وَلَمَّا جَآءَ عِيسَىٰ بِٱلۡبَيِّنَٰتِ قَالَ قَدۡ جِئۡتُكُم بِٱلۡحِكۡمَةِ وَلِأُبَيِّنَ لَكُم بَعۡضَ ٱلَّذِي تَخۡتَلِفُونَ فِيهِۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
Lokacin da kuma Isa ya zo da hujjoji bayyanannu ya ce: “Haqiqa na zo muku da hikima, don kuma in bayyana muku sashin da kuke sassavawa cikinsa; to ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku bi ni
إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ رَبِّي وَرَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُوهُۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ
“Lalle Allah Shi ne Ubangijina kuma Ubangijinku, sai ku bauta masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya.”
ثُمَّ قَفَّيۡنَا عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِم بِرُسُلِنَا وَقَفَّيۡنَا بِعِيسَى ٱبۡنِ مَرۡيَمَ وَءَاتَيۡنَٰهُ ٱلۡإِنجِيلَۖ وَجَعَلۡنَا فِي قُلُوبِ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُ رَأۡفَةٗ وَرَحۡمَةٗۚ وَرَهۡبَانِيَّةً ٱبۡتَدَعُوهَا مَا كَتَبۡنَٰهَا عَلَيۡهِمۡ إِلَّا ٱبۡتِغَآءَ رِضۡوَٰنِ ٱللَّهِ فَمَا رَعَوۡهَا حَقَّ رِعَايَتِهَاۖ فَـَٔاتَيۡنَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنۡهُمۡ أَجۡرَهُمۡۖ وَكَثِيرٞ مِّنۡهُمۡ فَٰسِقُونَ
Sannan a bayansu Muka biyar da manzanninmu, Muka kuma biyar da Isa xan Maryamu Muka kuma ba shi Linjila, kuma Muka sanya jin qai da rahama a cikin zukatan waxanda suka bi shi. Rahbaniyanci[1] kuma su ne suka qago shi, ba Mu wajabta musu shi ba, sai dai (Mun wajabta musu) neman yardar Allah, amma ba su kiyaye shi ba kamar yadda ya kamata; sai Muka bai wa waxanda suka yi imani daga cikinsu ladansu; da yawa kuwa fasiqai ne
1- Bidi’ar Rahbaniyanci ita ce, qaurace wa aure da barin cin daxaxan abubuwa na halal da haramta wa kai wasu abubuwa da Allah ya halatta.
وَإِذۡ قَالَ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ يَٰبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ إِنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيۡكُم مُّصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيَّ مِنَ ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَمُبَشِّرَۢا بِرَسُولٖ يَأۡتِي مِنۢ بَعۡدِي ٱسۡمُهُۥٓ أَحۡمَدُۖ فَلَمَّا جَآءَهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ قَالُواْ هَٰذَا سِحۡرٞ مُّبِينٞ
Kuma (ka tuna) lokacin da Isa xan Maryamu ya ce: “Ya ku ‘ya’yan Isra’ila, lalle ni Manzon Allah ne zuwa gare ku, mai gaskata abin da yake gabanina na Attaura, kuma mai albishir da wani manzo da zai zo bayana, sunansa Ahmadu[1].” To lokacin da ya zo musu da (ayoyi) bayyanannu sai suka ce: “Wannan sihiri ne mabayyani.”
1- Ahmad, xaya ne daga cikin sunayen Annabi Muhammad ().
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُونُوٓاْ أَنصَارَ ٱللَّهِ كَمَا قَالَ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ لِلۡحَوَارِيِّـۧنَ مَنۡ أَنصَارِيٓ إِلَى ٱللَّهِۖ قَالَ ٱلۡحَوَارِيُّونَ نَحۡنُ أَنصَارُ ٱللَّهِۖ فَـَٔامَنَت طَّآئِفَةٞ مِّنۢ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ وَكَفَرَت طَّآئِفَةٞۖ فَأَيَّدۡنَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ عَلَىٰ عَدُوِّهِمۡ فَأَصۡبَحُواْ ظَٰهِرِينَ
Ya ku waxanda suka yi imani, ku zama masu taimaka wa (addinin) Allah, kamar yadda Isa xan Maryamu ya ce da Hawariyawa[1]: “Su wane ne masu taimaka mini zuwa ga Allah?” Hawariyawan suka ce: “Mu ne masu taimaka wa Allah.” Sai wata qungiya daga Bani Isra’ila suka yi imani, wata qungiya kuma ta kafirta, sai Muka qarfafa waxanda suka yi imani a kan maqiyansu, sai suka wayi gari suna masu cin nasara
1- Su ne almajiransa da suka yi imani da shi.