السورة: Suratuz Zariyat

الآية : 39

فَتَوَلَّىٰ بِرُكۡنِهِۦ وَقَالَ سَٰحِرٌ أَوۡ مَجۡنُونٞ

Sai ya ba da baya shi da qarfin rundunarsa, ya kuma ce: “(Musa) mai sihiri ne ko mahaukaci.”



السورة: Suratuz Zariyat

الآية : 40

فَأَخَذۡنَٰهُ وَجُنُودَهُۥ فَنَبَذۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡيَمِّ وَهُوَ مُلِيمٞ

Saboda haka Muka kama shi tare da rundunarsa, sai Muka watsa su a cikin kogi, alhali yana mai aikata abin Allah-wadai



السورة: Suratul Qamar

الآية : 41

وَلَقَدۡ جَآءَ ءَالَ فِرۡعَوۡنَ ٱلنُّذُرُ

Kuma haqiqa gargaxi ya zo wa mutanen Fir’auna



السورة: Suratul Qamar

الآية : 42

كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا كُلِّهَا فَأَخَذۡنَٰهُمۡ أَخۡذَ عَزِيزٖ مُّقۡتَدِرٍ

Suka qaryata ayoyinmu dukkaninsu, sai Muka kama su irin kamu na Mabuwayi, Mai iko



السورة: Suratut Tahrim

الآية : 11

وَضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱمۡرَأَتَ فِرۡعَوۡنَ إِذۡ قَالَتۡ رَبِّ ٱبۡنِ لِي عِندَكَ بَيۡتٗا فِي ٱلۡجَنَّةِ وَنَجِّنِي مِن فِرۡعَوۡنَ وَعَمَلِهِۦ وَنَجِّنِي مِنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Allah kuma Ya ba da wani misali ga waxanda suka yi imani da matar Fir’auna lokacin da ta ce: “Ya Ubangijina, Ka gina min gida a wurinka cikin Aljanna, Ka kuma tserar da ni daga Fir’auna da aikinsa, kuma Ka tserar da ni daga azzaluman mutane.”



السورة: Suratul Muzzammil

الآية : 15

إِنَّآ أَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡكُمۡ رَسُولٗا شَٰهِدًا عَلَيۡكُمۡ كَمَآ أَرۡسَلۡنَآ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ رَسُولٗا

Lalle Mu Muka aiko muku da Manzo yana mai shaida a kanku kamar yadda Muka aiko wani manzo zuwa ga Fir’auna



السورة: Suratul Muzzammil

الآية : 16

فَعَصَىٰ فِرۡعَوۡنُ ٱلرَّسُولَ فَأَخَذۡنَٰهُ أَخۡذٗا وَبِيلٗا

Sai Fir’auna ya sava wa Manzon, sai Muka kama shi kamu mai tsanani



السورة: Suratun Nazi’at

الآية : 17

ٱذۡهَبۡ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ

(Aka ce da shi): Ka tafi zuwa ga Fir’auna, haqiqa shi ya yi xagawa



السورة: Suratun Nazi’at

الآية : 18

فَقُلۡ هَل لَّكَ إِلَىٰٓ أَن تَزَكَّىٰ

Sai ka ce: “Shin zai yiwu gare ka kuwa ka tsarkaka?



السورة: Suratun Nazi’at

الآية : 19

وَأَهۡدِيَكَ إِلَىٰ رَبِّكَ فَتَخۡشَىٰ

“In kuma shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka, sai ka ji tsoron Sa?



السورة: Suratun Nazi’at

الآية : 20

فَأَرَىٰهُ ٱلۡأٓيَةَ ٱلۡكُبۡرَىٰ

Sai ya nuna masa babbar aya[1]


1- Watau ya nuna masa hannun mai haske kamar fitila da kuma sandarsa mai rikixa ta zama macijiya.


السورة: Suratun Nazi’at

الآية : 21

فَكَذَّبَ وَعَصَىٰ

Sai ya qaryata ya kuma kangare



السورة: Suratun Nazi’at

الآية : 22

ثُمَّ أَدۡبَرَ يَسۡعَىٰ

Sannan ya ba da baya yana ta gaggawa



السورة: Suratun Nazi’at

الآية : 23

فَحَشَرَ فَنَادَىٰ

Sai ya tattara (jama’arsa) sai ya yi shela



السورة: Suratun Nazi’at

الآية : 24

فَقَالَ أَنَا۠ رَبُّكُمُ ٱلۡأَعۡلَىٰ

Sai ya ce, “Ni ne ubangijinku mafi girma!”



السورة: Suratun Nazi’at

الآية : 25

فَأَخَذَهُ ٱللَّهُ نَكَالَ ٱلۡأٓخِرَةِ وَٱلۡأُولَىٰٓ

Saboda haka Allah Ya kama shi da azabar lahira (watau Jahannama) da ta duniya (watau nutse wa a ruwa)



السورة: Suratun Nazi’at

الآية : 26

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَعِبۡرَةٗ لِّمَن يَخۡشَىٰٓ

Lalle a game da wannan tabbas akwai izina ga wanda yake tsoron (Allah)



السورة: Suratul Fajr

الآية : 10

وَفِرۡعَوۡنَ ذِي ٱلۡأَوۡتَادِ

Da kuma Fir’auna ma’abocin turaku



السورة: Suratul Fajr

الآية : 11

ٱلَّذِينَ طَغَوۡاْ فِي ٱلۡبِلَٰدِ

Waxanda suka yi xagawa a cikin garuruwa



السورة: Suratul Fajr

الآية : 12

فَأَكۡثَرُواْ فِيهَا ٱلۡفَسَادَ

Suka kuma yawaita varna a cikinsu



السورة: Suratul Fajr

الآية : 13

فَصَبَّ عَلَيۡهِمۡ رَبُّكَ سَوۡطَ عَذَابٍ

Sai Ubangijinka Ya saukar musu azaba mai tsanani