السورة: Suratul Baqara

الآية : 154

وَلَا تَقُولُواْ لِمَن يُقۡتَلُ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أَمۡوَٰتُۢۚ بَلۡ أَحۡيَآءٞ وَلَٰكِن لَّا تَشۡعُرُونَ

Kada kuma ku ce wa waxanda ake kashewa a kan hanyar Allah su matattu ne. A’a, rayayyu ne, sai dai ku ne ba ku sani ba



السورة: Suratul Baqara

الآية : 234

وَٱلَّذِينَ يُتَوَفَّوۡنَ مِنكُمۡ وَيَذَرُونَ أَزۡوَٰجٗا يَتَرَبَّصۡنَ بِأَنفُسِهِنَّ أَرۡبَعَةَ أَشۡهُرٖ وَعَشۡرٗاۖ فَإِذَا بَلَغۡنَ أَجَلَهُنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ فِيمَا فَعَلۡنَ فِيٓ أَنفُسِهِنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ

Kuma waxanda suke mutuwa daga cikinku, suna kuma barin mata na aure, (su matan) za su yi zaman jira na wata huxu da kwana goma. To idan sun cika wa’adinsu, babu laifi a kanku (waliyyansu) cikin duk abin da suka aikata game da kawunansu ta hanyar da aka saba (a shari’a). Kuma Allah Mai cikakken sani ne game da abin da kuke aikatawa



السورة: Suratul Baqara

الآية : 240

وَٱلَّذِينَ يُتَوَفَّوۡنَ مِنكُمۡ وَيَذَرُونَ أَزۡوَٰجٗا وَصِيَّةٗ لِّأَزۡوَٰجِهِم مَّتَٰعًا إِلَى ٱلۡحَوۡلِ غَيۡرَ إِخۡرَاجٖۚ فَإِنۡ خَرَجۡنَ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ فِي مَا فَعَلۡنَ فِيٓ أَنفُسِهِنَّ مِن مَّعۡرُوفٖۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٞ

Kuma waxanda suke rasuwa daga cikinku suke barin matan aure, (to za su yi) wasiyya ga matansu cewa, a jiyar da su daxi har zuwa shekara, ba tare da an fitar da su ba; to idan su suka fita da kansu, to babu laifi a kanku dangane da abin da suka aikata wa kansu na abin da yake sananne a shari’a. Kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima[1]


1- Wasu malamai suna ganin wannan aya an shafe ta da aya ta 234. Wasu kuma suna ganin umarni ne ga mazaje su yi wasiyya ga magadansu a kan su qale matansu su zauna a gidajensu tsawon shekara xaya, Wannan kuwa ya kasance ne kafin Allah ya shar’anta rabon gado, a inda ya ambaci kason mace daga dukiyar mijinta.


السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 107

وَأَمَّا ٱلَّذِينَ ٱبۡيَضَّتۡ وُجُوهُهُمۡ فَفِي رَحۡمَةِ ٱللَّهِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Amma waxanda fuskokinsu suka yi fari kuwa, to suna cikin rahamar Allah, suna masu dawwama a cikinta



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 108

تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱللَّهِ نَتۡلُوهَا عَلَيۡكَ بِٱلۡحَقِّۗ وَمَا ٱللَّهُ يُرِيدُ ظُلۡمٗا لِّلۡعَٰلَمِينَ

Waxannan ayoyin Allah ne Muke karanta maka su da gaskiya. Kuma Allah ba Ya nufin zalunci ga talikai



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 145

وَمَا كَانَ لِنَفۡسٍ أَن تَمُوتَ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِ كِتَٰبٗا مُّؤَجَّلٗاۗ وَمَن يُرِدۡ ثَوَابَ ٱلدُّنۡيَا نُؤۡتِهِۦ مِنۡهَا وَمَن يُرِدۡ ثَوَابَ ٱلۡأٓخِرَةِ نُؤۡتِهِۦ مِنۡهَاۚ وَسَنَجۡزِي ٱلشَّـٰكِرِينَ

Kuma babu wani rai da zai mutu sai da izinin Allah, rubutaccen abu ne qayyadajje. Kuma duk wanda yake nufin sakamakon duniya, za Mu ba shi daga gare ta, wanda kuma yake nufin sakamakon lahira, to za Mu ba shi daga gare ta. Kuma da sannu za Mu saka ma masu godiya



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 157

وَلَئِن قُتِلۡتُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أَوۡ مُتُّمۡ لَمَغۡفِرَةٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَرَحۡمَةٌ خَيۡرٞ مِّمَّا يَجۡمَعُونَ

Kuma lalle idan ma har an kashe ku a hanyar Allah ko kuma kuka mutu, to kuna da gafara ta musamman a wajen Allah da kuma rahama, wanda shi ne mafi alheri fiye da abin da suke tarawa



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 158

وَلَئِن مُّتُّمۡ أَوۡ قُتِلۡتُمۡ لَإِلَى ٱللَّهِ تُحۡشَرُونَ

Kuma lalle in kuka mutu ko aka kashe ku, lalle zuwa ga Allah dai za a tattara ku



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 169

وَلَا تَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ قُتِلُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أَمۡوَٰتَۢاۚ بَلۡ أَحۡيَآءٌ عِندَ رَبِّهِمۡ يُرۡزَقُونَ

Kuma kada ka yi tsammanin waxanda aka kashe su a wajen yaxa kalmar Allah matattu ne. A’a, rayayyu ne a wajen Ubangijinsu, ana arzurta su



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 185

كُلُّ نَفۡسٖ ذَآئِقَةُ ٱلۡمَوۡتِۗ وَإِنَّمَا تُوَفَّوۡنَ أُجُورَكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۖ فَمَن زُحۡزِحَ عَنِ ٱلنَّارِ وَأُدۡخِلَ ٱلۡجَنَّةَ فَقَدۡ فَازَۗ وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَآ إِلَّا مَتَٰعُ ٱلۡغُرُورِ

Kowane rai zai xanxani mutuwa. Kuma a ranar alqiyama ne za a cika muku ladan ayyukanku; to duk wanda aka nisanta shi daga wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to haqiqa ya rabauta. Kuma rayuwar duniya ba komai ba ce face jin daxi mai ruxarwa



السورة: Suratun Nisa’i

الآية : 100

۞وَمَن يُهَاجِرۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ يَجِدۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُرَٰغَمٗا كَثِيرٗا وَسَعَةٗۚ وَمَن يَخۡرُجۡ مِنۢ بَيۡتِهِۦ مُهَاجِرًا إِلَى ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ ثُمَّ يُدۡرِكۡهُ ٱلۡمَوۡتُ فَقَدۡ وَقَعَ أَجۡرُهُۥ عَلَى ٱللَّهِۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

Kuma duk wanda ya yi hijira saboda Allah, zai samu wuraren hijira masu yawa da yalwa a bayan qasa. Kuma duk wanda ya fita daga gidansa, yana mai hijira zuwa ga Allah da Manzonsa, sannan mutuwa ta riske shi, to haqiqa ladansa ya tabbata a wajen Allah. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin qai



السورة: Suratul Ma’ida

الآية : 106

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ شَهَٰدَةُ بَيۡنِكُمۡ إِذَا حَضَرَ أَحَدَكُمُ ٱلۡمَوۡتُ حِينَ ٱلۡوَصِيَّةِ ٱثۡنَانِ ذَوَا عَدۡلٖ مِّنكُمۡ أَوۡ ءَاخَرَانِ مِنۡ غَيۡرِكُمۡ إِنۡ أَنتُمۡ ضَرَبۡتُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَأَصَٰبَتۡكُم مُّصِيبَةُ ٱلۡمَوۡتِۚ تَحۡبِسُونَهُمَا مِنۢ بَعۡدِ ٱلصَّلَوٰةِ فَيُقۡسِمَانِ بِٱللَّهِ إِنِ ٱرۡتَبۡتُمۡ لَا نَشۡتَرِي بِهِۦ ثَمَنٗا وَلَوۡ كَانَ ذَا قُرۡبَىٰ وَلَا نَكۡتُمُ شَهَٰدَةَ ٱللَّهِ إِنَّآ إِذٗا لَّمِنَ ٱلۡأٓثِمِينَ

Ya ku waxanda suka yi imani, shaidar da take tsakaninku idan alamun mutuwa suka zo wa xaya daga cikinku, yayin da ya so ya yi wasiyya, shi ne a samu mutum biyu masu adalci daga cikinku ko kuma waxansu biyu daga wasunku (kafirai), yayin da kuka yi tafiya a bayan qasa, sai musibar mutuwa ta same ku. Za ku tsayar da su (shaidun) biyun ne bayan an kammala salla, sai su rantse da Allah- idan har kun yi shakka game da su-: “Wallahi, ba za mu musanya shi da wani farashi ba, ko da kuwa ya zamo ma’abocin kusanci ne, kuma ba za mu voye shaidar Allah ba, lalle kuwa idan har muka yi haka, tabbas muna cikin masu laifi.”



السورة: Suratul An’am

الآية : 93

وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ قَالَ أُوحِيَ إِلَيَّ وَلَمۡ يُوحَ إِلَيۡهِ شَيۡءٞ وَمَن قَالَ سَأُنزِلُ مِثۡلَ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُۗ وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذِ ٱلظَّـٰلِمُونَ فِي غَمَرَٰتِ ٱلۡمَوۡتِ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ بَاسِطُوٓاْ أَيۡدِيهِمۡ أَخۡرِجُوٓاْ أَنفُسَكُمُۖ ٱلۡيَوۡمَ تُجۡزَوۡنَ عَذَابَ ٱلۡهُونِ بِمَا كُنتُمۡ تَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ غَيۡرَ ٱلۡحَقِّ وَكُنتُمۡ عَنۡ ءَايَٰتِهِۦ تَسۡتَكۡبِرُونَ

Kuma wane ne ya fi zalunci kamar wanda ya qagi qarya ya jingina wa Allah, ko kuma ya ce: “An yiwo mini wahayi,” alhalin kuma ba a yi masa wahayin komai ba, da kuma wanda ya ce: “Zan saukar da irin abin da Allah Ya saukar?” Kuma da za ka ga lokacin da kafirai suke cikin magagin mutuwa, mala’iku kuma suna miqa hannayensu suna cewa: “Ku fito da rayukanku (da kanku), a yau ne za a saka muku da azabar wulaqanci, saboda irin abin da kuke faxa game da Allah wanda ba gaskiya ba, kuma kun kasance kuna girman kai game da ayoyinsa.”



السورة: Suratul Anfal

الآية : 50

وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذۡ يَتَوَفَّى ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَضۡرِبُونَ وُجُوهَهُمۡ وَأَدۡبَٰرَهُمۡ وَذُوقُواْ عَذَابَ ٱلۡحَرِيقِ

Kuma da za ka ga lokacin da mala’iku suke xaukan ran waxanda suka kafirta, suna dukan fuskokinsu da kuma bayansu, suna kuma (cewa da su): “Ku xanxani azabar quna.”



السورة: Suratun Nahl

الآية : 28

ٱلَّذِينَ تَتَوَفَّىٰهُمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ ظَالِمِيٓ أَنفُسِهِمۡۖ فَأَلۡقَوُاْ ٱلسَّلَمَ مَا كُنَّا نَعۡمَلُ مِن سُوٓءِۭۚ بَلَىٰٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمُۢ بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Waxanda mala’iku suke karvar ransu suna masu zaluntar kawunansu; sai suka ba da kai (suna cewa,): “Ba mu kasance muna yin wani mummunan aiki ba.” A’a, ba haka ba ne, lalle Allah Masanin abin da kuka zamanto kuna aikatawa ne



السورة: Suratun Nahl

الآية : 32

ٱلَّذِينَ تَتَوَفَّىٰهُمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ طَيِّبِينَ يَقُولُونَ سَلَٰمٌ عَلَيۡكُمُ ٱدۡخُلُواْ ٱلۡجَنَّةَ بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Waxanda mala’iku suke xaukar ransu suna tsarkaka, suna cewa: “Aminci ya tabbata a gare ku, ku shiga Aljanna saboda abin da kuka zamanto kuna aikatawa (a duniya)



السورة: Suratul Hajji

الآية : 5

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِن كُنتُمۡ فِي رَيۡبٖ مِّنَ ٱلۡبَعۡثِ فَإِنَّا خَلَقۡنَٰكُم مِّن تُرَابٖ ثُمَّ مِن نُّطۡفَةٖ ثُمَّ مِنۡ عَلَقَةٖ ثُمَّ مِن مُّضۡغَةٖ مُّخَلَّقَةٖ وَغَيۡرِ مُخَلَّقَةٖ لِّنُبَيِّنَ لَكُمۡۚ وَنُقِرُّ فِي ٱلۡأَرۡحَامِ مَا نَشَآءُ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى ثُمَّ نُخۡرِجُكُمۡ طِفۡلٗا ثُمَّ لِتَبۡلُغُوٓاْ أَشُدَّكُمۡۖ وَمِنكُم مَّن يُتَوَفَّىٰ وَمِنكُم مَّن يُرَدُّ إِلَىٰٓ أَرۡذَلِ ٱلۡعُمُرِ لِكَيۡلَا يَعۡلَمَ مِنۢ بَعۡدِ عِلۡمٖ شَيۡـٔٗاۚ وَتَرَى ٱلۡأَرۡضَ هَامِدَةٗ فَإِذَآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡهَا ٱلۡمَآءَ ٱهۡتَزَّتۡ وَرَبَتۡ وَأَنۢبَتَتۡ مِن كُلِّ زَوۡجِۭ بَهِيجٖ

Ya ku mutane, idan kun zamanto cikin kokwanton tashi (bayan mutuwa), to lalle Mu Muka halicce ku daga qasa, sannan daga maniyyi, sannan daga gudan jini, sannan daga tsoka, mai cikakkiyar halitta da kuma wadda ba cikakkiya ba[1], don Mu bayyana muku (Ikonmu). Kuma Muna tabbatar da abin da Muka ga dama a cikin mahaifa har zuwa wani lokaci qayyadajje, sannan kuma Mu fito da ku kuna jarirai, sannan kuma don ku kai cikar qarfinku; daga cikinku akwai wanda za a karvi ransa, akwai kuma wanda za a bari har zuwa mafi qasqantar rayuwa don ya kai ga halin da ba zai san komai ba bayan kuwa da can ya sani. Za ka kuma ga qasa a qeqashe, sannan idan Muka saukar mata da ruwa sai ta girgiza ta kumbura kuma ta fitar da kowanne irin tsiro mai qayatarwa


1- Watau tsokar ta zama wata halitta wadda ba cikakken mutum ba, daga bisani a yi varin ta.


السورة: Suratul Mu’uminun

الآية : 99

حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَ أَحَدَهُمُ ٱلۡمَوۡتُ قَالَ رَبِّ ٱرۡجِعُونِ

Har sai idan da mutuwa ta zo wa xayansu zai ce: “Ubangijina, Ku mai da ni (duniya) mana



السورة: Suratu Luqman

الآية : 34

إِنَّ ٱللَّهَ عِندَهُۥ عِلۡمُ ٱلسَّاعَةِ وَيُنَزِّلُ ٱلۡغَيۡثَ وَيَعۡلَمُ مَا فِي ٱلۡأَرۡحَامِۖ وَمَا تَدۡرِي نَفۡسٞ مَّاذَا تَكۡسِبُ غَدٗاۖ وَمَا تَدۡرِي نَفۡسُۢ بِأَيِّ أَرۡضٖ تَمُوتُۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرُۢ

Lalle Allah a wurinsa ne (kaxai) sanin lokacin tashin alqiyama yake, kuma (Shi) Yake saukar da ruwa, (Shi) kuma Yake sane da abin da yake cikin mahaifa[1]; ba kuwa wani rai da yake sane da abin da zai aikata gobe, ba kuma wani rai da yake sane da qasar da zai mutu. Lalle Allah Shi ne Masani, Mai cikakken ilimi


1- Watau ya san komai na halittarsa, tun daga lokacin shigarsa mahaifa har zuwa makomarsa ta qarshe.


السورة: Suratus Sajda

الآية : 11

۞قُلۡ يَتَوَفَّىٰكُم مَّلَكُ ٱلۡمَوۡتِ ٱلَّذِي وُكِّلَ بِكُمۡ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُمۡ تُرۡجَعُونَ

Ka ce (da su): “Mala’ikan mutuwa ne wanda aka wakilta muku zai karvi ranku sannan kuma ga Ubangijinku za a komar da ku



السورة: Suratuz Zumar

الآية : 30

إِنَّكَ مَيِّتٞ وَإِنَّهُم مَّيِّتُونَ

Lalle kai mai mutuwa ne, su ma kuma lalle masu mutuwa ne



السورة: Suratuz Zumar

الآية : 42

ٱللَّهُ يَتَوَفَّى ٱلۡأَنفُسَ حِينَ مَوۡتِهَا وَٱلَّتِي لَمۡ تَمُتۡ فِي مَنَامِهَاۖ فَيُمۡسِكُ ٱلَّتِي قَضَىٰ عَلَيۡهَا ٱلۡمَوۡتَ وَيُرۡسِلُ ٱلۡأُخۡرَىٰٓ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمًّىۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ

Allah Yana karvar rayuka lokacin mutuwarsu, da waxanda kuma ba su mutu ba a lokacin baccinsu; sai Ya riqe waxanda Ya qaddara wa mutuwa, Ya kuma saki sauran har zuwa wani lokaci qayyadadde. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutane masu tunani



السورة: Suratu Ghafir

الآية : 67

هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَكُم مِّن تُرَابٖ ثُمَّ مِن نُّطۡفَةٖ ثُمَّ مِنۡ عَلَقَةٖ ثُمَّ يُخۡرِجُكُمۡ طِفۡلٗا ثُمَّ لِتَبۡلُغُوٓاْ أَشُدَّكُمۡ ثُمَّ لِتَكُونُواْ شُيُوخٗاۚ وَمِنكُم مَّن يُتَوَفَّىٰ مِن قَبۡلُۖ وَلِتَبۡلُغُوٓاْ أَجَلٗا مُّسَمّٗى وَلَعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ

“Shi ne wanda Ya halicce ku daga qasa, sannan daga xigon maniyyi, sannan daga gudan jini, daga nan Ya fito da ku kuna jarirai, sannan don ku kai qarfinku, sannan kuma ku zama tsofaffi. Daga cikinku kuma akwai wanda ake karvar ransa kafin wannan; don kuma ku isa zuwa wani lokaci qayyadajje[1], don kuma ku hankalta


1- Wanda ba za su rage ba ba kuma za su qara ba, watau lokacin mutuwarsu.


السورة: Suratu Ghafir

الآية : 68

هُوَ ٱلَّذِي يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ فَإِذَا قَضَىٰٓ أَمۡرٗا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ

“Shi ne wanda Yake rayawa Yake kuma kashewa; to idan zai hukunta wani al’amari sai kawai Ya ce da shi: ‘Kasance’, sai ya kasance.”



السورة: Suratud Dukhan

الآية : 56

لَا يَذُوقُونَ فِيهَا ٱلۡمَوۡتَ إِلَّا ٱلۡمَوۡتَةَ ٱلۡأُولَىٰۖ وَوَقَىٰهُمۡ عَذَابَ ٱلۡجَحِيمِ

Ba za su xanxani wata mutuwa a cikinta ba sai dai mutuwar farko; Ya kuma tserar da su daga azabar wutar Jahima



السورة: Suratu Muhammad

الآية : 27

فَكَيۡفَ إِذَا تَوَفَّتۡهُمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَضۡرِبُونَ وُجُوهَهُمۡ وَأَدۡبَٰرَهُمۡ

To yaya za su zama lokacin da mala’iku za su karvi rayukansu suna dukan fuskokinsu da bayansu?



السورة: Suratu Qaf 

الآية : 19

وَجَآءَتۡ سَكۡرَةُ ٱلۡمَوۡتِ بِٱلۡحَقِّۖ ذَٰلِكَ مَا كُنتَ مِنۡهُ تَحِيدُ

Kuma magagin mutuwa ya zo da gaskiya; wannan ne abin da ka kasance kana kakkauce wa



السورة: Suratul Waqi’a

الآية : 60

نَحۡنُ قَدَّرۡنَا بَيۡنَكُمُ ٱلۡمَوۡتَ وَمَا نَحۡنُ بِمَسۡبُوقِينَ

Mu ne Muke qaddara mutuwa a tsakaninku, kuma Mu ba Masu gajiyawa ba ne



السورة: Suratul Waqi’a

الآية : 83

فَلَوۡلَآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلۡحُلۡقُومَ

Me ya hana idan (rai) ya isa maqogwaro



السورة: Suratul Waqi’a

الآية : 84

وَأَنتُمۡ حِينَئِذٖ تَنظُرُونَ

Ku kuma a lokacin kuna kallo