السورة: Suratul Qasas

الآية : 73

وَمِن رَّحۡمَتِهِۦ جَعَلَ لَكُمُ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ لِتَسۡكُنُواْ فِيهِ وَلِتَبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِهِۦ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

Daga rahamarsa ne kuma Ya sanya muku dare da rana don ku samu nutsuwa a cikinsa (wato dare) kuma don ku nema daga falalarsa (da rana), don kuma ku riqa yin godiya



السورة: Suratul Ahzab

الآية : 43

هُوَ ٱلَّذِي يُصَلِّي عَلَيۡكُمۡ وَمَلَـٰٓئِكَتُهُۥ لِيُخۡرِجَكُم مِّنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِۚ وَكَانَ بِٱلۡمُؤۡمِنِينَ رَحِيمٗا

Shi ne wanda Yake yi muku salati da mala’ikunsa don Ya fitar da ku daga duffai zuwa haske, Allah kuwa Ya kasance Mai rahama ga muminai



السورة: Suratu Faxir

الآية : 2

مَّا يَفۡتَحِ ٱللَّهُ لِلنَّاسِ مِن رَّحۡمَةٖ فَلَا مُمۡسِكَ لَهَاۖ وَمَا يُمۡسِكۡ فَلَا مُرۡسِلَ لَهُۥ مِنۢ بَعۡدِهِۦۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

Abin da Allah Yake yi wa mutane buxi da shi na rahama ba mai iya riqe shi; abin da kuma Yake riqewa ba mai iya sakin sa bayansa. Shi kuma Mabuwayi ne, Mai hikima



السورة: Suratuz Zumar

الآية : 38

وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّنۡ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُۚ قُلۡ أَفَرَءَيۡتُم مَّا تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ إِنۡ أَرَادَنِيَ ٱللَّهُ بِضُرٍّ هَلۡ هُنَّ كَٰشِفَٰتُ ضُرِّهِۦٓ أَوۡ أَرَادَنِي بِرَحۡمَةٍ هَلۡ هُنَّ مُمۡسِكَٰتُ رَحۡمَتِهِۦۚ قُلۡ حَسۡبِيَ ٱللَّهُۖ عَلَيۡهِ يَتَوَكَّلُ ٱلۡمُتَوَكِّلُونَ

Tabbas da za ka tambaye su wanda ya halicci sammai da qasa, lalle za su ce: “Allah ne.” Ka ce (da su): “Ku ba ni labarin waxanda kuke bauta wa ba Allah ba, idan Allah Ya nufe ni da wata cuta, yanzu za su iya yaye cutar tasa, ko kuwa idan Ya nufe ni da rahama yanzu za su iya riqe rahamarsa?” Ka ce: “Allah Ya ishe ni; a gare Shi ne kawai masu dogaro suke dogaro.”



السورة: Suratuz Zumar

الآية : 53

۞قُلۡ يَٰعِبَادِيَ ٱلَّذِينَ أَسۡرَفُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ لَا تَقۡنَطُواْ مِن رَّحۡمَةِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَغۡفِرُ ٱلذُّنُوبَ جَمِيعًاۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ

Ka ce[1]: “Ya ku bayina waxanda suka vata kawunansu sosai (da kafirci da savon Allah), kada ku xebe qauna daga rahamar Allah. Lalle Allah Yana gafarta zunubai baki xaya[2]. Lalle Shi Mai gafara ne, Mai rahama


1- Allah ne yake umartar Manzonsa () da ya faxa wa muminai bayin Allah.


2- Watau ga wanda ya tuba.


السورة: Suratu Ghafir

الآية : 7

ٱلَّذِينَ يَحۡمِلُونَ ٱلۡعَرۡشَ وَمَنۡ حَوۡلَهُۥ يُسَبِّحُونَ بِحَمۡدِ رَبِّهِمۡ وَيُؤۡمِنُونَ بِهِۦ وَيَسۡتَغۡفِرُونَ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْۖ رَبَّنَا وَسِعۡتَ كُلَّ شَيۡءٖ رَّحۡمَةٗ وَعِلۡمٗا فَٱغۡفِرۡ لِلَّذِينَ تَابُواْ وَٱتَّبَعُواْ سَبِيلَكَ وَقِهِمۡ عَذَابَ ٱلۡجَحِيمِ

Waxanda suke xauke da Al’arshi da waxanda suke kewaye da shi suna yin tasbihi da yabon Ubangijinsu, suna kuma yin imani da Shi, kuma suna nema wa waxanda suka yi imani gafara, (suna cewa): “Ya Ubangiijnmu, ka yalwaci kowane abu da rahama da ilimi, to Ka gafarta wa waxanda suka tuba suka kuma bi hanyarka, Ka kuma kiyaye su daga azabar (wutar) Jahimu



السورة: Suratus Shura

الآية : 8

وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَجَعَلَهُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَلَٰكِن يُدۡخِلُ مَن يَشَآءُ فِي رَحۡمَتِهِۦۚ وَٱلظَّـٰلِمُونَ مَا لَهُم مِّن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٍ

Da kuma Allah Ya ga dama da Ya sanya su al’umma xaya (watau a kan addini xaya), sai dai kuma Yana shigar da wanda Ya ga dama cikin rahamarsa. Azzalumai kuma ba su da wani majivinci ko wani mataimaki



السورة: Suratus Shura

الآية : 28

وَهُوَ ٱلَّذِي يُنَزِّلُ ٱلۡغَيۡثَ مِنۢ بَعۡدِ مَا قَنَطُواْ وَيَنشُرُ رَحۡمَتَهُۥۚ وَهُوَ ٱلۡوَلِيُّ ٱلۡحَمِيدُ

Shi ne kuma Yake saukar da ruwan sama bayan sun xebe qauna, Ya kuma yaxa rahamarsa. Kuma Shi ne Majivincin al’amura, Sha-yabo



السورة: Suratuz Zukhruf 

الآية : 32

أَهُمۡ يَقۡسِمُونَ رَحۡمَتَ رَبِّكَۚ نَحۡنُ قَسَمۡنَا بَيۡنَهُم مَّعِيشَتَهُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۚ وَرَفَعۡنَا بَعۡضَهُمۡ فَوۡقَ بَعۡضٖ دَرَجَٰتٖ لِّيَتَّخِذَ بَعۡضُهُم بَعۡضٗا سُخۡرِيّٗاۗ وَرَحۡمَتُ رَبِّكَ خَيۡرٞ مِّمَّا يَجۡمَعُونَ

Yanzu su ne suke raba rahamar Ubangijinka (ta annabci)? Mu ne Muka raba musu arzikinsu a rayuwar duniya. Muka kuma xaukaka darajojin sashinsu a kan sashi, don wani sashin ya riqi wani sashi mai yi masa hidima. Rahamar Ubangijinka kuma ita ta fi abin da suke tarawa (na duniya)



السورة: Suratud Dukhan

الآية : 6

رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

Don rahama daga Ubangijinka. Lalle shi Mai ji ne, Masani



السورة: Suratul Jasiya

الآية : 30

فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ فَيُدۡخِلُهُمۡ رَبُّهُمۡ فِي رَحۡمَتِهِۦۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡمُبِينُ

To amma waxanda suka yi imani suka yi ayyuka nagari, to Ubangijinsu zai shigar da su cikin rahamarsa. Wannan shi ne rabo mabayyani



السورة: Suratul Fat’h

الآية : 25

هُمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَصَدُّوكُمۡ عَنِ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ وَٱلۡهَدۡيَ مَعۡكُوفًا أَن يَبۡلُغَ مَحِلَّهُۥۚ وَلَوۡلَا رِجَالٞ مُّؤۡمِنُونَ وَنِسَآءٞ مُّؤۡمِنَٰتٞ لَّمۡ تَعۡلَمُوهُمۡ أَن تَطَـُٔوهُمۡ فَتُصِيبَكُم مِّنۡهُم مَّعَرَّةُۢ بِغَيۡرِ عِلۡمٖۖ لِّيُدۡخِلَ ٱللَّهُ فِي رَحۡمَتِهِۦ مَن يَشَآءُۚ لَوۡ تَزَيَّلُواْ لَعَذَّبۡنَا ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡهُمۡ عَذَابًا أَلِيمًا

Su ne waxanda suka kafirta suka kuma hana ku isa ga Masallaci mai alfarma, suka kuma hana dabbobin hadaya isa wurin yankansu. Kuma ba don wasu mazaje muminai da wasu mataye muminai da ba ku san su ba, don kada ku kashe su, sannan wani laifi nasu ya same ku ba tare da sani ba, (da Ya ba ku damar yaqar su. Wannan ya faru ne) don Allah Ya shigar da wanda Ya ga dama cikin rahamarsa. Da sun ware to lalle da Mun azabtar da waxanda suka kafirta daga cikinsu azaba mai tsanani



السورة: Suratul Hadid

الآية : 28

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَءَامِنُواْ بِرَسُولِهِۦ يُؤۡتِكُمۡ كِفۡلَيۡنِ مِن رَّحۡمَتِهِۦ وَيَجۡعَل لَّكُمۡ نُورٗا تَمۡشُونَ بِهِۦ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Ya ku waxanda suka imani, ku kiyaye dokokin Allah, ku kuma yi imani da Manzonsa, zai ba ku rivi biyu na rahamarsa, Ya kuma sanya muku haske da za ku riqa tafiya da shi, kuma Ya gafarta muku. Domin kuwa Allah Mai gafara ne, Mai rahama



السورة: Suratul Hashr

الآية : 22

هُوَ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِۖ هُوَ ٱلرَّحۡمَٰنُ ٱلرَّحِيمُ

Shi ne Allah wanda babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi; Masanin voye da sarari; kuma Shi ne Mai rahama, Mai jin qai



السورة: Suratul Insan

الآية : 31

يُدۡخِلُ مَن يَشَآءُ فِي رَحۡمَتِهِۦۚ وَٱلظَّـٰلِمِينَ أَعَدَّ لَهُمۡ عَذَابًا أَلِيمَۢا

Yana shigar da wanda Ya ga dama cikin rahamarsa. Azzalumai kuwa Ya tanadar musu azaba mai raxaxi