لَمَجۡمُوعُونَ إِلَىٰ مِيقَٰتِ يَوۡمٖ مَّعۡلُومٖ
“Tabbas za a tattara su zuwa wani lokaci na rana sananniya
زَعَمَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَن لَّن يُبۡعَثُواْۚ قُلۡ بَلَىٰ وَرَبِّي لَتُبۡعَثُنَّ ثُمَّ لَتُنَبَّؤُنَّ بِمَا عَمِلۡتُمۡۚ وَذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ
Waxanda suka kafirta sun riya cewa ba za a tashe su ba har abada. Ka ce: “A’a, na rantse da Ubangijina tabbas za a tashe ku, sannan kuma tabbas za a ba ku labarin abin da kuka aikata. Wannan kuwa mai sauqi ne a wurin Allah
هُوَ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ ذَلُولٗا فَٱمۡشُواْ فِي مَنَاكِبِهَا وَكُلُواْ مِن رِّزۡقِهِۦۖ وَإِلَيۡهِ ٱلنُّشُورُ
Shi ne wanda Ya sanya muku qasa horarriya[1], saboda haka ku yi tafiya a cikin sasanninta kuma ku ci daga arzikinta; makoma kuwa zuwa gare Shi take
1- Watau ta zamanto mai sauqin zama da rayuwa a kanta, ba tare da tana tangal-tangal da su ba.