لَّقَدۡ أَحۡصَىٰهُمۡ وَعَدَّهُمۡ عَدّٗا
Lalle Ya kiyaye da su Ya kuma qididdige su sosai
وَكُلُّهُمۡ ءَاتِيهِ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فَرۡدًا
Kuma dukkansu kowa zai zo masa a ranar alqiyama shi kaxai
يَوۡمَ يُنفَخُ فِي ٱلصُّورِۚ وَنَحۡشُرُ ٱلۡمُجۡرِمِينَ يَوۡمَئِذٖ زُرۡقٗا
(Ita ce) ranar da za a busa qaho. Kuma Mu tayar da kafirai a wannan ranar idanuwansu jawur[1]
1- Watau saboda tsananin tsoro da fargaba.
يَتَخَٰفَتُونَ بَيۡنَهُمۡ إِن لَّبِثۡتُمۡ إِلَّا عَشۡرٗا
Suna raxa a tsakaninsu (suna cewa): “Ba ku zauna (a qaburburanku) ba face (kwana) goma.”
نَّحۡنُ أَعۡلَمُ بِمَا يَقُولُونَ إِذۡ يَقُولُ أَمۡثَلُهُمۡ طَرِيقَةً إِن لَّبِثۡتُمۡ إِلَّا يَوۡمٗا
Mu Muka fi sanin abin da suke faxi lokacin da wanda ya fi tunani daga cikinsu yake cewa: “Ba ku zauna ba face rana guda.”
وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡجِبَالِ فَقُلۡ يَنسِفُهَا رَبِّي نَسۡفٗا
Suna kuma tambayar ka game da duwatsu, to ka ce (da su): “Ubangijina zai niqe su tilis
فَيَذَرُهَا قَاعٗا صَفۡصَفٗا
“Sannan Ya bar ta (wato qasar) fili fetal
لَّا تَرَىٰ فِيهَا عِوَجٗا وَلَآ أَمۡتٗا
“Ba za ka ga wani kwari ko tudu a kanta ba.”
يَوۡمَئِذٖ يَتَّبِعُونَ ٱلدَّاعِيَ لَا عِوَجَ لَهُۥۖ وَخَشَعَتِ ٱلۡأَصۡوَاتُ لِلرَّحۡمَٰنِ فَلَا تَسۡمَعُ إِلَّا هَمۡسٗا
A wannan rana ne za su bi mai kira (zuwa matattara), ba mai bauxe masa; kuma (duk) muryoyi su yi qasa-qasa saboda (girman Allah) Mai rahama, sannan ba za ka ji (komai) ba sai raxa
يَوۡمَئِذٖ لَّا تَنفَعُ ٱلشَّفَٰعَةُ إِلَّا مَنۡ أَذِنَ لَهُ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَرَضِيَ لَهُۥ قَوۡلٗا
A wannan ranar ceto ba ya amfani sai ga wanda (Allah) Mai rahama Ya yi wa izini, kuma Ya yarda da maganarsa
۞وَعَنَتِ ٱلۡوُجُوهُ لِلۡحَيِّ ٱلۡقَيُّومِۖ وَقَدۡ خَابَ مَنۡ حَمَلَ ظُلۡمٗا
Kuma dukkanin fuskoki suka qasqanta ga (Allah) Rayayye, Tsayayye (da Zatinsa). Haqiqa kuma duk wanda ya yo dakon zalunci ya tave
وَمَن يَعۡمَلۡ مِنَ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَا يَخَافُ ظُلۡمٗا وَلَا هَضۡمٗا
Duk kuma wanda yake yin aiki na gari alhali kuwa shi mumini ne, to ba zai ji tsoron zalunci ba ko kuma qwauro
وَنَضَعُ ٱلۡمَوَٰزِينَ ٱلۡقِسۡطَ لِيَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ فَلَا تُظۡلَمُ نَفۡسٞ شَيۡـٔٗاۖ وَإِن كَانَ مِثۡقَالَ حَبَّةٖ مِّنۡ خَرۡدَلٍ أَتَيۡنَا بِهَاۗ وَكَفَىٰ بِنَا حَٰسِبِينَ
Za Mu kuma sanya ma’aunai na adalci a ranar alqiyama, sannan ba za a zalunci kowanne rai da komai ba, ko da ya zama gwargwadon qwayar komayya ne, za Mu zo da shi. Kuma Mun isa Masu hisabi!
يَوۡمَ نَطۡوِي ٱلسَّمَآءَ كَطَيِّ ٱلسِّجِلِّ لِلۡكُتُبِۚ كَمَا بَدَأۡنَآ أَوَّلَ خَلۡقٖ نُّعِيدُهُۥۚ وَعۡدًا عَلَيۡنَآۚ إِنَّا كُنَّا فَٰعِلِينَ
(Ita ce) ranar da za Mu naxe sama kamar naxin marubuci ga takardu. Kamar yadda Muka qagi halitta da farko (haka) za Mu mai da ita. Wannan alqawari ne da Muka xauka. Lallai Mun kasance Masu aikata (haka)
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمۡۚ إِنَّ زَلۡزَلَةَ ٱلسَّاعَةِ شَيۡءٌ عَظِيمٞ
Ya ku mutane, ku kiyaye dokokin Ubangijinku. Lalle girgizar (ranar) alqiyama abu ne mai girma
يَوۡمَ تَرَوۡنَهَا تَذۡهَلُ كُلُّ مُرۡضِعَةٍ عَمَّآ أَرۡضَعَتۡ وَتَضَعُ كُلُّ ذَاتِ حَمۡلٍ حَمۡلَهَا وَتَرَى ٱلنَّاسَ سُكَٰرَىٰ وَمَا هُم بِسُكَٰرَىٰ وَلَٰكِنَّ عَذَابَ ٱللَّهِ شَدِيدٞ
Ranar da za ku gan ta, (don tsananin firgita) kowacce mai shayarwa za ta manta da abin da ta shayar, kuma kowacce mai ciki ta zubar da cikinta, ka ga kuma mutane suna tangaxi, alhali kuwa ba bugaggu ba ne, sai dai azabar Allah ce mai tsanani
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَٱلَّذِينَ هَادُواْ وَٱلصَّـٰبِـِٔينَ وَٱلنَّصَٰرَىٰ وَٱلۡمَجُوسَ وَٱلَّذِينَ أَشۡرَكُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ يَفۡصِلُ بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٌ
Lalle waxanda suka yi imani da waxanda suka zama Yahudawa da Sabi’awa da waxanda suka zama Majusawa da kuma waxanda suka yi shirka, lalle Allah zai yi hukunci a tsakaninsu ranar alqiyama. Lalle Allah Mai ganin kowane abu ne
وَلَا يَزَالُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فِي مِرۡيَةٖ مِّنۡهُ حَتَّىٰ تَأۡتِيَهُمُ ٱلسَّاعَةُ بَغۡتَةً أَوۡ يَأۡتِيَهُمۡ عَذَابُ يَوۡمٍ عَقِيمٍ
Waxanda kuwa suka kafirce ba za su daina kokwanton sa ba (watau Alqur’ani) har sai alqiyama ta zo musu ba zato ba tsammani, ko kuma azabar rana bakarara[1] ta zo musu
1- Watau ranar da kafirai ba za su samu wata rahama ko wani alheri ba.
ٱلۡمُلۡكُ يَوۡمَئِذٖ لِّلَّهِ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡۚ فَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ فِي جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ
Mulki a wannan ranar na Allah ne, zai yi hukunci a tsakaninsu. To waxanda suka yi imani suka kuma yi kyawawan ayyuka, suna cikin gidajen Aljanna na ni’ima
ٱللَّهُ يَحۡكُمُ بَيۡنَكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فِيمَا كُنتُمۡ فِيهِ تَخۡتَلِفُونَ
Allah zai yi hukunci a tsakaninku ranar alqiyama game da abin da kuka kasance kuna sassavawa a kansa
ثُمَّ إِنَّكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ تُبۡعَثُونَ
Sannan kuma haqiqa za a tashe ku ranar Alqiyama
يَوۡمَ تَشۡهَدُ عَلَيۡهِمۡ أَلۡسِنَتُهُمۡ وَأَيۡدِيهِمۡ وَأَرۡجُلُهُم بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
A ranar da harsunansu da hannayensu da kuma qafafunsu za su ba da shaida a kansu game da abin da suka kasance suna aikatawa
يَوۡمَئِذٖ يُوَفِّيهِمُ ٱللَّهُ دِينَهُمُ ٱلۡحَقَّ وَيَعۡلَمُونَ أَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡحَقُّ ٱلۡمُبِينُ
A wannan ranar Allah zai ba su cikakken sakamakonsu na gaskiya kuma za su san cewa lalle Allah Shi ne gaskiya bayyananniya
يَوۡمَ يَرَوۡنَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ لَا بُشۡرَىٰ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُجۡرِمِينَ وَيَقُولُونَ حِجۡرٗا مَّحۡجُورٗا
Ranar da za su ga mala’iku[1] a wannan ranar babu wani farin ciki ga masu laifi, za kuma su riqa cewa: “(Albishir daga Allah) haramun ne abin haramtawa ne (a gare su)”
1- Watau ranar mutuwarsu ko a cikin qaburburansu da ranar da za a kora su domin yi musu hisabi.
وَقَدِمۡنَآ إِلَىٰ مَا عَمِلُواْ مِنۡ عَمَلٖ فَجَعَلۡنَٰهُ هَبَآءٗ مَّنثُورًا
Muka kuma gabato zuwa ga duk wani aiki da suka yi, sai Muka mai da shi qura abar xaixaitawa
أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِ يَوۡمَئِذٍ خَيۡرٞ مُّسۡتَقَرّٗا وَأَحۡسَنُ مَقِيلٗا
‘Yan Aljanna a wannan ranar su suka fi kyakkyawan mazauni kuma suka fi kyawon wurin barcin qailula[1]
1- Domin za a gama hisabi gabanin lokacin azahar, har ‘yan Aljanna za su shige ta su riski lokacin qailula a cikinta.
وَيَوۡمَ تَشَقَّقُ ٱلسَّمَآءُ بِٱلۡغَمَٰمِ وَنُزِّلَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ تَنزِيلًا
Kuma (ka tuna) ranar da sama za ta kekkece da girgije, kuma a saukar da mala’iku gungu-gungu
ٱلۡمُلۡكُ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡحَقُّ لِلرَّحۡمَٰنِۚ وَكَانَ يَوۡمًا عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ عَسِيرٗا
Mulki tabbatacce a wannan ranar na (Allah) Mai rahama ne. Kuma ta kasance rana ce mawuyaciya ga kafurai
وَيَوۡمَ يَعَضُّ ٱلظَّالِمُ عَلَىٰ يَدَيۡهِ يَقُولُ يَٰلَيۡتَنِي ٱتَّخَذۡتُ مَعَ ٱلرَّسُولِ سَبِيلٗا
(Ka tuna) kuma ranar da azzalumi zai riqa cizon yatsunsa yana cewa: “Ina ma na bi hanya tare da Manzo!
يَٰوَيۡلَتَىٰ لَيۡتَنِي لَمۡ أَتَّخِذۡ فُلَانًا خَلِيلٗا
“Kaicona ina ma da ban riqi wane aboki ba!