قَالَ نَعَمۡ وَإِنَّكُمۡ إِذٗا لَّمِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ
(Fir’auna) ya ce: “Na’am, kuma ma idan haka ya faru, to tabbas za ku zama daga makusanta.”
قَالَ لَهُم مُّوسَىٰٓ أَلۡقُواْ مَآ أَنتُم مُّلۡقُونَ
(Sai Musa) ya ce da su: “Ku jefa duk abin da za ku jefa.”
فَأَلۡقَوۡاْ حِبَالَهُمۡ وَعِصِيَّهُمۡ وَقَالُواْ بِعِزَّةِ فِرۡعَوۡنَ إِنَّا لَنَحۡنُ ٱلۡغَٰلِبُونَ
Sai suka jefa igiyoyinsu da sandunansu suka kuma ce: “Lalle da izzar Fir’auna tabbas mu ne masu galaba.”
فَأَلۡقَىٰ مُوسَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ تَلۡقَفُ مَا يَأۡفِكُونَ
Sai Musa ya jefa sandarsa, sai ga ta tana lanqwame duk abin da suke qagowa (na sihiri)
فَأُلۡقِيَ ٱلسَّحَرَةُ سَٰجِدِينَ
Sai aka durqusar da masu sihirin suna masu sujjada
قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Suka ce: “Mun yi imani da Ubangijin talikai
رَبِّ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ
“Ubangijin Musa da Haruna.”
قَالَ ءَامَنتُمۡ لَهُۥ قَبۡلَ أَنۡ ءَاذَنَ لَكُمۡۖ إِنَّهُۥ لَكَبِيرُكُمُ ٱلَّذِي عَلَّمَكُمُ ٱلسِّحۡرَ فَلَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَۚ لَأُقَطِّعَنَّ أَيۡدِيَكُمۡ وَأَرۡجُلَكُم مِّنۡ خِلَٰفٖ وَلَأُصَلِّبَنَّكُمۡ أَجۡمَعِينَ
(Sai Fir’auna) ya ce: “Yanzu kwa yi imani da shi tun kafin in ba ku izini? Lalle tabbas shi ne babbanku wanda ya koya muku sihiri; to tabbas kuwa kwa sani. Lalle zan yanyanke hannayenku da qafafuwanku a tarnaqe, kuma tabbas zan gicciye ku gaba xaya!”
قَالُواْ لَا ضَيۡرَۖ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ
Sai suka ce: “Ai ba damuwa; lalle mu masu komawa ne zuwa ga Ubangijinmu
إِنَّا نَطۡمَعُ أَن يَغۡفِرَ لَنَا رَبُّنَا خَطَٰيَٰنَآ أَن كُنَّآ أَوَّلَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
“Lalle mu muna kwaxayin Ubangijinmu Ya gafarta mana kurakuranmu saboda zamantowarmu farkon muminai.”
۞وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنۡ أَسۡرِ بِعِبَادِيٓ إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ
Muka kuma yi wa Musa wahayi cewa: “Ka tafi cikin dare tare da bayina, lalle ku za a biyo bayanku.”
فَأَرۡسَلَ فِرۡعَوۡنُ فِي ٱلۡمَدَآئِنِ حَٰشِرِينَ
Sai Fir’auna ya aika zuwa birane don a tattaro (mayaqa)
إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ لَشِرۡذِمَةٞ قَلِيلُونَ
(Fir’auna yana cewa): “Lalle waxannan tabbas ‘yan tsirarin jama’a ne
وَإِنَّهُمۡ لَنَا لَغَآئِظُونَ
“Kuma haqiqa su lalle suna fusata mu
وَإِنَّا لَجَمِيعٌ حَٰذِرُونَ
“Lalle kuma mu tabbas gaba xayanmu masu kwana cikin shiri ne.”
فَأَخۡرَجۡنَٰهُم مِّن جَنَّـٰتٖ وَعُيُونٖ
(Allah Ya ce): Sai Muka fitar da su daga gonaki da kuma idandunan ruwa
وَكُنُوزٖ وَمَقَامٖ كَرِيمٖ
Da taskoki da kuma mazauni na alfarma
كَذَٰلِكَۖ وَأَوۡرَثۡنَٰهَا بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ
Kamar haka ne Muka gadar da su ga Banu-Isra’ila
فَأَتۡبَعُوهُم مُّشۡرِقِينَ
Sai suka bi bayansu a lokacin fitowar rana
فَلَمَّا تَرَـٰٓءَا ٱلۡجَمۡعَانِ قَالَ أَصۡحَٰبُ مُوسَىٰٓ إِنَّا لَمُدۡرَكُونَ
To lokacin da jama’ar biyu suka ga juna, sai sahabban Musa suka ce: “Lalle tabbas mu za a cim mana.”
قَالَ كَلَّآۖ إِنَّ مَعِيَ رَبِّي سَيَهۡدِينِ
(Musa) ya ce: “A’a; Ubangijina Yana tare da ni, zai kuwa shiryar da ni (hanyar tsira).”
فَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱضۡرِب بِّعَصَاكَ ٱلۡبَحۡرَۖ فَٱنفَلَقَ فَكَانَ كُلُّ فِرۡقٖ كَٱلطَّوۡدِ ٱلۡعَظِيمِ
Sai Muka yi wahayi ga Musa cewa: “Ka bugi kogin da sandarka;” (da ya buge shi) sai ya dare, kowanne yanki sai ya zama kamar qaton dutse
وَأَزۡلَفۡنَا ثَمَّ ٱلۡأٓخَرِينَ
Muka kuma kusantar da waxancan (watau mutanen Fir’auna) zuwa can (kusa da kogin)
وَأَنجَيۡنَا مُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُۥٓ أَجۡمَعِينَ
Muka kuma tserar da Musa da waxanda suke tare da shi gaba xaya
ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ
Sannan Muka nutsar da sauran mutanen (watau Fir’auna da mutanensa)
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu ba su zamanto muminai ba
إِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِأَهۡلِهِۦٓ إِنِّيٓ ءَانَسۡتُ نَارٗا سَـَٔاتِيكُم مِّنۡهَا بِخَبَرٍ أَوۡ ءَاتِيكُم بِشِهَابٖ قَبَسٖ لَّعَلَّكُمۡ تَصۡطَلُونَ
Ka tuna lokacin da Musa ya ce da iyalinsa: “Lalle ni na hango wata wuta, to (zan je) in zo muku da labari, ko kuma in zo muku da xosanen garwashi don ku ji xumi.”
فَلَمَّا جَآءَهَا نُودِيَ أَنۢ بُورِكَ مَن فِي ٱلنَّارِ وَمَنۡ حَوۡلَهَا وَسُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
To lokacin da ya zo mata (wutar) sai aka kira shi cewa, an tsarkake wanda yake cikin wutar da waxanda suke daura da ita (wato mala’iku), kuma tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai
يَٰمُوسَىٰٓ إِنَّهُۥٓ أَنَا ٱللَّهُ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Ya Musa, lalle lamarin dai, Ni ne Allah Mabuwayi, Mai hikima
وَأَلۡقِ عَصَاكَۚ فَلَمَّا رَءَاهَا تَهۡتَزُّ كَأَنَّهَا جَآنّٞ وَلَّىٰ مُدۡبِرٗا وَلَمۡ يُعَقِّبۡۚ يَٰمُوسَىٰ لَا تَخَفۡ إِنِّي لَا يَخَافُ لَدَيَّ ٱلۡمُرۡسَلُونَ
Kuma ka jefar da sandarka. To lokacin da ya gan ta tana jujjuyawa kamar macijiya, sai ya juya da baya a guje bai dawo ba. (Allah ya ce): Ya Musa, kada ka ji tsoro, lalle Ni manzanni ba sa jin tsoro a wurina