السورة: Suratu Luqman

الآية : 13

وَإِذۡ قَالَ لُقۡمَٰنُ لِٱبۡنِهِۦ وَهُوَ يَعِظُهُۥ يَٰبُنَيَّ لَا تُشۡرِكۡ بِٱللَّهِۖ إِنَّ ٱلشِّرۡكَ لَظُلۡمٌ عَظِيمٞ

Kuma (ka tuna) lokacin da Luqumanu ya ce da xansa a yayin da yake yi masa wa’azi: “Ya kai xanxana, kada ka yi shirka da Allah; lalle ita shirka zalunci ne mai girma



السورة: Suratu Luqman

الآية : 15

وَإِن جَٰهَدَاكَ عَلَىٰٓ أَن تُشۡرِكَ بِي مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٞ فَلَا تُطِعۡهُمَاۖ وَصَاحِبۡهُمَا فِي ٱلدُّنۡيَا مَعۡرُوفٗاۖ وَٱتَّبِعۡ سَبِيلَ مَنۡ أَنَابَ إِلَيَّۚ ثُمَّ إِلَيَّ مَرۡجِعُكُمۡ فَأُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Idan kuma suka matsa maka kan ka yi tarayya da Ni game da abin da ba ka da wani sani a kansa, to kada ka bi su; kuma ka yi zaman duniya da su ta kyakkyawar hanya; ka kuma bi hanyar wanda ya mayar da al’amarinsa gare Ni. Sannan kuma zuwa gare Ni ne kawai makomarku, sai in ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa



السورة: Suratu Saba’i

الآية : 40

وَيَوۡمَ يَحۡشُرُهُمۡ جَمِيعٗا ثُمَّ يَقُولُ لِلۡمَلَـٰٓئِكَةِ أَهَـٰٓؤُلَآءِ إِيَّاكُمۡ كَانُواْ يَعۡبُدُونَ

Kuma (ka tuna) ranar da zai tattaro su gaba xaya sannan Ya ce da mala’iku: “Ashe yanzu ku ne waxannan suka kasance suna bauta wa?”



السورة: Suratu Saba’i

الآية : 41

قَالُواْ سُبۡحَٰنَكَ أَنتَ وَلِيُّنَا مِن دُونِهِمۖ بَلۡ كَانُواْ يَعۡبُدُونَ ٱلۡجِنَّۖ أَكۡثَرُهُم بِهِم مُّؤۡمِنُونَ

Suka ce: “Tsarki ya tabbata a gare Ka, Kai ne Majivincinmu ba su ba.” Ba haka ba ne, sun kasance suna bauta wa aljannu ne; mafiya yawansu masu yin imani da su ne



السورة: Suratu Faxir

الآية : 40

قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ شُرَكَآءَكُمُ ٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَرُونِي مَاذَا خَلَقُواْ مِنَ ٱلۡأَرۡضِ أَمۡ لَهُمۡ شِرۡكٞ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ أَمۡ ءَاتَيۡنَٰهُمۡ كِتَٰبٗا فَهُمۡ عَلَىٰ بَيِّنَتٖ مِّنۡهُۚ بَلۡ إِن يَعِدُ ٱلظَّـٰلِمُونَ بَعۡضُهُم بَعۡضًا إِلَّا غُرُورًا

Ka ce: “Ku ba ni labarin abokan tarayyar naku da kuke bauta wa ba Allah ba, ku nuna min abin da suka halitta daga qasa, ko kuma suna da wata tarayya ne a cikin (halittar) sammai, ko kuma Mun ba su wani littafi ne, saboda haka suke da wata hujja daga wajensa?” Ba haka ba ne, ba dai abin da azzalumai suke wa juna alqawari da shi in ban da ruxi



السورة: Suratu Yasin

الآية : 23

ءَأَتَّخِذُ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةً إِن يُرِدۡنِ ٱلرَّحۡمَٰنُ بِضُرّٖ لَّا تُغۡنِ عَنِّي شَفَٰعَتُهُمۡ شَيۡـٔٗا وَلَا يُنقِذُونِ

“Yanzu na riqi wasu ababen bauta ba Shi ba, alhali kuwa idan (Allah) Mai rahama Ya nufe ni da wata cuta, cetonsu ba zai amfana min komai ba, kuma ba za su iya tsamo ni ba?



السورة: Suratu Yasin

الآية : 24

إِنِّيٓ إِذٗا لَّفِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ

“Lalle ni idan na yi haka to tabbas na zama cikin vata mabayyani



السورة: Suratu Yasin

الآية : 74

وَٱتَّخَذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ ءَالِهَةٗ لَّعَلَّهُمۡ يُنصَرُونَ

Suka kuma riqi wasu ababen bauta ba Allah ba, don a taimaka musu



السورة: Suratu Yasin

الآية : 75

لَا يَسۡتَطِيعُونَ نَصۡرَهُمۡ وَهُمۡ لَهُمۡ جُندٞ مُّحۡضَرُونَ

Ba za su iya taimakon su ba, su da gumakan nasu duka ababen tattarawa ne (cikin wuta)



السورة: Suratuz Zumar

الآية : 3

أَلَا لِلَّهِ ٱلدِّينُ ٱلۡخَالِصُۚ وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءَ مَا نَعۡبُدُهُمۡ إِلَّا لِيُقَرِّبُونَآ إِلَى ٱللَّهِ زُلۡفَىٰٓ إِنَّ ٱللَّهَ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡ فِي مَا هُمۡ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي مَنۡ هُوَ كَٰذِبٞ كَفَّارٞ

Ku saurara! Tsantsan addini na Allah ne[1]. Waxanda kuwa suka riqi wasu majivinta al’amari ba Shi ba (suna cewa): “Ba ma bauta musu sai kawai don su kusanta mu ga Allah.” Lalle Allah zai yi hukunci a tsakaninsu game da abin da suke sassavawa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake maqaryaci, mai yawan kafirci


1- Watau addinin kaxaita Allah da guje wa shirka.


السورة: Suratuz Zumar

الآية : 8

۞وَإِذَا مَسَّ ٱلۡإِنسَٰنَ ضُرّٞ دَعَا رَبَّهُۥ مُنِيبًا إِلَيۡهِ ثُمَّ إِذَا خَوَّلَهُۥ نِعۡمَةٗ مِّنۡهُ نَسِيَ مَا كَانَ يَدۡعُوٓاْ إِلَيۡهِ مِن قَبۡلُ وَجَعَلَ لِلَّهِ أَندَادٗا لِّيُضِلَّ عَن سَبِيلِهِۦۚ قُلۡ تَمَتَّعۡ بِكُفۡرِكَ قَلِيلًا إِنَّكَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلنَّارِ

Idan kuma wata cuta ta sami mutum sai ya roqi Ubangijinsa yana mai komawa gare Shi, sannan idan Ya ba shi wata ni’ima daga gare Shi, sai ya manta abin da ya kasance yana roqon Sa a da, ya kuma sanya abokan tarayya ga Allah don ya vatar (da mutane) daga hanyarsa (Allah). Ka ce: “Ka ji daxi xan kaxan da kafircinka; lalle kai kam kana daga cikin ‘yan wuta.”



السورة: Suratuz Zumar

الآية : 65

وَلَقَدۡ أُوحِيَ إِلَيۡكَ وَإِلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكَ لَئِنۡ أَشۡرَكۡتَ لَيَحۡبَطَنَّ عَمَلُكَ وَلَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

Haqiqa kuma an yi maka wahayi kai da waxanda suka gabace ka cewa: “Tabbas idan ka yi shirka lallai aikinka zai vaci, kuma tabbas za ka kasance daga asararru.”



السورة: Suratu Ghafir

الآية : 66

۞قُلۡ إِنِّي نُهِيتُ أَنۡ أَعۡبُدَ ٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَمَّا جَآءَنِيَ ٱلۡبَيِّنَٰتُ مِن رَّبِّي وَأُمِرۡتُ أَنۡ أُسۡلِمَ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Ka ce: “Lalle ni an hana ni in bauta wa waxanda kuke bauta wa ba Allah ba a yayin da (ayoyi) bayyanannu suka zo min daga Ubangijina, an kuma umarce ni da in miqa wuya ga Ubangijin talikai



السورة: Suratu Ghafir

الآية : 73

ثُمَّ قِيلَ لَهُمۡ أَيۡنَ مَا كُنتُمۡ تُشۡرِكُونَ

Sannan kuma a ce da su: “Ina abin da kuka kasance kuna shirka da shi?



السورة: Suratu Ghafir

الآية : 74

مِن دُونِ ٱللَّهِۖ قَالُواْ ضَلُّواْ عَنَّا بَل لَّمۡ نَكُن نَّدۡعُواْ مِن قَبۡلُ شَيۡـٔٗاۚ كَذَٰلِكَ يُضِلُّ ٱللَّهُ ٱلۡكَٰفِرِينَ

“Wanda ba Allah ba?” Suka ce: “Sun vace mana; ai ba mu kasance muna bauta wa wani abu ba a da”. Kamar haka ne Allah Yake vatar da kafirai



السورة: Suratu Fussilat

الآية : 37

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِ ٱلَّيۡلُ وَٱلنَّهَارُ وَٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُۚ لَا تَسۡجُدُواْ لِلشَّمۡسِ وَلَا لِلۡقَمَرِ وَٱسۡجُدُواْۤ لِلَّهِۤ ٱلَّذِي خَلَقَهُنَّ إِن كُنتُمۡ إِيَّاهُ تَعۡبُدُونَ

Kuma dare da wuni da rana da wata suna daga ayoyinsa. Kada ku yi sujjada ga rana ko ga wata, ku yi sujjada ga Allah Wanda Ya halicce su idan har kun kasance Shi kaxai kuke bauta wa



السورة: Suratus Shura

الآية : 21

أَمۡ لَهُمۡ شُرَكَـٰٓؤُاْ شَرَعُواْ لَهُم مِّنَ ٱلدِّينِ مَا لَمۡ يَأۡذَنۢ بِهِ ٱللَّهُۚ وَلَوۡلَا كَلِمَةُ ٱلۡفَصۡلِ لَقُضِيَ بَيۡنَهُمۡۗ وَإِنَّ ٱلظَّـٰلِمِينَ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Ko dai suna da wasu abokan tarayya ne da suka shar’anta musu wani abu na addini wanda Allah bai yi izinin yin sa ba? Ba don kalmar yin hukunci (a lahira) ta tabbata ba, da lalle an yi hukunci a tsakaninsu (tun a duniya). Lalle kuma azzalumai suna da azaba mai raxaxi



السورة: Suratul Jasiya

الآية : 23

أَفَرَءَيۡتَ مَنِ ٱتَّخَذَ إِلَٰهَهُۥ هَوَىٰهُ وَأَضَلَّهُ ٱللَّهُ عَلَىٰ عِلۡمٖ وَخَتَمَ عَلَىٰ سَمۡعِهِۦ وَقَلۡبِهِۦ وَجَعَلَ عَلَىٰ بَصَرِهِۦ غِشَٰوَةٗ فَمَن يَهۡدِيهِ مِنۢ بَعۡدِ ٱللَّهِۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ

Shin kuwa ka ga wanda ya xauki son zuciyarsa (shi ne) abin bautarsa, Allah kuwa Ya vatar da shi a kan yana sane[1], Ya kuma rufe jinsa da zuciyarsa, kuma Ya sanya yana a kan ganinsa, to wane ne zai shiryar da shi in ba Allah ba? Me ya sa ba kwa wa’azantuwa?


1- Watau ya vatar da shi bayan ilimi ya zo masa, saboda Allah ya san cewa ya cancanci vata.


السورة: Suratul Ahqaf 

الآية : 4

قُلۡ أَرَءَيۡتُم مَّا تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَرُونِي مَاذَا خَلَقُواْ مِنَ ٱلۡأَرۡضِ أَمۡ لَهُمۡ شِرۡكٞ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِۖ ٱئۡتُونِي بِكِتَٰبٖ مِّن قَبۡلِ هَٰذَآ أَوۡ أَثَٰرَةٖ مِّنۡ عِلۡمٍ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Ka ce: “Shin kun ga abin da kuke bauta wa ba Allah ba, ku nuna min abin da suka halitta na qasa, ko kuwa suna da tarayya ne a (halittar) sammai; ku kawo mini wani littafi da yake gabanin wannan (Alqur’anin), ko kuma wani virvishi na ilimi idan kun kasance masu gaskiya.”



السورة: Suratul Ahqaf 

الآية : 5

وَمَنۡ أَضَلُّ مِمَّن يَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَن لَّا يَسۡتَجِيبُ لَهُۥٓ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَهُمۡ عَن دُعَآئِهِمۡ غَٰفِلُونَ

Wane ne ya fi vata fiye da wanda yake bauta wa wani ba Allah ba, wanda ba zai amsa masa ba har zuwa ranar alqiyama, kuma su (ababen bautar) rafkanannu ne game da bautar da suke yi musu?



السورة: Suratul Ahqaf 

الآية : 6

وَإِذَا حُشِرَ ٱلنَّاسُ كَانُواْ لَهُمۡ أَعۡدَآءٗ وَكَانُواْ بِعِبَادَتِهِمۡ كَٰفِرِينَ

Idan kuma aka tashi mutane (ababen bautar) za su kasance abokan gabarsu, kuma su zamo masu musanta bautar tasu



السورة: Suratu Qaf 

الآية : 26

ٱلَّذِي جَعَلَ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَأَلۡقِيَاهُ فِي ٱلۡعَذَابِ ٱلشَّدِيدِ

“Wanda ya sanya wani abin bauta daban tare da Allah, saboda haka ku jefa shi cikin azaba mai tsanani.”



السورة: Suratuz Zariyat

الآية : 51

وَلَا تَجۡعَلُواْ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَۖ إِنِّي لَكُم مِّنۡهُ نَذِيرٞ مُّبِينٞ

Kada kuma ku sanya wani abin bauta tare da Allah; lalle ni mai gargaxi ne game da Shi, mai bayyana (gargaxi)



السورة: Suratux Xur

الآية : 43

أَمۡ لَهُمۡ إِلَٰهٌ غَيۡرُ ٱللَّهِۚ سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يُشۡرِكُونَ

Ko kuwa suna da wani abin bauta ne ba Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke tara (Shi da shi)