إِنۡ أَنَا۠ إِلَّا نَذِيرٞ مُّبِينٞ
“Ni kawai mai gargaxi ne mai bayyanawa.”
قَالُواْ لَئِن لَّمۡ تَنتَهِ يَٰنُوحُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمَرۡجُومِينَ
Suka ce: “Ya Nuhu, mun rantse idan ba ka daina (faxar abin da kake faxa) ba, tabbas za ka zamanto daga cikin jefaffu!”
قَالَ رَبِّ إِنَّ قَوۡمِي كَذَّبُونِ
Ya ce: “Ya Ubangijina, lalle mutanena sun qaryata ni
فَٱفۡتَحۡ بَيۡنِي وَبَيۡنَهُمۡ فَتۡحٗا وَنَجِّنِي وَمَن مَّعِيَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
“Ka yi hukunci tsakanina da su, kuma Ka tserar da ni tare da muminan da suke tare da ni.”
فَأَنجَيۡنَٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ فِي ٱلۡفُلۡكِ ٱلۡمَشۡحُونِ
Sai Muka tserar da shi da waxanda suke tare da shi a cikin jirgin ruwan da ke maqare (da mutane da dabbobi)
ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا بَعۡدُ ٱلۡبَاقِينَ
Sannan bayan haka Muka nutsar da sauran
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu ba su zamanto muminai ba
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Kuma lalle Ubangijinka tabbas Shi ne Mabuwayi, Mai jin qai
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوۡمِهِۦ فَلَبِثَ فِيهِمۡ أَلۡفَ سَنَةٍ إِلَّا خَمۡسِينَ عَامٗا فَأَخَذَهُمُ ٱلطُّوفَانُ وَهُمۡ ظَٰلِمُونَ
Kuma haqiqa Mun aiko Nuhu zuwa ga mutanensa, sai ya zauna cikinsu shekara dubu ba hamsin, sai (ruwan) Xufana ya ci su, alhalin suna azzalumai
فَأَنجَيۡنَٰهُ وَأَصۡحَٰبَ ٱلسَّفِينَةِ وَجَعَلۡنَٰهَآ ءَايَةٗ لِّلۡعَٰلَمِينَ
Sai Muka tserar da shi tare da mutanen jirgin ruwa, Muka kuma sanya shi (jirgin) aya ga talikai
وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِنَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مِيثَٰقَهُمۡ وَمِنكَ وَمِن نُّوحٖ وَإِبۡرَٰهِيمَ وَمُوسَىٰ وَعِيسَى ٱبۡنِ مَرۡيَمَۖ وَأَخَذۡنَا مِنۡهُم مِّيثَٰقًا غَلِيظٗا
Kuma (ka tuna) lokacin da Muka riqi alqawura daga annabawa (na isar da aike), kuma daga gare ka, kuma daga Nuhu da Ibrahimu da Musa da Isa xan Maryamu; Muka kuma riqi alqawari mai kauri daga gare su
وَلَقَدۡ نَادَىٰنَا نُوحٞ فَلَنِعۡمَ ٱلۡمُجِيبُونَ
Kuma haqiqa Nuhu ya roqe Mu, to madalla da Masu amsawa
وَنَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥ مِنَ ٱلۡكَرۡبِ ٱلۡعَظِيمِ
Muka kuma tserar da shi tare da iyalinsa daga baqin ciki mai girma
وَجَعَلۡنَا ذُرِّيَّتَهُۥ هُمُ ٱلۡبَاقِينَ
Muka kuma sanya zuriyarsa su ne suka wanzu
وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ
Muka kuma bar (kyakkyawan yabo) a gare shi ga ‘yan baya
سَلَٰمٌ عَلَىٰ نُوحٖ فِي ٱلۡعَٰلَمِينَ
Aminci ya tabbata ga Nuhu a cikin talikai
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Lalle Mu kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa
إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Lalle shi yana daga bayinmu muminai
ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ
Sannan Muka nutsar da sauran
۞شَرَعَ لَكُم مِّنَ ٱلدِّينِ مَا وَصَّىٰ بِهِۦ نُوحٗا وَٱلَّذِيٓ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ وَمَا وَصَّيۡنَا بِهِۦٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَمُوسَىٰ وَعِيسَىٰٓۖ أَنۡ أَقِيمُواْ ٱلدِّينَ وَلَا تَتَفَرَّقُواْ فِيهِۚ كَبُرَ عَلَى ٱلۡمُشۡرِكِينَ مَا تَدۡعُوهُمۡ إِلَيۡهِۚ ٱللَّهُ يَجۡتَبِيٓ إِلَيۡهِ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِيٓ إِلَيۡهِ مَن يُنِيبُ
Ya shar’anta muku (irin) abin da Ya yi wa Nuhu wahayi da shi na addini, da kuma wanda Muka yiwo maka wahayinsa, da kuma abin da Muka yi wa Ibrahimu da Musa da Isa wasiyya da shi cewa: “Ku tsayar da addini, kuma kada ku rarraba a cikinsa.” Abin da kake kiran kafirai zuwa gare shi ya yi musu nauyi. Allah Yana zavar wanda Ya ga dama zuwa gare shi (addini) Yana kuma shiryar da wanda Ya mayar da al’amarinsa zuwa gare Shi
۞كَذَّبَتۡ قَبۡلَهُمۡ قَوۡمُ نُوحٖ فَكَذَّبُواْ عَبۡدَنَا وَقَالُواْ مَجۡنُونٞ وَٱزۡدُجِرَ
Mutanen Nuhu sun qaryata kafin su (Quraishawa), sai suka qaryata Bawanmu suka kuma ce, mahaukaci ne, aka kuma kyare (shi)
فَدَعَا رَبَّهُۥٓ أَنِّي مَغۡلُوبٞ فَٱنتَصِرۡ
Sai ya roqi Ubangijinsa (cewa): “Lalle an fi qarfina, sai Ka taimaka.”
فَفَتَحۡنَآ أَبۡوَٰبَ ٱلسَّمَآءِ بِمَآءٖ مُّنۡهَمِرٖ
Sai Muka buxe qofofin sama da ruwa mai kwararowa
وَفَجَّرۡنَا ٱلۡأَرۡضَ عُيُونٗا فَٱلۡتَقَى ٱلۡمَآءُ عَلَىٰٓ أَمۡرٖ قَدۡ قُدِرَ
Muka kuma vuvvugar da idanuwan ruwa daga qasa, sai ruwayen suka haxu a bisa al’amarin da aka riga aka qaddara
وَحَمَلۡنَٰهُ عَلَىٰ ذَاتِ أَلۡوَٰحٖ وَدُسُرٖ
Muka kuma xauke shi a kan (jirgin ruwa) mai alluna da qusoshi
تَجۡرِي بِأَعۡيُنِنَا جَزَآءٗ لِّمَن كَانَ كُفِرَ
Yana gudu a kan idonmu, don ya zama sakayya ga wanda aka kafirce wa (watau Nuhu)
وَلَقَد تَّرَكۡنَٰهَآ ءَايَةٗ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ
Haqiqa kuma Mun bar (abin da ya faru) ya zama aya, to ko akwai mai wa’azantuwa?
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا نُوحٗا وَإِبۡرَٰهِيمَ وَجَعَلۡنَا فِي ذُرِّيَّتِهِمَا ٱلنُّبُوَّةَ وَٱلۡكِتَٰبَۖ فَمِنۡهُم مُّهۡتَدٖۖ وَكَثِيرٞ مِّنۡهُمۡ فَٰسِقُونَ
Haqiqa kuma Mun aiko Nuhu da Ibrahimu, Muka kuma sanya annabta da littafi cikin zuriyarsu; To daga cikinsu akwai shiryayyu, masu yawa kuwa daga cikinsu fasiqai ne
إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوۡمِهِۦٓ أَنۡ أَنذِرۡ قَوۡمَكَ مِن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ
Lalle Mu Mun aika Nuhu zuwa ga mutanensa cewa: “Ka gargaxi mutanenka tun kafin azaba mai raxaxi ta zo musu.”
قَالَ يَٰقَوۡمِ إِنِّي لَكُمۡ نَذِيرٞ مُّبِينٌ
Ya ce: “Ya ku mutanena, lalle ni mai gargaxi ne mabayyani a gare ku