فَسَتَذۡكُرُونَ مَآ أَقُولُ لَكُمۡۚ وَأُفَوِّضُ أَمۡرِيٓ إِلَى ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ بَصِيرُۢ بِٱلۡعِبَادِ
“To ba da daxewa ba za ku tuna abin da nake gaya muku. Ina kuma miqa al’amarina zuwa ga Allah. Lalle Allah Mai ganin bayi ne.”
فَوَقَىٰهُ ٱللَّهُ سَيِّـَٔاتِ مَا مَكَرُواْۖ وَحَاقَ بِـَٔالِ فِرۡعَوۡنَ سُوٓءُ ٱلۡعَذَابِ
Sai Allah Ya kiyaye shi (sakamakon) mummunan abin da suka shirya; kuma mummunar azaba ta saukar wa mutanen Fir’auna
ٱلنَّارُ يُعۡرَضُونَ عَلَيۡهَا غُدُوّٗا وَعَشِيّٗاۚ وَيَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ أَدۡخِلُوٓاْ ءَالَ فِرۡعَوۡنَ أَشَدَّ ٱلۡعَذَابِ
(Ita ce) wuta da za a riqa bijirar da su a gare ta safe da yamma; Ranar tashin alqiyama kuma za a ce: “Ku shigar da mutanen Fir’auna mafi tsananin azaba
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَآ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ فَقَالَ إِنِّي رَسُولُ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Haqiqa kuma Mun aiko Musa da ayoyinmu zuwa ga Fir’auna da manyan fadawansa, sai ya ce: “Lalle ni Manzo ne na Ubangijin talikai.”
فَلَمَّا جَآءَهُم بِـَٔايَٰتِنَآ إِذَا هُم مِّنۡهَا يَضۡحَكُونَ
To lokacin da ya zo musu da ayoyinmu sai ga su suna yi musu dariya
وَمَا نُرِيهِم مِّنۡ ءَايَةٍ إِلَّا هِيَ أَكۡبَرُ مِنۡ أُخۡتِهَاۖ وَأَخَذۡنَٰهُم بِٱلۡعَذَابِ لَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ
Ba Mu kuma nuna musu wata aya ba sai wadda take ta fi `yar’uwarta girma; Muka kuma kama su da azaba don su dawo (kan hanya)
وَقَالُواْ يَـٰٓأَيُّهَ ٱلسَّاحِرُ ٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ بِمَا عَهِدَ عِندَكَ إِنَّنَا لَمُهۡتَدُونَ
Suka kuma ce: “Ya kai wannan mai sihiri, ka roqa mana Ubangijinka da abin da Ya yi maka wahayinsa (Ya yaye mana azaba), lalle mu tabbas za mu shiriya.”
فَلَمَّا كَشَفۡنَا عَنۡهُمُ ٱلۡعَذَابَ إِذَا هُمۡ يَنكُثُونَ
To lokacin da Muka yaye musu azabar sai ga su suna warware alqawari
وَنَادَىٰ فِرۡعَوۡنُ فِي قَوۡمِهِۦ قَالَ يَٰقَوۡمِ أَلَيۡسَ لِي مُلۡكُ مِصۡرَ وَهَٰذِهِ ٱلۡأَنۡهَٰرُ تَجۡرِي مِن تَحۡتِيٓۚ أَفَلَا تُبۡصِرُونَ
Fir’auna kuma ya yi shela a cikin mutanensa ya ce: “Ya ku mutanena, yanzu mulkin Misra ba nawa ba ne, kuma ga qoramu suna ta kwarara ta qarqashina, ko ba kwa gani ne?
أَمۡ أَنَا۠ خَيۡرٞ مِّنۡ هَٰذَا ٱلَّذِي هُوَ مَهِينٞ وَلَا يَكَادُ يُبِينُ
“A’a, ni na fi wannan wulaqantaccen wanda da qyar yake iya bayani
فَلَوۡلَآ أُلۡقِيَ عَلَيۡهِ أَسۡوِرَةٞ مِّن ذَهَبٍ أَوۡ جَآءَ مَعَهُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ مُقۡتَرِنِينَ
“To me ya hana a saukar masa da warawarai na zinare, ko kuma wasu mala’iku su zo tare da shi suna masu dafa masa baya?”
فَٱسۡتَخَفَّ قَوۡمَهُۥ فَأَطَاعُوهُۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَوۡمٗا فَٰسِقِينَ
Sai ya yi wasa da hankalin mutanensa sai suka bi shi. Lalle su sun kasance mutane ne fasiqai
فَلَمَّآ ءَاسَفُونَا ٱنتَقَمۡنَا مِنۡهُمۡ فَأَغۡرَقۡنَٰهُمۡ أَجۡمَعِينَ
To lokacin da suka fusata Mu sai Muka saukar musu da uquba, Muka nutsar da su ga baki xaya
فَجَعَلۡنَٰهُمۡ سَلَفٗا وَمَثَلٗا لِّلۡأٓخِرِينَ
Sai Muka sanya su ja-gaba (wajen hallakarwa), kuma wa’azi ga na baya
۞وَلَقَدۡ فَتَنَّا قَبۡلَهُمۡ قَوۡمَ فِرۡعَوۡنَ وَجَآءَهُمۡ رَسُولٞ كَرِيمٌ
Haqiqa kuma Mun jarrabi mutanen Fir’auna tun kafin su, kuma Manzo mai karamci ya zo musu
أَنۡ أَدُّوٓاْ إِلَيَّ عِبَادَ ٱللَّهِۖ إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ
(Da cewa): “Ku ba ni bayin Allah (watau Banu Isra’ila); lalle ni Manzo ne amintacce a gare ku
وَأَن لَّا تَعۡلُواْ عَلَى ٱللَّهِۖ إِنِّيٓ ءَاتِيكُم بِسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٖ
“Kuma kada ku yi wa Allah girman kai; lalle ni zan kawo muku hujjoji mabayyana
وَإِنِّي عُذۡتُ بِرَبِّي وَرَبِّكُمۡ أَن تَرۡجُمُونِ
“Kuma lalle ni ina neman tsari na Ubangijina kuma Ubangijinku, don kada ku jefe ni
وَإِن لَّمۡ تُؤۡمِنُواْ لِي فَٱعۡتَزِلُونِ
“Idan kuma ba ku yi imani da ni ba sai ku qyale ni.”
فَدَعَا رَبَّهُۥٓ أَنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ قَوۡمٞ مُّجۡرِمُونَ
Sai ya roqi Ubangijinsa cewa: “Lalle waxannan mutane ne masu manyan laifuka.”
فَأَسۡرِ بِعِبَادِي لَيۡلًا إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ
Sai (aka ce masa): “Ka tafi da bayina da daddare, lalle ku za a biyo bayanku
وَٱتۡرُكِ ٱلۡبَحۡرَ رَهۡوًاۖ إِنَّهُمۡ جُندٞ مُّغۡرَقُونَ
“Kuma ka bar kogi a tsaye cak (bayan tsallakewa); lalle su runduna ne da za a nutsar.”
كَمۡ تَرَكُواْ مِن جَنَّـٰتٖ وَعُيُونٖ
Sun bar gonaki da kuma idanuwan ruwa masu yawa
وَزُرُوعٖ وَمَقَامٖ كَرِيمٖ
Da kuma shuke-shuke da wurin zama mai daraja
وَنَعۡمَةٖ كَانُواْ فِيهَا فَٰكِهِينَ
Da kuma kayan jin daxi da suka kasance masu ni’imtuwa da su
كَذَٰلِكَۖ وَأَوۡرَثۡنَٰهَا قَوۡمًا ءَاخَرِينَ
Kamar haka ne; sai Muka kuma gadar da su ga wasu mutane daban (su ne Banu Isra’ila)
فَمَا بَكَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلسَّمَآءُ وَٱلۡأَرۡضُ وَمَا كَانُواْ مُنظَرِينَ
Sannan (halittun) sama da na qasa ba su yi alhininsu ba, ba su kuma kasance ababen saurara wa ba
وَلَقَدۡ نَجَّيۡنَا بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ مِنَ ٱلۡعَذَابِ ٱلۡمُهِينِ
Haqiqa kuma Mun tserar da Banu Isra’ila daga azabar wulaqanci
مِن فِرۡعَوۡنَۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَالِيٗا مِّنَ ٱلۡمُسۡرِفِينَ
Daga Fir’auna. Lalle shi ya kasance mai girman kai daga mavarnata
وَفِي مُوسَىٰٓ إِذۡ أَرۡسَلۡنَٰهُ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ بِسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٖ
Game da Musa kuma (akwai aya), lokacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir’auna da hujjoji bayyanannu