السورة: Suratus Shu’ara

الآية : 156

وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوٓءٖ فَيَأۡخُذَكُمۡ عَذَابُ يَوۡمٍ عَظِيمٖ

“Kada kuwa ku shafe ta da mugun abu, sai azabar wani yini mai girma ta kama ku.”



السورة: Suratus Shu’ara

الآية : 157

فَعَقَرُوهَا فَأَصۡبَحُواْ نَٰدِمِينَ

Sai suka soke ta, sai kuwa suka wayi gari suna masu nadama



السورة: Suratus Shu’ara

الآية : 158

فَأَخَذَهُمُ ٱلۡعَذَابُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ

Sai azaba ta kama su. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu ba su zamanto muminai ba



السورة: Suratus Shu’ara

الآية : 159

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Kuma lalle Ubangijinka tabbas Shi ne Mabuwayi, Mai jin qai



السورة: Suratun Namli

الآية : 45

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَآ إِلَىٰ ثَمُودَ أَخَاهُمۡ صَٰلِحًا أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ فَإِذَا هُمۡ فَرِيقَانِ يَخۡتَصِمُونَ

Haqiqa kuma Mun aiko wa Samudawa xan’uwansu Salihu da cewa: “Ku bauta wa Allah,” sai ga su sun rabu qungiyoyi biyu[1] suna jayayya


1- Watau qungiya ta farko su ne waxanda suka yi imani da Annabi Salihu, qungiya ta biyu su ne waxanda suka kafirce masa.


السورة: Suratun Namli

الآية : 46

قَالَ يَٰقَوۡمِ لِمَ تَسۡتَعۡجِلُونَ بِٱلسَّيِّئَةِ قَبۡلَ ٱلۡحَسَنَةِۖ لَوۡلَا تَسۡتَغۡفِرُونَ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ

Ya ce: “Ya ku mutanena, don me kuke neman gaggautowar mummunan sakamako tun gabanin kyakkyawa[1]? Don me ba za ku nemi gafarar Allah ba don a ji qan ku.”


1- Watau suna neman a kawo musu azaba, maimakon su roqi rahamar Allah.


السورة: Suratun Namli

الآية : 47

قَالُواْ ٱطَّيَّرۡنَا بِكَ وَبِمَن مَّعَكَۚ قَالَ طَـٰٓئِرُكُمۡ عِندَ ٱللَّهِۖ بَلۡ أَنتُمۡ قَوۡمٞ تُفۡتَنُونَ

Sai suka ce: “Mu mun camfa ka kai da waxanda suke tare da kai.” Sai ya ce: “Camfinku na ga Allah. A’a, ku dai mutane ne da ake jarraba ku.”



السورة: Suratun Namli

الآية : 48

وَكَانَ فِي ٱلۡمَدِينَةِ تِسۡعَةُ رَهۡطٖ يُفۡسِدُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا يُصۡلِحُونَ

A cikin birnin kuma akwai wani gungu na mutum tara waxanda suke varna a bayan qasa kuma ba sa gyara



السورة: Suratun Namli

الآية : 49

قَالُواْ تَقَاسَمُواْ بِٱللَّهِ لَنُبَيِّتَنَّهُۥ وَأَهۡلَهُۥ ثُمَّ لَنَقُولَنَّ لِوَلِيِّهِۦ مَا شَهِدۡنَا مَهۡلِكَ أَهۡلِهِۦ وَإِنَّا لَصَٰدِقُونَ

Sai suka ce wa (juna): “Ku rantse da Allah cewa, lalle za mu kashe shi cikin dare shi da iyalinsa, sannan za mu faxa wa mai neman jininsa cewa, ba mu halarci wurin kashe iyalinsa ba, kuma lalle mu masu gaskiya ne.”



السورة: Suratun Namli

الآية : 50

وَمَكَرُواْ مَكۡرٗا وَمَكَرۡنَا مَكۡرٗا وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ

Kuma suka shirya makirci, Mu kuma Muka shirya rusa makircinsu alhali kuwa su ba su sani ba



السورة: Suratun Namli

الآية : 51

فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ مَكۡرِهِمۡ أَنَّا دَمَّرۡنَٰهُمۡ وَقَوۡمَهُمۡ أَجۡمَعِينَ

Sai ka duba ka ga yadda qarshen makircinsu ya zama, watau Mun hallakar da su tare da mutanensu baki xaya



السورة: Suratun Namli

الآية : 52

فَتِلۡكَ بُيُوتُهُمۡ خَاوِيَةَۢ بِمَا ظَلَمُوٓاْۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ

To ga gidajensu can a rugurguje babu kowa saboda zaluncinsu. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya ga mutanen da suke ganewa



السورة: Suratun Namli

الآية : 53

وَأَنجَيۡنَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَكَانُواْ يَتَّقُونَ

Muka kuma tserar da waxanda suka yi imani, suka kuma kasance suna kiyaye dokokin Allah



السورة: Suratus Shams

الآية : 13

فَقَالَ لَهُمۡ رَسُولُ ٱللَّهِ نَاقَةَ ٱللَّهِ وَسُقۡيَٰهَا

Sai Manzon Allah[1] ya ce da su: “Ku bar taguwar Allah da (ranar) shanta.”


1- Watau Annabi Salihu ().