قُلۡ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَۖ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Ka ce: “Ku yi xa’a ga Allah da Manzo; to in kuwa kuka juya baya, to lalle Allah ba Ya son kafirai.”
وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ
Kuma ku bi Allah da Manzo don a ji qan ku (a ranar tashin alqiyama)
تِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِۚ وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ يُدۡخِلۡهُ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ وَذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
Waxannan iyakoki ne na Allah. Wanda duk yake bin Allah da Manzonsa, to zai shigar da shi gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinsu. Kuma wannan shi ne rabo mai girma
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَأُوْلِي ٱلۡأَمۡرِ مِنكُمۡۖ فَإِن تَنَٰزَعۡتُمۡ فِي شَيۡءٖ فَرُدُّوهُ إِلَى ٱللَّهِ وَٱلرَّسُولِ إِن كُنتُمۡ تُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ وَأَحۡسَنُ تَأۡوِيلًا
Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi xa’a ga Allah, kuma ku yi xa’a ga Manzo da kuma majivinta lamarinku. Idan kun yi jayayya a kan wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzonsa in kun kasance kun yi imani da Allah da ranar qarshe. Wannan shi ne mafi alheri, kuma mafi kyan makoma
وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَ فَأُوْلَـٰٓئِكَ مَعَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ وَٱلصِّدِّيقِينَ وَٱلشُّهَدَآءِ وَٱلصَّـٰلِحِينَۚ وَحَسُنَ أُوْلَـٰٓئِكَ رَفِيقٗا
Kuma duk waxanda suka yi wa Allah xa’a da wannan Manzon, to waxannan suna tare da waxanda Allah Ya yi musu ni’ima, su ne annabawa da siddiqai da shahidai da salihan bayi. Kuma madalla da waxannan abokai
مَّن يُطِعِ ٱلرَّسُولَ فَقَدۡ أَطَاعَ ٱللَّهَۖ وَمَن تَوَلَّىٰ فَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ عَلَيۡهِمۡ حَفِيظٗا
Duk wanda ya yi wa wannan Manzo xa’a, to haqiqa ya yi wa Allah xa’a ne; wanda kuwa ya bijire, to ba Mu aiko ka a matsayin mai tsaron su ba
وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَٱحۡذَرُواْۚ فَإِن تَوَلَّيۡتُمۡ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَا عَلَىٰ رَسُولِنَا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ
Kuma ku bi Allah, kuma ku bi wannan Manzon, kuma ku yi hattara. Idan kuka juya baya, to ku sani abin da kawai yake kan Manzonmu shi ne isar da saqo filla-filla
يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡأَنفَالِۖ قُلِ ٱلۡأَنفَالُ لِلَّهِ وَٱلرَّسُولِۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَصۡلِحُواْ ذَاتَ بَيۡنِكُمۡۖ وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ
Suna tambayar ka game da ganimomi[1]; ka ce (da su): “Ganimomi na Allah ne da kuma Manzo; saboda haka ku kiyaye dokokin Allah, ku kuma gyara tsakaninku, kuma ku bi Allah da Manzonsa, idan kun kasance muminai.”
1- Watau tambayar da sahabbai suka yi wa Annabi () game da hukuncin ganimar yaqin Badar.
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَلَا تَوَلَّوۡاْ عَنۡهُ وَأَنتُمۡ تَسۡمَعُونَ
Ya ku waxanda suka yi imani, ku bi Allah da Manzonsa kada kuma ku ba shi baya alhali kuwa kuna ji
وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَلَا تَنَٰزَعُواْ فَتَفۡشَلُواْ وَتَذۡهَبَ رِيحُكُمۡۖ وَٱصۡبِرُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلصَّـٰبِرِينَ
Kuma ku bi Allah da Manzonsa, kada ku rarrabu sai ku zama matsorata kuma qarfinku ya tafi; ku kuma yi haquri. Lalle Allah Yana tare da masu haquri
وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتُ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلِيَآءُ بَعۡضٖۚ يَأۡمُرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَيُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَيُطِيعُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓۚ أُوْلَـٰٓئِكَ سَيَرۡحَمُهُمُ ٱللَّهُۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٞ
Muminai maza da muninai mata kuwa masoyan juna ne: Suna yin umurni da kyakkyawan abu suna kuma hana mummunan, suna kuma tsai da salla suna ba da zakka suna kuma bin Allah da Manzonsa. Waxannan Allah zai yi musu rahama. Lalle Allah kuwa Mabuwayi ne Mai hikima
إِنَّمَا كَانَ قَوۡلَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ إِذَا دُعُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ لِيَحۡكُمَ بَيۡنَهُمۡ أَن يَقُولُواْ سَمِعۡنَا وَأَطَعۡنَاۚ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ
Muminai ba su da wata magana idan aka kira su zuwa ga Allah da Manzonsa don ya yi hukunci a tsakaninsu sai faxar: “Mun ji kuma mun bi.” Waxannan kuwa su ne masu babban rabo
وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَيَخۡشَ ٱللَّهَ وَيَتَّقۡهِ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَآئِزُونَ
Duk kuwa wanda ya bi Allah da Manzonsa kuma yake tsoron Allah kuma yake kiyaye dokokinsa, to waxannan su ne masu rabauta
قُلۡ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَۖ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّمَا عَلَيۡهِ مَا حُمِّلَ وَعَلَيۡكُم مَّا حُمِّلۡتُمۡۖ وَإِن تُطِيعُوهُ تَهۡتَدُواْۚ وَمَا عَلَى ٱلرَّسُولِ إِلَّا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ
Ka ce (da su): “Ku bi Allah kuma ku bi Manzo; sannan idan kuka ba da baya, to lalle nauyin abin da aka xora masa ne kawai a kansa; kuma nauyin da aka xora muku yana kanku, idan kuwa kuka bi shi za ku shiriya. Ba kuwa abin da yake kan Manzo sai isar da aike mabayyani
وَقَرۡنَ فِي بُيُوتِكُنَّ وَلَا تَبَرَّجۡنَ تَبَرُّجَ ٱلۡجَٰهِلِيَّةِ ٱلۡأُولَىٰۖ وَأَقِمۡنَ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتِينَ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَطِعۡنَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓۚ إِنَّمَا يُرِيدُ ٱللَّهُ لِيُذۡهِبَ عَنكُمُ ٱلرِّجۡسَ أَهۡلَ ٱلۡبَيۡتِ وَيُطَهِّرَكُمۡ تَطۡهِيرٗا
Ku kuma zauna a cikin gidajenku, kada kuma ku riqa fita (da bayyana ado) irin ta jahiliyyar farko; ku kuma tsayar da salla, ku ba da zakka, ku kuma bi Allah da Manzonsa. Abin da Allah Yake nufi kawai shi ne Ya kawar muku da duk wata qazanta, ya ku iyalin gidan Annabi, Ya kuma tsarkake ku tsarkakewa
يُصۡلِحۡ لَكُمۡ أَعۡمَٰلَكُمۡ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡ ذُنُوبَكُمۡۗ وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَقَدۡ فَازَ فَوۡزًا عَظِيمًا
Zai kyautata muku ayyukanku, Ya kuma gafarta muku zunubanku. Duk kuwa wanda ya bi Allah da Manzonsa, to haqiqa ya rabauta rabauta mai girma
۞يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَلَا تُبۡطِلُوٓاْ أَعۡمَٰلَكُمۡ
Ya ku waxanda suka yi imani, ku bi Allah, kuma ku bi Manzonsa, kada kuma ku vata ayyukanku[1]
1- Watau ta hanyar aikata kafirci ko munafurci ko riya.
لَّيۡسَ عَلَى ٱلۡأَعۡمَىٰ حَرَجٞ وَلَا عَلَى ٱلۡأَعۡرَجِ حَرَجٞ وَلَا عَلَى ٱلۡمَرِيضِ حَرَجٞۗ وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ يُدۡخِلۡهُ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ وَمَن يَتَوَلَّ يُعَذِّبۡهُ عَذَابًا أَلِيمٗا
Babu wani laifi a kan makaho, babu kuma wani laifi a kan gurgu, kuma babu wani laifi a kan marar lafiya (game da rashin fita yaqi). Wanda kuwa ya bi Allah da Manzonsa to zai shigar da shi gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, wanda kuma ya ba da baya to zai azabtar da shi azaba mai raxaxi
۞قَالَتِ ٱلۡأَعۡرَابُ ءَامَنَّاۖ قُل لَّمۡ تُؤۡمِنُواْ وَلَٰكِن قُولُوٓاْ أَسۡلَمۡنَا وَلَمَّا يَدۡخُلِ ٱلۡإِيمَٰنُ فِي قُلُوبِكُمۡۖ وَإِن تُطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ لَا يَلِتۡكُم مِّنۡ أَعۡمَٰلِكُمۡ شَيۡـًٔاۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ
(Larabawa) qauyawa suka ce: “Mun yi imani.” Ka ce: “Ba ku yi imani ba, sai dai ku ce ‘mun musulunta’, don kuwa imani bai riga ya shiga zukatanku ba; idan kuwa kuka bi Allah da Manzonsa, to ba zai tauye muku wani abu daga (ladan) ayyukanku ba. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai rahama.”
ءَأَشۡفَقۡتُمۡ أَن تُقَدِّمُواْ بَيۡنَ يَدَيۡ نَجۡوَىٰكُمۡ صَدَقَٰتٖۚ فَإِذۡ لَمۡ تَفۡعَلُواْ وَتَابَ ٱللَّهُ عَلَيۡكُمۡ فَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥۚ وَٱللَّهُ خَبِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ
Yanzu kun samu damuwa ne ta gabatar da sadaka kafin ganawarku? To idan ba ku aikata haka ba Allah kuma ya karvi tubarku, to sai ku tsayar da salla, ku ba da zakka, ku kuma bi Allah da Manzonsa. Allah kuma Masanin abin da kuke aikatawa ne
وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَۚ فَإِن تَوَلَّيۡتُمۡ فَإِنَّمَا عَلَىٰ رَسُولِنَا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ
Ku bi Allah kuma ku bi Manzon. To idan kuka ba da baya to abin da yake kan Manzonmu kawai shi ne isar da aike
فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ مَا ٱسۡتَطَعۡتُمۡ وَٱسۡمَعُواْ وَأَطِيعُواْ وَأَنفِقُواْ خَيۡرٗا لِّأَنفُسِكُمۡۗ وَمَن يُوقَ شُحَّ نَفۡسِهِۦ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ
Saboda haka ku kiyaye dokokin Allah gwargwadon ikonku, kuma ku yi sauraro, ku bi, ku kuma ciyar, shi ya fi alheri a gare ku. Duk kuwa wanda aka kare shi daga tsananin son kansa, to waxannan su ne masu babban rabo