَا لِيُرِيَهُمَا سَوۡءَٰتِهِمَآۚ إِنَّهُۥ يَرَىٰكُمۡ هُوَ وَقَبِيلُهُۥ مِنۡ حَيۡثُ لَا تَرَوۡنَهُمۡۗ إِنَّا جَعَلۡنَا ٱلشَّيَٰطِينَ أَوۡلِيَآءَ لِلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ

Ya ku ‘yan’adam, kada Shaixan ya fitine ku kamar yadda ya fitar da iyayenku daga cikin Aljanna, yana mai cire musu tufafinsu don ya nuna musu tsiraicin junansu. Lalle shi yana ganin ku, shi da jama’arsa ta inda ku ba kwa ganin su. Lalle Mu Mun sanya shaixanu su zamo masoya ga waxanda ba sa yin imani



السورة: Suratul A’araf

الآية : 30

فَرِيقًا هَدَىٰ وَفَرِيقًا حَقَّ عَلَيۡهِمُ ٱلضَّلَٰلَةُۚ إِنَّهُمُ ٱتَّخَذُواْ ٱلشَّيَٰطِينَ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَيَحۡسَبُونَ أَنَّهُم مُّهۡتَدُونَ

Wani sashi Ya shirye su, wani sashin kuma vata ya tabbata a kansu. Lalle su sun mayar da shaixanu masoya ba Allah ba, suna kuma tsammanin cewa lalle su shiryayyu ne



السورة: Suratul Isra’i

الآية : 27

إِنَّ ٱلۡمُبَذِّرِينَ كَانُوٓاْ إِخۡوَٰنَ ٱلشَّيَٰطِينِۖ وَكَانَ ٱلشَّيۡطَٰنُ لِرَبِّهِۦ كَفُورٗا

Lalle masu almubazzaranci sun tabbata dangin shaixanu; Shaixan kuwa ya zamanto mai yawan kafirce wa Ubangijinsa ne



السورة: Suratu Maryam

الآية : 68

فَوَرَبِّكَ لَنَحۡشُرَنَّهُمۡ وَٱلشَّيَٰطِينَ ثُمَّ لَنُحۡضِرَنَّهُمۡ حَوۡلَ جَهَنَّمَ جِثِيّٗا

To na rantse da Ubangijinka lalle za Mu tashe su tare da shaixanu, sannan za Mu kawo su a gaban Jahannama suna a duddurqushe



السورة: Suratu Maryam

الآية : 83

أَلَمۡ تَرَ أَنَّآ أَرۡسَلۡنَا ٱلشَّيَٰطِينَ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ تَؤُزُّهُمۡ أَزّٗا

Shin ba ka san Mu Muka xora shaixanu a kan kafirai ba suna ingiza su (cikin vata) ingizawa?



السورة: Suratul Anbiya

الآية : 82

وَمِنَ ٱلشَّيَٰطِينِ مَن يَغُوصُونَ لَهُۥ وَيَعۡمَلُونَ عَمَلٗا دُونَ ذَٰلِكَۖ وَكُنَّا لَهُمۡ حَٰفِظِينَ

Akwai kuma wasu aljannu da suke nutso don fito masa (da lu’u-lu’u) suna kuma yin wani aikin ban da wannan (kamar gine-gine); Mun zamanto kuma Masu kula da su))



السورة: Suratul Hajji

الآية : 3

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُجَٰدِلُ فِي ٱللَّهِ بِغَيۡرِ عِلۡمٖ وَيَتَّبِعُ كُلَّ شَيۡطَٰنٖ مَّرِيدٖ

Daga mutane kuma akwai wanda yake jayayya game da Allah ba tare da wani ilimi ba, kuma yake bin kowanne shaixani mai tsaurin kai



السورة: Suratul Hajji

الآية : 4

كُتِبَ عَلَيۡهِ أَنَّهُۥ مَن تَوَلَّاهُ فَأَنَّهُۥ يُضِلُّهُۥ وَيَهۡدِيهِ إِلَىٰ عَذَابِ ٱلسَّعِيرِ

An qaddara masa (wato Shaixan) cewa duk wanda ya rungume shi to haqiqa zai vatar da shi kuma ya ja shi zuwa ga azaba ta (wutar) Sa’ira



السورة: Suratul Mu’uminun

الآية : 97

وَقُل رَّبِّ أَعُوذُ بِكَ مِنۡ هَمَزَٰتِ ٱلشَّيَٰطِينِ

Kuma ka ce: “Ubangijina, ina neman tsarinka daga waswasin shaixanu



السورة: Suratul Mu’uminun

الآية : 98

وَأَعُوذُ بِكَ رَبِّ أَن يَحۡضُرُونِ

“Ina kuma neman tsarinka Ubangijina kar su zo min.”



السورة: Suratus Shu’ara

الآية : 210

وَمَا تَنَزَّلَتۡ بِهِ ٱلشَّيَٰطِينُ

Kuma shaixanu ba su sauko da shi ba



السورة: Suratus Shu’ara

الآية : 221

هَلۡ أُنَبِّئُكُمۡ عَلَىٰ مَن تَنَزَّلُ ٱلشَّيَٰطِينُ

Shin ba Na ba ku labari ba game da wanda shexanu suke saukar masa?



السورة: Suratus Shu’ara

الآية : 222

تَنَزَّلُ عَلَىٰ كُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٖ

Suna sauka ne a kan duk wani maqaryaci mai yawan laifi



السورة: Suratus Shu’ara

الآية : 223

يُلۡقُونَ ٱلسَّمۡعَ وَأَكۡثَرُهُمۡ كَٰذِبُونَ

Suna jefa wa (bokaye) abin da suka sato jinsa, yawancinsu kuwa maqaryata ne



السورة: Suratus Saffat

الآية : 7

وَحِفۡظٗا مِّن كُلِّ شَيۡطَٰنٖ مَّارِدٖ

Da kuma tsaro daga dukkan wani shaixan mai tsaurin kai



السورة: Suratus Saffat

الآية : 8

لَّا يَسَّمَّعُونَ إِلَى ٱلۡمَلَإِ ٱلۡأَعۡلَىٰ وَيُقۡذَفُونَ مِن كُلِّ جَانِبٖ

Ba kuma za su iya jiyowa ba (daga asirin) mala’iku na sama, sai a yi ta jifan su ta kowane vangare



السورة: Suratus Saffat

الآية : 9

دُحُورٗاۖ وَلَهُمۡ عَذَابٞ وَاصِبٌ

Don kora; suna kuma da wata azaba dawwamamma



السورة: Suratus Saffat

الآية : 10

إِلَّا مَنۡ خَطِفَ ٱلۡخَطۡفَةَ فَأَتۡبَعَهُۥ شِهَابٞ ثَاقِبٞ

Sai dai wanda ya yi fautowar jin, to sai wani tauraro mai haske da quna ya biyo shi



السورة: Suratu Sad

الآية : 37

وَٱلشَّيَٰطِينَ كُلَّ بَنَّآءٖ وَغَوَّاصٖ

Da kuma shaixanu masu yin kowane irin gini da kuma masu yin nutso (a ruwa)



السورة: Suratu Sad

الآية : 38

وَءَاخَرِينَ مُقَرَّنِينَ فِي ٱلۡأَصۡفَادِ

Wasu kuma an xaxxaure su cikin maruruwa



السورة: Suratul Mulk

الآية : 5

وَلَقَدۡ زَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنۡيَا بِمَصَٰبِيحَ وَجَعَلۡنَٰهَا رُجُومٗا لِّلشَّيَٰطِينِۖ وَأَعۡتَدۡنَا لَهُمۡ عَذَابَ ٱلسَّعِيرِ

Kuma haqiqa Mun qawata saman duniya da taurari Muka sanya su kuma ababan jifan shaixanu[1]; Muka kuma tanadar musu azabar (wutar) Sa’ira


1- Watau jifar shaixanu masu qoqarin satar ji su qona su.