قَالَ إِنِّي عَبۡدُ ٱللَّهِ ءَاتَىٰنِيَ ٱلۡكِتَٰبَ وَجَعَلَنِي نَبِيّٗا
(Isa) ya ce (da su): “Lalle ni bawan Allah ne, Ya ba ni littafi Ya kuma sanya ni Annabi
وَجَعَلَنِي مُبَارَكًا أَيۡنَ مَا كُنتُ وَأَوۡصَٰنِي بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱلزَّكَوٰةِ مَا دُمۡتُ حَيّٗا
“Ya kuma sanya ni mai albarka a duk inda nake, kuma Ya umarce ni da yin salla da kuma ba da zakka matuqar ina raye
وَبَرَّۢا بِوَٰلِدَتِي وَلَمۡ يَجۡعَلۡنِي جَبَّارٗا شَقِيّٗا
“Kuma mai biyayya ga mahaifiyata, bai kuma sanya ni mai girman kai mai savo ba
وَٱلسَّلَٰمُ عَلَيَّ يَوۡمَ وُلِدتُّ وَيَوۡمَ أَمُوتُ وَيَوۡمَ أُبۡعَثُ حَيّٗا
“Amincin (Allah) kuma ya tabbata a gare ni ranar da aka haife ni da ranar da zan mutu da kuma ranar da za a tashe ni rayayye.”
ذَٰلِكَ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَۖ قَوۡلَ ٱلۡحَقِّ ٱلَّذِي فِيهِ يَمۡتَرُونَ
Wannan shi ne Isa xan Maryamu. Zance na gaskiya wanda a kansa ne suke ta shakka suna jayayya (da junansu)
وَٱلَّتِيٓ أَحۡصَنَتۡ فَرۡجَهَا فَنَفَخۡنَا فِيهَا مِن رُّوحِنَا وَجَعَلۡنَٰهَا وَٱبۡنَهَآ ءَايَةٗ لِّلۡعَٰلَمِينَ
(Ka tuna) kuma wadda ta tsare matancinta, sai Muka yi busa a cikinta daga Ruhinmu, Muka kuma sanya ta ita da xanta aya ga talikai
وَجَعَلۡنَا ٱبۡنَ مَرۡيَمَ وَأُمَّهُۥٓ ءَايَةٗ وَءَاوَيۡنَٰهُمَآ إِلَىٰ رَبۡوَةٖ ذَاتِ قَرَارٖ وَمَعِينٖ
Muka kuma sanya Xan Maryamu da mahaifiyarsa (don su zama) aya, Muka kuma zaunar da su a wata jigawa ta hutawa da kuma ruwa mai gudana
وَمَرۡيَمَ ٱبۡنَتَ عِمۡرَٰنَ ٱلَّتِيٓ أَحۡصَنَتۡ فَرۡجَهَا فَنَفَخۡنَا فِيهِ مِن رُّوحِنَا وَصَدَّقَتۡ بِكَلِمَٰتِ رَبِّهَا وَكُتُبِهِۦ وَكَانَتۡ مِنَ ٱلۡقَٰنِتِينَ
Da kuma Maryamu ‘yar Imrana wadda ta kiyaye matuncinta, sai Muka masa busa daga Ruhinmu[1], ta kuma gaskata ayoyin Ubangijinta da littattafansa, ta kuma kasance daga masu biyayya ga Allah
1- Watau Allah ya umarci Mala’ika Jibrilu () ya yi busa a gare ta.