السورة: Suratul Ma’ida

الآية : 25

قَالَ رَبِّ إِنِّي لَآ أَمۡلِكُ إِلَّا نَفۡسِي وَأَخِيۖ فَٱفۡرُقۡ بَيۡنَنَا وَبَيۡنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡفَٰسِقِينَ

Ya ce: “Ya Ubangijina, lalle ni ban mallaki kowa ba sai kaina da xan’uwana; don haka Ka yi hukunci tsakaninmu da mutanen da suke fasiqai.”



السورة: Suratul Ma’ida

الآية : 26

قَالَ فَإِنَّهَا مُحَرَّمَةٌ عَلَيۡهِمۡۛ أَرۡبَعِينَ سَنَةٗۛ يَتِيهُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِۚ فَلَا تَأۡسَ عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡفَٰسِقِينَ

Ya ce: “To lalle an haramta musu (shigarta) har tsawon shekara arba’in. Za su yi ta ximuwa a bayan qasa. Don haka kada ka yi baqin ciki a kan mutanen da suke fasiqai.”



السورة: Suratul An’am

الآية : 154

ثُمَّ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ تَمَامًا عَلَى ٱلَّذِيٓ أَحۡسَنَ وَتَفۡصِيلٗا لِّكُلِّ شَيۡءٖ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٗ لَّعَلَّهُم بِلِقَآءِ رَبِّهِمۡ يُؤۡمِنُونَ

Sannan Muka bai wa Musa littafin (Attaura) don cika (ni’imarmu) ga wanda ya kyautata, kuma bayani ne na kowane irin abu, kuma shiriya ne da rahama, domin su zamo masu imani da haxuwa da Ubangijinsu



السورة: Suratul A’araf

الآية : 103

ثُمَّ بَعَثۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِم مُّوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَآ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ فَظَلَمُواْ بِهَاۖ فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُفۡسِدِينَ

Sannan sai Muka aika Musa a bayansu da ayoyinmu, zuwa Fir’auna da manyan mutanensa, sai suka zalunci (kansu) da su; to duba ka ga, yaya qarshen mavarnata ya kasance?



السورة: Suratul A’araf

الآية : 104

وَقَالَ مُوسَىٰ يَٰفِرۡعَوۡنُ إِنِّي رَسُولٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Kuma Musa ya ce: “Ya kai Fir’auna, lalle ni Manzo ne daga Ubangijin talikai



السورة: Suratul A’araf

الآية : 105

حَقِيقٌ عَلَىٰٓ أَن لَّآ أَقُولَ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡحَقَّۚ قَدۡ جِئۡتُكُم بِبَيِّنَةٖ مِّن رَّبِّكُمۡ فَأَرۡسِلۡ مَعِيَ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ

“Wajibi ne a kaina cewa ba zan faxi wata magana game da Allah ba sai ta gaskiya. Haqiqa na zo muku da hujja bayyananniya daga Ubangijinku, don haka ka sakar min Banu Isra’ila.”



السورة: Suratul A’araf

الآية : 106

قَالَ إِن كُنتَ جِئۡتَ بِـَٔايَةٖ فَأۡتِ بِهَآ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ

Sai ya ce: “Idan har kana da wata alama, to ka zo da ita, idan har kana cikin masu gaskiya.[1]”


1- A al’adar annabawa ba su ne suke fara bayyana mu’ujizarsu ba, har sai an qalubalance su, sai Allah () ya bayyana ta, don kiyaye martabar annabci kada a yi saurin qaryata su.


السورة: Suratul A’araf

الآية : 107

فَأَلۡقَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ ثُعۡبَانٞ مُّبِينٞ

Sai ya jefar da sandarsa, sai ga shi ta zama wani irin qaton kumurci a fili



السورة: Suratul A’araf

الآية : 108

وَنَزَعَ يَدَهُۥ فَإِذَا هِيَ بَيۡضَآءُ لِلنَّـٰظِرِينَ

Kuma ya zaro hannunsa, sai ga shi fari qal ga masu kallo



السورة: Suratul A’araf

الآية : 109

قَالَ ٱلۡمَلَأُ مِن قَوۡمِ فِرۡعَوۡنَ إِنَّ هَٰذَا لَسَٰحِرٌ عَلِيمٞ

Sai manyan gari daga cikin mutanen Fir’auna suka ce: “Lalle wannan tabbas mai sihiri ne, masani



السورة: Suratul A’araf

الآية : 110

يُرِيدُ أَن يُخۡرِجَكُم مِّنۡ أَرۡضِكُمۡۖ فَمَاذَا تَأۡمُرُونَ

“Yana nufi ne ya fitar da ku daga qasarku, don haka me kuke yin umarni (da a yi)?”



السورة: Suratul A’araf

الآية : 111

قَالُوٓاْ أَرۡجِهۡ وَأَخَاهُ وَأَرۡسِلۡ فِي ٱلۡمَدَآئِنِ حَٰشِرِينَ

Sai suka ce: “Ka dakatar da shi da xan’uwansa, ka kuma tura masu yin gangami cikin birane



السورة: Suratul A’araf

الآية : 112

يَأۡتُوكَ بِكُلِّ سَٰحِرٍ عَلِيمٖ

“Za su zo maka da duk wani qwararren matsafi.”



السورة: Suratul A’araf

الآية : 113

وَجَآءَ ٱلسَّحَرَةُ فِرۡعَوۡنَ قَالُوٓاْ إِنَّ لَنَا لَأَجۡرًا إِن كُنَّا نَحۡنُ ٱلۡغَٰلِبِينَ

Matsafan kuwa suka zo wa Fir’auna suka ce: “Shin tabbas muna da wani lada idan muka kasance masu rinjaye?”



السورة: Suratul A’araf

الآية : 114

قَالَ نَعَمۡ وَإِنَّكُمۡ لَمِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ

Ya ce, “E, kuma ma tabbas kuna cikin makusanta.”



السورة: Suratul A’araf

الآية : 115

قَالُواْ يَٰمُوسَىٰٓ إِمَّآ أَن تُلۡقِيَ وَإِمَّآ أَن نَّكُونَ نَحۡنُ ٱلۡمُلۡقِينَ

Sai suka ce: “Ya kai Musa, ko dai ka (fara) jefawa, ko kuwa mu mu kasance mu ne masu (fara) jefawa.”



السورة: Suratul A’araf

الآية : 116

قَالَ أَلۡقُواْۖ فَلَمَّآ أَلۡقَوۡاْ سَحَرُوٓاْ أَعۡيُنَ ٱلنَّاسِ وَٱسۡتَرۡهَبُوهُمۡ وَجَآءُو بِسِحۡرٍ عَظِيمٖ

Ya ce: “Ku jefa”. To yayin da suka jefa (sandunansu) sai suka sihirce idon mutane[1], kuma suka gigita su, suka zo da wani tsafi babba


1- Sihiri ba ya canza haqiqanin abu zuwa wani abu daban sai dai ya zama rufa ido kawai.


السورة: Suratul A’araf

الآية : 117

۞وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنۡ أَلۡقِ عَصَاكَۖ فَإِذَا هِيَ تَلۡقَفُ مَا يَأۡفِكُونَ

Muka kuma yi wahayi ga Musa cewa: “Jefa sandarka.” Sai ga shi nan take tana haxiye abin da suke qagowa



السورة: Suratul A’araf

الآية : 118

فَوَقَعَ ٱلۡحَقُّ وَبَطَلَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Sai gaskiya ta tabbata, abin da kuma suka kasance suna aikatawa sai ya lalace



السورة: Suratul A’araf

الآية : 119

فَغُلِبُواْ هُنَالِكَ وَٱنقَلَبُواْ صَٰغِرِينَ

Sai aka rinjaye su a nan, suka kuma juya a qasqance



السورة: Suratul A’araf

الآية : 120

وَأُلۡقِيَ ٱلسَّحَرَةُ سَٰجِدِينَ

Matsafa kuwa suka faxi suna masu sujjada



السورة: Suratul A’araf

الآية : 121

قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Suka ce: “Mun yi imani da Ubangijin talikai



السورة: Suratul A’araf

الآية : 122

رَبِّ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ

“Ubangijin Musa da Haruna.”



السورة: Suratul A’araf

الآية : 123

قَالَ فِرۡعَوۡنُ ءَامَنتُم بِهِۦ قَبۡلَ أَنۡ ءَاذَنَ لَكُمۡۖ إِنَّ هَٰذَا لَمَكۡرٞ مَّكَرۡتُمُوهُ فِي ٱلۡمَدِينَةِ لِتُخۡرِجُواْ مِنۡهَآ أَهۡلَهَاۖ فَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ

Sai Fir’auna ya ce: “Yanzu kun yi imani da shi tun kafin in yi muku izini? Lalle wannan tabbas wani makirci ne da kuka qulla shi a nan cikin garin, don ku fitar da mutanensa daga cikinsa; to da sannu za ku sani



السورة: Suratul A’araf

الآية : 124

لَأُقَطِّعَنَّ أَيۡدِيَكُمۡ وَأَرۡجُلَكُم مِّنۡ خِلَٰفٖ ثُمَّ لَأُصَلِّبَنَّكُمۡ أَجۡمَعِينَ

“Lalle zan yanyanke hannayenku da qafafuwanku a tarnaqe, sannan kuma gaba xaya zan gicciye ku.”



السورة: Suratul A’araf

الآية : 125

قَالُوٓاْ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ

Sai suka ce: “Mu kam lalle masu komawa ne ga Ubangijinmu.”



السورة: Suratul A’araf

الآية : 126

وَمَا تَنقِمُ مِنَّآ إِلَّآ أَنۡ ءَامَنَّا بِـَٔايَٰتِ رَبِّنَا لَمَّا جَآءَتۡنَاۚ رَبَّنَآ أَفۡرِغۡ عَلَيۡنَا صَبۡرٗا وَتَوَفَّنَا مُسۡلِمِينَ

“Kuma ba don komai za ka azabtar da mu ba sai don kawai mun yi imani da ayoyin Ubangijinmu yayin da suka zo mana. Ya Ubangijinmu, Ka zubo mana haquri, kuma Ka karvi rayukanmu muna Musulmi.”



السورة: Suratul A’araf

الآية : 127

وَقَالَ ٱلۡمَلَأُ مِن قَوۡمِ فِرۡعَوۡنَ أَتَذَرُ مُوسَىٰ وَقَوۡمَهُۥ لِيُفۡسِدُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَيَذَرَكَ وَءَالِهَتَكَۚ قَالَ سَنُقَتِّلُ أَبۡنَآءَهُمۡ وَنَسۡتَحۡيِۦ نِسَآءَهُمۡ وَإِنَّا فَوۡقَهُمۡ قَٰهِرُونَ

Sai manyan gari cikin mutanen Fir’auna suka ce: “Yanzu za ka qyale Musa da mutanensa, don su yi varna a bayan qasa, kuma ya watsar da kai da abubuwan bautarka?”[1] Sai ya ce: “Lalle za mu karkashe ‘ya’yansu maza, mu qyale ‘ya’yansu mata da rai[2], kuma lalle mu masu rinjaye ne a kansu.”


1- Bahaushe yana cewa, ba a mugun sarki sai mugun bafade. Manyan fadawan Fir’auna ne suke zuga shi a kan ya gaggauta xaukar mataki a kan Musa () da mabiyansa.


2- Da alama yanzu zai riqa kashe ‘ya’yan muminai ne kaxai. Ba kamar yadda yake kuxin goro da farko ba ba tare da bambancewa tsakanin Banu Isra’ila waxanda suka bi shi da waxanda ba su bi shi ba.


السورة: Suratul A’araf

الآية : 128

قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِ ٱسۡتَعِينُواْ بِٱللَّهِ وَٱصۡبِرُوٓاْۖ إِنَّ ٱلۡأَرۡضَ لِلَّهِ يُورِثُهَا مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۖ وَٱلۡعَٰقِبَةُ لِلۡمُتَّقِينَ

Sai Musa ya ce da mutanensa: “Ku nemi taimakon Allah, kuma ku yi haquri; lalle qasa mulkin Allah ce, Yana gadar da ita ga wanda Ya ga dama daga cikin bayinsa; kuma kyakkyawan qarshe yana tabbata ne ga masu taqawa.”



السورة: Suratul A’araf

الآية : 129

قَالُوٓاْ أُوذِينَا مِن قَبۡلِ أَن تَأۡتِيَنَا وَمِنۢ بَعۡدِ مَا جِئۡتَنَاۚ قَالَ عَسَىٰ رَبُّكُمۡ أَن يُهۡلِكَ عَدُوَّكُمۡ وَيَسۡتَخۡلِفَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرَ كَيۡفَ تَعۡمَلُونَ

Sai suka ce: “An cutar da mu tun kafin ka zo mana, da kuma bayan ka zo mana.” Sai ya ce: “Ta yiwu Ubangijinku Ya halakar da abokan gabarku, kuma Ya mayar da ku halifofi a bayan qasa, sai Ya ga kuma, me za ku aikata?”