السورة: Suratul Baqara

الآية : 262

ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ ثُمَّ لَا يُتۡبِعُونَ مَآ أَنفَقُواْ مَنّٗا وَلَآ أَذٗى لَّهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

Waxanda suke ciyar da dukiyoyinsu a hanyar Allah, sannan ba sa bin abin da suka ciyar da gori ko cuta, (waxannan) suna da ladansu a wajen Ubangijinsu, kuma babu tsoro a tare da su, kuma ba za su yi baqin ciki ba



السورة: Suratul Baqara

الآية : 263

۞قَوۡلٞ مَّعۡرُوفٞ وَمَغۡفِرَةٌ خَيۡرٞ مِّن صَدَقَةٖ يَتۡبَعُهَآ أَذٗىۗ وَٱللَّهُ غَنِيٌّ حَلِيمٞ

Kyakkyawar magana da yafiya sun fi sadakar da cutarwa za ta biyo bayanta alheri. Kuma Allah Shi ne Wadatacce, Mai haquri



السورة: Suratul Baqara

الآية : 264

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُبۡطِلُواْ صَدَقَٰتِكُم بِٱلۡمَنِّ وَٱلۡأَذَىٰ كَٱلَّذِي يُنفِقُ مَالَهُۥ رِئَآءَ ٱلنَّاسِ وَلَا يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۖ فَمَثَلُهُۥ كَمَثَلِ صَفۡوَانٍ عَلَيۡهِ تُرَابٞ فَأَصَابَهُۥ وَابِلٞ فَتَرَكَهُۥ صَلۡدٗاۖ لَّا يَقۡدِرُونَ عَلَىٰ شَيۡءٖ مِّمَّا كَسَبُواْۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku vata sadaqoqinku da gori da cutarwa, kamar wanda yake ciyar da dukiyarsa don mutane su gani, kuma ba ya imani da Allah da ranar lahira; to misalinsa kamar misalin kamfa ne da turvaya take a kansa sai ruwan sama mamako ya same shi, sai ya bar shi tatas. Ba za su amfana da komai daga abin da suka aikata ba. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane kafirai



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 111

لَن يَضُرُّوكُمۡ إِلَّآ أَذٗىۖ وَإِن يُقَٰتِلُوكُمۡ يُوَلُّوكُمُ ٱلۡأَدۡبَارَ ثُمَّ لَا يُنصَرُونَ

Ba za su tava iya cutar da ku ba sai dai cutarwa kaxan; kuma in da za su yaqe ku, sai sun juya muku baya, sannan ba za a taimake su ba



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 159

فَبِمَا رَحۡمَةٖ مِّنَ ٱللَّهِ لِنتَ لَهُمۡۖ وَلَوۡ كُنتَ فَظًّا غَلِيظَ ٱلۡقَلۡبِ لَٱنفَضُّواْ مِنۡ حَوۡلِكَۖ فَٱعۡفُ عَنۡهُمۡ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لَهُمۡ وَشَاوِرۡهُمۡ فِي ٱلۡأَمۡرِۖ فَإِذَا عَزَمۡتَ فَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُتَوَكِّلِينَ

To saboda rahama ta musamman daga Allah, sai ka zamo mai tausasawa gare su; in da kuwa ka kasance mai kaushin mu’amala, mai qeqasasshiyar zuciya ne, to da sun watse sun bar ka. To ka yi musu afuwa, kuma ka nema musu gafara, kuma ka nemi shawararsu cikin duk lamura; amma idan ka riga ka qulla niyya, to ka dogara ga Allah. Lalle Allah Yana son masu dogara a gare Shi



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 186

۞لَتُبۡلَوُنَّ فِيٓ أَمۡوَٰلِكُمۡ وَأَنفُسِكُمۡ وَلَتَسۡمَعُنَّ مِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلِكُمۡ وَمِنَ ٱلَّذِينَ أَشۡرَكُوٓاْ أَذٗى كَثِيرٗاۚ وَإِن تَصۡبِرُواْ وَتَتَّقُواْ فَإِنَّ ذَٰلِكَ مِنۡ عَزۡمِ ٱلۡأُمُورِ

Lalle za a jarrabe ku a cikin dukiyoyinku da rayukanku, kuma lalle za ku riqa jin cutarwa mai yawa daga waxanda aka bai wa Littafi kafinku, haka kuma daga waxanda suke mushirikai. Amma idan har kuka yi haquri, kuma kuka tsare dokar Allah, to lalle wannan yana daga cikin manyan al’amura



السورة: Suratut Tauba

الآية : 65

وَلَئِن سَأَلۡتَهُمۡ لَيَقُولُنَّ إِنَّمَا كُنَّا نَخُوضُ وَنَلۡعَبُۚ قُلۡ أَبِٱللَّهِ وَءَايَٰتِهِۦ وَرَسُولِهِۦ كُنتُمۡ تَسۡتَهۡزِءُونَ

Kuma lalle idan har ka tambaye su, tabbas za su ce: “Kawai muna kutse ne da wasa.” To ka ce (da su): “Yanzu Allah ne da ayoyinsa da Manzonsa kuka kasance kuna yi wa izgili?”



السورة: Suratut Tauba

الآية : 79

ٱلَّذِينَ يَلۡمِزُونَ ٱلۡمُطَّوِّعِينَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ فِي ٱلصَّدَقَٰتِ وَٱلَّذِينَ لَا يَجِدُونَ إِلَّا جُهۡدَهُمۡ فَيَسۡخَرُونَ مِنۡهُمۡ سَخِرَ ٱللَّهُ مِنۡهُمۡ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٌ

Waxanda kuma suke aibata muminai masu yin sadaka (mai yawa) don neman lada da kuma waxanda ba su da abin da za su bayar sai (kaxan) gwargwadon wahalarsu, sannan su riqa yi musu izgili, to Allah zai mayar musu da sakamakon izgilinsu, suna kuma da azaba mai raxaxi



السورة: Suratul Isra’i

الآية : 53

وَقُل لِّعِبَادِي يَقُولُواْ ٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُۚ إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ يَنزَغُ بَيۡنَهُمۡۚ إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ كَانَ لِلۡإِنسَٰنِ عَدُوّٗا مُّبِينٗا

Ka kuma ce da bayina su faxi (magana) wadda ita ce ta fi kyau. Lalle Shaixan yana vata tsakaninsu. Lalle Shaixan ya tabbata maqiyi ne mai bayyana (qiyayya) ga mutum



السورة: Suratul Mu’uminun

الآية : 109

إِنَّهُۥ كَانَ فَرِيقٞ مِّنۡ عِبَادِي يَقُولُونَ رَبَّنَآ ءَامَنَّا فَٱغۡفِرۡ لَنَا وَٱرۡحَمۡنَا وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلرَّـٰحِمِينَ

“Lalle yadda lamarin yake, wata qungiya daga bayina sun kasance suna cewa: “Ya Ubangijinmu, mun yi imani, sai Ka gafarta mana, kuma Ka ji qan mu, Kai ne kuwa Fiyayyen masu jin qai



السورة: Suratul Mu’uminun

الآية : 110

فَٱتَّخَذۡتُمُوهُمۡ سِخۡرِيًّا حَتَّىٰٓ أَنسَوۡكُمۡ ذِكۡرِي وَكُنتُم مِّنۡهُمۡ تَضۡحَكُونَ

“Sai kuka xauke su ababen yi wa izgili, har suka mantar da ku ambatona kuka kuma kasance kuna yi musu dariya



السورة: Suratul Mu’uminun

الآية : 111

إِنِّي جَزَيۡتُهُمُ ٱلۡيَوۡمَ بِمَا صَبَرُوٓاْ أَنَّهُمۡ هُمُ ٱلۡفَآئِزُونَ

“Lalle Ni Na saka musu a yau saboda haqurinsu. Lalle kuma su ne marabauta.”



السورة: Suratul Ahzab

الآية : 58

وَٱلَّذِينَ يُؤۡذُونَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ بِغَيۡرِ مَا ٱكۡتَسَبُواْ فَقَدِ ٱحۡتَمَلُواْ بُهۡتَٰنٗا وَإِثۡمٗا مُّبِينٗا

Waxanda suke cutar muminai maza da muminai mata ba tare da sun yi laifi ba, to haqiqa sun xauki nauyin qage da kuma zunubi bayyananne



السورة: Suratul Ahzab

الآية : 69

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ ءَاذَوۡاْ مُوسَىٰ فَبَرَّأَهُ ٱللَّهُ مِمَّا قَالُواْۚ وَكَانَ عِندَ ٱللَّهِ وَجِيهٗا

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku zamanto kamar waxanda suka cuci Musa sai Allah Ya wanke shi daga abin da suka faxa (a kansa). Ya kuma kasance mai alfarma ne a wurin Allah



السورة: Suratuz Zumar

الآية : 56

أَن تَقُولَ نَفۡسٞ يَٰحَسۡرَتَىٰ عَلَىٰ مَا فَرَّطتُ فِي جَنۢبِ ٱللَّهِ وَإِن كُنتُ لَمِنَ ٱلسَّـٰخِرِينَ

“Don kada wani rai ya ce: ‘Kaicona game da abin da na yi sakaci na haqqin Allah, ni tabbas na kasance daga masu yin izgili.’



السورة: Suratul Hujurat

الآية : 11

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا يَسۡخَرۡ قَوۡمٞ مِّن قَوۡمٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُونُواْ خَيۡرٗا مِّنۡهُمۡ وَلَا نِسَآءٞ مِّن نِّسَآءٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُنَّ خَيۡرٗا مِّنۡهُنَّۖ وَلَا تَلۡمِزُوٓاْ أَنفُسَكُمۡ وَلَا تَنَابَزُواْ بِٱلۡأَلۡقَٰبِۖ بِئۡسَ ٱلِٱسۡمُ ٱلۡفُسُوقُ بَعۡدَ ٱلۡإِيمَٰنِۚ وَمَن لَّمۡ يَتُبۡ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada wasu mutane su yi wa wasu mutane izgili, mai yiwuwa ne su zamanto sun fi su alheri, kuma kada wasu mata (su yi wa) wasu mata (izgili), mai yiwuwa ne su zamanto sun fi su alheri; kada kuma ku riqa aibata junanku, kuma kada ku riqa jifan juna da munanan laquba (da kuke qi). Tir da sunan fasiqanci bayan imani. Wanda duk bai tuba ba, to waxannan su ne azzalumai



السورة: Suratul Muxaffifin

الآية : 29

إِنَّ ٱلَّذِينَ أَجۡرَمُواْ كَانُواْ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ يَضۡحَكُونَ

Lalle waxanda suka yi manyan laifuka[1] sun kasance suna yi wa waxanda suka yi imani dariya (a duniya)


1- Watau kafirai.


السورة: Suratul Muxaffifin

الآية : 30

وَإِذَا مَرُّواْ بِهِمۡ يَتَغَامَزُونَ

Kuma idan suka wuce ta wajensu sai su riqa zunxen su



السورة: Suratul Muxaffifin

الآية : 31

وَإِذَا ٱنقَلَبُوٓاْ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِمُ ٱنقَلَبُواْ فَكِهِينَ

Idan kuma sun koma wurin iyalinsu sai su komo suna masu farin ciki[1]


1- Watau saboda izgili da dariya da suka yi wa muminai.


السورة: Suratul Muxaffifin

الآية : 32

وَإِذَا رَأَوۡهُمۡ قَالُوٓاْ إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ لَضَآلُّونَ

Kuma idan sun gan su sai su ce: “Lalle waxannan vatattu ne.”



السورة: Suratul Muxaffifin

الآية : 33

وَمَآ أُرۡسِلُواْ عَلَيۡهِمۡ حَٰفِظِينَ

Ba a kuwa aiko su don su zama masu tsaron su ba



السورة: Suratul Muxaffifin

الآية : 34

فَٱلۡيَوۡمَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنَ ٱلۡكُفَّارِ يَضۡحَكُونَ

To a wannan rana ne[1] waxanda suka yi imani za su yi wa kafirai dariya


1- Watau ranar alqiyama.


السورة: Suratul Humaza

الآية : 1

وَيۡلٞ لِّكُلِّ هُمَزَةٖ لُّمَزَةٍ

Tsananin azaba ya tabbata ga duk wani mai yawan qyafice mai yawan suka[1]


1- Watau yawan qyafice ga mutane, yana kuma yawan sukan su da aibata su a bayan idanuwansu..