السورة: Suratul Baqara

الآية : 250

وَلَمَّا بَرَزُواْ لِجَالُوتَ وَجُنُودِهِۦ قَالُواْ رَبَّنَآ أَفۡرِغۡ عَلَيۡنَا صَبۡرٗا وَثَبِّتۡ أَقۡدَامَنَا وَٱنصُرۡنَا عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Kuma yayin da suka yi fito-na-fito da Jalutu da rundunarsa, sai suka ce: “Ya Ubangijinmu, Ka zubo mana haquri na musamman, kuma Ka tabbatar da dugaduganmu, kuma Ka taimake mu a kan mutane kafirai.”



السورة: Suratul Baqara

الآية : 251

فَهَزَمُوهُم بِإِذۡنِ ٱللَّهِ وَقَتَلَ دَاوُۥدُ جَالُوتَ وَءَاتَىٰهُ ٱللَّهُ ٱلۡمُلۡكَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَعَلَّمَهُۥ مِمَّا يَشَآءُۗ وَلَوۡلَا دَفۡعُ ٱللَّهِ ٱلنَّاسَ بَعۡضَهُم بِبَعۡضٖ لَّفَسَدَتِ ٱلۡأَرۡضُ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ ذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ

Sai suka murqushe su da izinin Allah, kuma Dawudu ya kashe Jalutu, sai Allah Ya ba shi mulki da hikima, kuma Ya sanar da shi irin abin da Ya ga dama. Ba don yadda Allah Yake kare wani sashin mutane da wani sashi ba, to lalle da qasa ta lalace, sai dai kuma Allah Ma’abocin falala ne ga talikai



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 123

وَلَقَدۡ نَصَرَكُمُ ٱللَّهُ بِبَدۡرٖ وَأَنتُمۡ أَذِلَّةٞۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

Kuma tabbas haqiqa Allah Ya taimake ku a (yaqin) Badar, alhalin kuna raunana, to ku ji tsoron Allah don ku zamanto masu godiya a gare Shi



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 124

إِذۡ تَقُولُ لِلۡمُؤۡمِنِينَ أَلَن يَكۡفِيَكُمۡ أَن يُمِدَّكُمۡ رَبُّكُم بِثَلَٰثَةِ ءَالَٰفٖ مِّنَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ مُنزَلِينَ

Ka tuna lokacin da kake ce wa muminai: “Shin bai ishe ku ba idan Ubangijinku Ya kawo muku agajin mala’iku dubu uku waxanda za a saukar da su (daga sama)?”



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 125

بَلَىٰٓۚ إِن تَصۡبِرُواْ وَتَتَّقُواْ وَيَأۡتُوكُم مِّن فَوۡرِهِمۡ هَٰذَا يُمۡدِدۡكُمۡ رَبُّكُم بِخَمۡسَةِ ءَالَٰفٖ مِّنَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ مُسَوِّمِينَ

Haka ne, idan har za ku yi haquri, kuma ku yi taqawa, kuma (kafirai) suka auko muku cikin gaggawa a wannan lokacin, to Ubangijinku zai qaro muku agaji da mala’iku dubu biyar masu alamomi



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 126

وَمَا جَعَلَهُ ٱللَّهُ إِلَّا بُشۡرَىٰ لَكُمۡ وَلِتَطۡمَئِنَّ قُلُوبُكُم بِهِۦۗ وَمَا ٱلنَّصۡرُ إِلَّا مِنۡ عِندِ ٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَكِيمِ

Kuma Allah bai sanya wannan ba sai don albishir a gare ku, kuma domin zukatanku su nutsu da shi. Kuma nasara ba ta zuwa daga kowa sai daga Allah Mabuwayi, Mai hikima



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 127

لِيَقۡطَعَ طَرَفٗا مِّنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَوۡ يَكۡبِتَهُمۡ فَيَنقَلِبُواْ خَآئِبِينَ

Domin Ya karya lagon wani vangare na kafirai ko Ya qasqantar da su, sai su juya da baya suna tavavvu



السورة: Suratul Anfal

الآية : 10

وَمَا جَعَلَهُ ٱللَّهُ إِلَّا بُشۡرَىٰ وَلِتَطۡمَئِنَّ بِهِۦ قُلُوبُكُمۡۚ وَمَا ٱلنَّصۡرُ إِلَّا مِنۡ عِندِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ

Kuma (wannan taimakon) Allah bai sanya shi ba, sai don albishir a gare ku, don kuma zukatanku su nutsu da shi. Babu kuma wata nasara sai daga wurin Allah. Lalle Allah Mabuwayi ne Mai hikima



السورة: Suratut Tauba

الآية : 25

لَقَدۡ نَصَرَكُمُ ٱللَّهُ فِي مَوَاطِنَ كَثِيرَةٖ وَيَوۡمَ حُنَيۡنٍ إِذۡ أَعۡجَبَتۡكُمۡ كَثۡرَتُكُمۡ فَلَمۡ تُغۡنِ عَنكُمۡ شَيۡـٔٗا وَضَاقَتۡ عَلَيۡكُمُ ٱلۡأَرۡضُ بِمَا رَحُبَتۡ ثُمَّ وَلَّيۡتُم مُّدۡبِرِينَ

Lalle haqiqa Allah Ya taimake ku a wurare da yawa, da kuma ranar (yaqin) Hunaini lokacin da yawanku ya ruxe ku sai (yawan naku) bai amfana muku komai ba, qasa kuma ta yi muku qunci duk da yalwarta, sannan kuka juya kuna masu ba da baya



السورة: Suratut Tauba

الآية : 26

ثُمَّ أَنزَلَ ٱللَّهُ سَكِينَتَهُۥ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ وَعَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَأَنزَلَ جُنُودٗا لَّمۡ تَرَوۡهَا وَعَذَّبَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۚ وَذَٰلِكَ جَزَآءُ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Sannan Allah Ya sauqar wa da Manzonsa da kuma muminai nutsuwarsa, Ya kuma saukar da wasu rundunoni da ba kwa gani, Ya kuma azabtar da waxanda suka kafirta. Wannan kuwa shi ne sakamakon kafirai



السورة: Suratu Yusuf 

الآية : 110

حَتَّىٰٓ إِذَا ٱسۡتَيۡـَٔسَ ٱلرُّسُلُ وَظَنُّوٓاْ أَنَّهُمۡ قَدۡ كُذِبُواْ جَآءَهُمۡ نَصۡرُنَا فَنُجِّيَ مَن نَّشَآءُۖ وَلَا يُرَدُّ بَأۡسُنَا عَنِ ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ

Har yayin da manzanni suka xebe qauna (da imanin mutanensu), su kuma (kafiran) suka yi zaton an faxa musu qarya ne (game da zuwan azabar Allah) sai taimakonmu ya zo musu, sai Muka tserar da wanda Muka ga dama; ba kuwa za a kawar da azabarmu daga mutane masu laifi ba



السورة: Suratul Hajji

الآية : 39

أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَٰتَلُونَ بِأَنَّهُمۡ ظُلِمُواْۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ نَصۡرِهِمۡ لَقَدِيرٌ

An yi izini (na yin yaqi) ga waxanda ake yaqa[1] don ko lalle an zalunce su. Lalle kuma Allah Mai iko ne bisa taimakon su


1- Watau sahabban Annabi () waxanda kafirai a lokacin suke yaqar su.


السورة: Suratun Namli

الآية : 34

قَالَتۡ إِنَّ ٱلۡمُلُوكَ إِذَا دَخَلُواْ قَرۡيَةً أَفۡسَدُوهَا وَجَعَلُوٓاْ أَعِزَّةَ أَهۡلِهَآ أَذِلَّةٗۚ وَكَذَٰلِكَ يَفۡعَلُونَ

Sai ta ce: “Lalle sarakuna idan suka shigo wata alqarya sai su yi kaca-kaca da ita, kuma su mayar da manyanta qasqantattu; kuma haka suke aikatawa



السورة: Suratur Rum

الآية : 2

غُلِبَتِ ٱلرُّومُ

An yi galaba a kan Rumawa[1]


1- Watau Farisawa masu bautar wuta sun yi galaba a kan Rumawa masu bin addinin Annabi Isa () a wani yaqi da ya varke tsakaninsu.


السورة: Suratur Rum

الآية : 3

فِيٓ أَدۡنَى ٱلۡأَرۡضِ وَهُم مِّنۢ بَعۡدِ غَلَبِهِمۡ سَيَغۡلِبُونَ

A qasa mafi kusa (da su), su kuma da sannu za su yi galaba (a kan Farisa) bayan galabar da aka yi a kansu



السورة: Suratur Rum

الآية : 4

فِي بِضۡعِ سِنِينَۗ لِلَّهِ ٱلۡأَمۡرُ مِن قَبۡلُ وَمِنۢ بَعۡدُۚ وَيَوۡمَئِذٖ يَفۡرَحُ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ

A cikin ‘yan tsirarun shekarun (da ba su kai goma ba). Al’amari a da can da nan gaba na Allah ne. A wannan ranar ne muminai za su yi farin ciki



السورة: Suratur Rum

الآية : 5

بِنَصۡرِ ٱللَّهِۚ يَنصُرُ مَن يَشَآءُۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Da samun nasar Allah (a kan Farisa). Shi Yake taimakon wanda Ya ga dama; domin kuwa Shi ne Mabuwayi, Mai rahama



السورة: Suratus Sajda

الآية : 28

وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلۡفَتۡحُ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Suna kuma cewa: “Yaushe ne (ranar) wannan hukuncin idan kun kasance masu gaskiya?



السورة: Suratus Sajda

الآية : 29

قُلۡ يَوۡمَ ٱلۡفَتۡحِ لَا يَنفَعُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِيمَٰنُهُمۡ وَلَا هُمۡ يُنظَرُونَ

Ka ce: “Ranar hukuncin, waxanda suka kafirce, imaninsu ba zai amfane su ba, kuma ba ma za a saurara musu ba.”



السورة: Suratul Fat’h

الآية : 1

إِنَّا فَتَحۡنَا لَكَ فَتۡحٗا مُّبِينٗا

Lalle Mu ne Muka yi maka buxi, buxi mabayyani[1]


1- Watau ya ba shi nasara ta hanyar sulhun Hudaibiyya, wata yarjejeniya da Musulmi suka qulla da Quraishawa a shekara ta shida, don tsagaita yaqi a tsakaninsu har tsawon shekara goma.


السورة: Suratul Fat’h

الآية : 3

وَيَنصُرَكَ ٱللَّهُ نَصۡرًا عَزِيزًا

Allah kuma zai taimake ka da nasara mai girma



السورة: Suratul Fat’h

الآية : 18

۞لَّقَدۡ رَضِيَ ٱللَّهُ عَنِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ إِذۡ يُبَايِعُونَكَ تَحۡتَ ٱلشَّجَرَةِ فَعَلِمَ مَا فِي قُلُوبِهِمۡ فَأَنزَلَ ٱلسَّكِينَةَ عَلَيۡهِمۡ وَأَثَٰبَهُمۡ فَتۡحٗا قَرِيبٗا

Haqiqa Allah Ya yarda da muminai yayin da suke yi maka mubaya’a a qarqashin bishiyar[1] nan, to Allah Ya san abin da yake cikin zukatansu, sai Ya saukar musu da nutsuwa Ya kuma saka musu da buxi na kurkusa[2]


1- Su ne sahabban Annabi () kimanin su dubu da xari huxu da suka yi wa Manzon Allah () mubaya’a a Hudaibiyya a kan za su jajirce wajen yaqi tare da shi.


2- Watau buxe Khaibar a madadin rashin samun shiga garin Makka su yi umara.


السورة: Suratul Fat’h

الآية : 19

وَمَغَانِمَ كَثِيرَةٗ يَأۡخُذُونَهَاۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمٗا

Da kuma ganimomi masu yawa da za su yi ta kwasar su. Allah kuwa Ya kasance Mabuwayi ne, Mai hikima



السورة: Suratul Fat’h

الآية : 20

وَعَدَكُمُ ٱللَّهُ مَغَانِمَ كَثِيرَةٗ تَأۡخُذُونَهَا فَعَجَّلَ لَكُمۡ هَٰذِهِۦ وَكَفَّ أَيۡدِيَ ٱلنَّاسِ عَنكُمۡ وَلِتَكُونَ ءَايَةٗ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ وَيَهۡدِيَكُمۡ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا

Allah kuma Ya yi muku alqawarin wasu ganimomi masu yawa da za ku yi ta kwasar su, sai Ya gaggauto muku da wannan (ganimar Khaibara) Ya kuma kame muku hannayen mutanen (wato Yahudu), don kuwa (wannan) ya zama aya ga muminai, Ya kuma shiryar da su hanya madaidaiciya



السورة: Suratul Fat’h

الآية : 21

وَأُخۡرَىٰ لَمۡ تَقۡدِرُواْ عَلَيۡهَا قَدۡ أَحَاطَ ٱللَّهُ بِهَاۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٗا

Xaya (ganimar) kuwa ba ku sami iko a kanta ba[1], haqiqa Allah Ya san da ita, Allah kuwa Ya kasance Mai iko ne a kan komai


1- Kamar abin da suka samu na ganimomin Farisawa da Rumawa lokacin da suka cinye su da yaqi.


السورة: Suratul Fat’h

الآية : 27

لَّقَدۡ صَدَقَ ٱللَّهُ رَسُولَهُ ٱلرُّءۡيَا بِٱلۡحَقِّۖ لَتَدۡخُلُنَّ ٱلۡمَسۡجِدَ ٱلۡحَرَامَ إِن شَآءَ ٱللَّهُ ءَامِنِينَ مُحَلِّقِينَ رُءُوسَكُمۡ وَمُقَصِّرِينَ لَا تَخَافُونَۖ فَعَلِمَ مَا لَمۡ تَعۡلَمُواْ فَجَعَلَ مِن دُونِ ذَٰلِكَ فَتۡحٗا قَرِيبًا

Haqiqa Allah Ya tabbatar wa Manzonsa gaskiyar mafarkin cewa, lalle za ku shiga Masallaci mai alfarma insha Allahu, kuna cikin aminci kuna masu aske kawunanku da masu yin saisaye, ba tare da kuna jin tsoron (komai) ba, to Ya san abin da ba ku sani ba, sai Ya sanya buxi na kusa[1] kafin wannan


1- Watau sulhul Hudaibiyya da buxe Khaibar.


السورة: Suratul Mujadila

الآية : 21

كَتَبَ ٱللَّهُ لَأَغۡلِبَنَّ أَنَا۠ وَرُسُلِيٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ قَوِيٌّ عَزِيزٞ

Allah Ya rubuta cewa: Lalle Ni da manzannina ne za mu yi galaba. Lalle Allah Mai qarfi ne, Mabuwayi



السورة: Suratus Saff 

الآية : 13

وَأُخۡرَىٰ تُحِبُّونَهَاۖ نَصۡرٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَفَتۡحٞ قَرِيبٞۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Da kuma wata xayar da kuke so; (watau) nasara daga Allah da kuma buxi a kusa. Ka kuma yi wa muminai albishir



السورة: Suratun Nasr

الآية : 1

إِذَا جَآءَ نَصۡرُ ٱللَّهِ وَٱلۡفَتۡحُ

Idan nasarar Allah ta zo da kuma buxe (Makka)