وَلۡيَحۡكُمۡ أَهۡلُ ٱلۡإِنجِيلِ بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فِيهِۚ وَمَن لَّمۡ يَحۡكُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ
Lalle kuma ma’abota Linjila su yi hukunci da abin da Allah Ya saukar a cikinsa. Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba kuwa, to waxannan su ne fasiqai
وَلَوۡ أَنَّ أَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ ءَامَنُواْ وَٱتَّقَوۡاْ لَكَفَّرۡنَا عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡ وَلَأَدۡخَلۡنَٰهُمۡ جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ
Kuma in da a ce waxanda aka bai wa Littafi sun yi imani, kuma sun kiyaye dokokin Allah, to lalle da Mun kankare musu zunubansu, kuma lalle da Mun shigar da su gidajen Aljanna na ni’ima
وَلَوۡ أَنَّهُمۡ أَقَامُواْ ٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِم مِّن رَّبِّهِمۡ لَأَكَلُواْ مِن فَوۡقِهِمۡ وَمِن تَحۡتِ أَرۡجُلِهِمۚ مِّنۡهُمۡ أُمَّةٞ مُّقۡتَصِدَةٞۖ وَكَثِيرٞ مِّنۡهُمۡ سَآءَ مَا يَعۡمَلُونَ
Kuma da a ce sun tsaya a kan aiki da Attaura da Linjila da kuma abin da aka saukar musu daga Ubangijinsu, lalle da sun ci daga samansu da kuma qarqashin qafafunsu. Daga cikinsu akwai wata al’umma madaidaiciya, (amma) kuma mafi yawa daga cikinsu, irin abin da suke aikatawa ya munana (matuqa)
قُلۡ يَـٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لَسۡتُمۡ عَلَىٰ شَيۡءٍ حَتَّىٰ تُقِيمُواْ ٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكُم مِّن رَّبِّكُمۡۗ وَلَيَزِيدَنَّ كَثِيرٗا مِّنۡهُم مَّآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ طُغۡيَٰنٗا وَكُفۡرٗاۖ فَلَا تَأۡسَ عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Ka ce: “Ya ku Ma’abota Littafi, ba kwa kan wani abu (na addinin gaskiya), har sai kun tsaya a kan yin aiki da Attaura da Linjila da kuma abin da aka saukar muku daga wajen Ubangijinku.” Kuma abin da ake saukar maka daga Ubangijinka tabbas yana qara wa yawancinsu shisshigi da kafirci. Don haka kada ka yi baqin ciki dangane da (abin da yake samun) mutane kafirai
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَٱلَّذِينَ هَادُواْ وَٱلصَّـٰبِـُٔونَ وَٱلنَّصَٰرَىٰ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ
Lalle waxanda suka yi imani da waxanda suke Yahudawa da Sabi’awa da Nasara, duk wanda ya yi imani da Allah da ranar qarshe, kuma ya yi aiki nagari, to babu jin tsoro a tattare da su, kuma ba za su yi baqin ciki ba
ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَعۡرِفُونَهُۥ كَمَا يَعۡرِفُونَ أَبۡنَآءَهُمُۘ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ فَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ
Waxanda Muka ba su Littafi sun san shi kamar yadda suka san ‘ya’yansu. Waxanda suka yi hasarar kawunansu, to su kam ba za su tava yin imani ba
فَخَلَفَ مِنۢ بَعۡدِهِمۡ خَلۡفٞ وَرِثُواْ ٱلۡكِتَٰبَ يَأۡخُذُونَ عَرَضَ هَٰذَا ٱلۡأَدۡنَىٰ وَيَقُولُونَ سَيُغۡفَرُ لَنَا وَإِن يَأۡتِهِمۡ عَرَضٞ مِّثۡلُهُۥ يَأۡخُذُوهُۚ أَلَمۡ يُؤۡخَذۡ عَلَيۡهِم مِّيثَٰقُ ٱلۡكِتَٰبِ أَن لَّا يَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡحَقَّ وَدَرَسُواْ مَا فِيهِۗ وَٱلدَّارُ ٱلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ يَتَّقُونَۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ
Sai waxansu bara-gurbi suka maye bayansu, sun gaji littafin (Attaura), suna karvar abin duniya, suna kuma cewa: “Za a gafarta mana.” Kuma idan wani abin duniyar irinsa ya zo musu sai su sake karvar sa. Shin yanzu ba a xauki alqawari daga wurinsu ba a cikin littafin (Attaura) cewa, kada su faxi wata magana game da Allah sai gaskiya, kuma sun karanta abin da yake cikinsa? Kuma lalle gidan lahira shi ne mafi alheri ga dukkan waxanda suke da taqawa. Shin ba za ku hankalta ba?
وَٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَفۡرَحُونَ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَۖ وَمِنَ ٱلۡأَحۡزَابِ مَن يُنكِرُ بَعۡضَهُۥۚ قُلۡ إِنَّمَآ أُمِرۡتُ أَنۡ أَعۡبُدَ ٱللَّهَ وَلَآ أُشۡرِكَ بِهِۦٓۚ إِلَيۡهِ أَدۡعُواْ وَإِلَيۡهِ مَـَٔابِ
Waxanda kuwa Muka bai wa littafi (muminansu) suna farin ciki da abin da aka saukar maka; akwai kuma wasu daga qungiyoyi waxanda suke musun wani sashi nasa. Ka ce: “Ni dai an umarce ni ne kawai da in bauta wa Allah, kada kuma in tara wani abu da Shi. Kuma zuwa gare Shi kawai nake kira, wurinsa ne kawai kuma makomata.”
ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلِهِۦ هُم بِهِۦ يُؤۡمِنُونَ
Waxanda Muka bai wa littafi a gabaninsa (Alqur’ani) (suka tsaya a kansa) su suna yin imani da shi (Alqur’ani)
وَإِذَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِهِۦٓ إِنَّهُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّنَآ إِنَّا كُنَّا مِن قَبۡلِهِۦ مُسۡلِمِينَ
Idan kuma ana karanta musu (Alqur’anin) sai su ce: “Mun yi imani da shi, lalle shi gaskiya ne daga Ubangijinmu, lalle mu mun kasance Musulmi tun gabaninsa.”
أُوْلَـٰٓئِكَ يُؤۡتَوۡنَ أَجۡرَهُم مَّرَّتَيۡنِ بِمَا صَبَرُواْ وَيَدۡرَءُونَ بِٱلۡحَسَنَةِ ٱلسَّيِّئَةَ وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ
Waxannan (su ne) za a ba su ladansu ninki biyu saboda haqurin da suka yi. Kuma suna kawar da mummunan aiki da kyakkyawa, suna kuma ciyarwa daga abin da Muka arzuta su (da shi)
۞وَلَا تُجَٰدِلُوٓاْ أَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ إِلَّا بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ إِلَّا ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنۡهُمۡۖ وَقُولُوٓاْ ءَامَنَّا بِٱلَّذِيٓ أُنزِلَ إِلَيۡنَا وَأُنزِلَ إِلَيۡكُمۡ وَإِلَٰهُنَا وَإِلَٰهُكُمۡ وَٰحِدٞ وَنَحۡنُ لَهُۥ مُسۡلِمُونَ
Kuma kada ku yi jayayya da ma’abota littafi (Yahudu da Nasara) sai ta hanyar da ta fi kyau, sai dai waxanda suka yi zalunci daga cikinsu; kuma ku ce: “Mun yi imani da abin da aka saukar mana da kuma abin da aka saukar muku, kuma Abin bautarmu da Abin bautarku Xaya ne, kuma mu masu miqa wuya ne gare Shi.”
۞أَلَمۡ يَأۡنِ لِلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَن تَخۡشَعَ قُلُوبُهُمۡ لِذِكۡرِ ٱللَّهِ وَمَا نَزَلَ مِنَ ٱلۡحَقِّ وَلَا يَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلُ فَطَالَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡأَمَدُ فَقَسَتۡ قُلُوبُهُمۡۖ وَكَثِيرٞ مِّنۡهُمۡ فَٰسِقُونَ
Yanzu lokaci bai yi ba ga waxanda suka yi imani zukatansu su yi taushi da zikirin Allah da kuma abin da Ya saukar na gaskiya, kuma kada su zama kamar waxanda aka bai wa Littafi tun gabaninsu, sai lokaci ya tsawaita a gare su, sai zukatansu suka qeqashe; mafiya yawa kuma daga cikinsu fasiqai ne?
لِّئَلَّا يَعۡلَمَ أَهۡلُ ٱلۡكِتَٰبِ أَلَّا يَقۡدِرُونَ عَلَىٰ شَيۡءٖ مِّن فَضۡلِ ٱللَّهِ وَأَنَّ ٱلۡفَضۡلَ بِيَدِ ٱللَّهِ يُؤۡتِيهِ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ
Don ma’abota littafi su san cewa ba su da hannu a falalar Allah, don ko lalle falala a hannun Allah take, Yana ba da ita ga wanda Ya ga dama. Allah kuma Ma’abocin babbar falala ne
وَمَا جَعَلۡنَآ أَصۡحَٰبَ ٱلنَّارِ إِلَّا مَلَـٰٓئِكَةٗۖ وَمَا جَعَلۡنَا عِدَّتَهُمۡ إِلَّا فِتۡنَةٗ لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ لِيَسۡتَيۡقِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَيَزۡدَادَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِيمَٰنٗا وَلَا يَرۡتَابَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَلِيَقُولَ ٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ وَٱلۡكَٰفِرُونَ مَاذَآ أَرَادَ ٱللَّهُ بِهَٰذَا مَثَلٗاۚ كَذَٰلِكَ يُضِلُّ ٱللَّهُ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُۚ وَمَا يَعۡلَمُ جُنُودَ رَبِّكَ إِلَّا هُوَۚ وَمَا هِيَ إِلَّا ذِكۡرَىٰ لِلۡبَشَرِ
Ba Mu kuwa sanya masu tsaron wutar ba sai mala’iku, ba Mu kuma sanya adadinsu ba sai don fitina ga waxanda suka kafirta, don kuma waxanda aka bai wa littafi su sami yaqini, waxanda kuma suka yi imani su qara imani, waxanda aka bai wa littafi da muminai kuma kada su yi tababa, don kuma waxanda suke da raunin imani a zukatansu da kuma kafirai su ce: “Me Allah Yake nufi da yin misali da wannan (adadin)?” Kamar haka Allah Yake vatar da wanda Ya ga dama, Yake kuma shiryar da wanda Ya ga dama. Ba kuma wanda ya san (yawan) rundunar Ubangijinka sai Shi. Ita (Saqara) kuma ba wata abu ba ce face wa’azi ga mutane
لَمۡ يَكُنِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ وَٱلۡمُشۡرِكِينَ مُنفَكِّينَ حَتَّىٰ تَأۡتِيَهُمُ ٱلۡبَيِّنَةُ
Waxanda suka kafirta daga ma’abota littafi da mushirikai ba su zamanto masu barin abin da suke kai (na kafirci) ba har sai hujja bayyananniya ta zo musu
رَسُولٞ مِّنَ ٱللَّهِ يَتۡلُواْ صُحُفٗا مُّطَهَّرَةٗ
(Watau) Manzo daga Allah da zai riqa karanta (musu) takardu masu tsarki
فِيهَا كُتُبٞ قَيِّمَةٞ
(Waxanda) a cikinsu akwai hukunce-hukunce masu qima
وَمَا تَفَرَّقَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡبَيِّنَةُ
Waxanda kuma aka bai wa littafi ba su rarraba ba[1] sai bayan da hujja bayyananniya ta zo musu
1- Watau Yahudawa da Nasara ba su rarrabu ba suka zama qungiya-qungiya wasu suka yi imani da Manzo Allah (), wasu kuma suka kafirce.
وَمَآ أُمِرُوٓاْ إِلَّا لِيَعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ حُنَفَآءَ وَيُقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُواْ ٱلزَّكَوٰةَۚ وَذَٰلِكَ دِينُ ٱلۡقَيِّمَةِ
Ba a kuma umarce su ba sai don su bauta wa Allah suna masu tsantsanta addini gare Shi, suna masu kauce wa varna, suna kuma tsayar da salla, kuma suna ba da zakka. Wannan kuwa shi ne addinin miqaqqiyar hanya