قُتِلَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡأُخۡدُودِ
An la’anci ma’abota rami (na azabtar da muminai)[1]
1- Wani azzalumin sarki ne da aka yi a Najrana ta qasar Yaman kafin aiko Annabi () wanda aka haqa masa rami aka hura wuta, ya riqa jefa muminai a cikinsa yana qona su da ransu.
ٱلنَّارِ ذَاتِ ٱلۡوَقُودِ
Na wuta mai ruruwa
إِذۡ هُمۡ عَلَيۡهَا قُعُودٞ
Yayin da suke zaune a gefenta
وَهُمۡ عَلَىٰ مَا يَفۡعَلُونَ بِٱلۡمُؤۡمِنِينَ شُهُودٞ
Alhali su suna kallon abin da suke aikata wa muminai
وَمَا نَقَمُواْ مِنۡهُمۡ إِلَّآ أَن يُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَمِيدِ
Babu kuwa abin da suke tuhumar su da shi sai don kawai sun yi imani da Allah Mabuwayi, Sha-yabo
ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٌ
Wanda Yake da mulkin sammai da qasa. Allah kuma Mai ganin komai ne
إِنَّ ٱلَّذِينَ فَتَنُواْ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ ثُمَّ لَمۡ يَتُوبُواْ فَلَهُمۡ عَذَابُ جَهَنَّمَ وَلَهُمۡ عَذَابُ ٱلۡحَرِيقِ
Lalle waxanda suka azabtar da muminai maza da muminai mata sannan ba su tuba ba, to suna da azabar Jahannama, suna kuma da azabar quna