السورة: Suratul Baqara

الآية : 155

وَلَنَبۡلُوَنَّكُم بِشَيۡءٖ مِّنَ ٱلۡخَوۡفِ وَٱلۡجُوعِ وَنَقۡصٖ مِّنَ ٱلۡأَمۡوَٰلِ وَٱلۡأَنفُسِ وَٱلثَّمَرَٰتِۗ وَبَشِّرِ ٱلصَّـٰبِرِينَ

Kuma lalle za Mu jarrabe ku da wani abin tsoro da yunwa da tawayar dukiya da ta rayuka da ta ‘ya’yan itatuwa. Don haka ka yi albishir ga masu haquri



السورة: Suratul An’am

الآية : 164

قُلۡ أَغَيۡرَ ٱللَّهِ أَبۡغِي رَبّٗا وَهُوَ رَبُّ كُلِّ شَيۡءٖۚ وَلَا تَكۡسِبُ كُلُّ نَفۡسٍ إِلَّا عَلَيۡهَاۚ وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰۚ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُم مَّرۡجِعُكُمۡ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ فِيهِ تَخۡتَلِفُونَ

Ka ce: “Yanzu wanin Allah zan riqa a matsayin ubangiji, alhalin kuwa Shi ne Ubangijin komai? Kuma ba wani rai da zai aikata wani abu face sai don kansa. Kuma ba wani rai da zai xauki laifin wani rai. Sannan kuma zuwa ga Ubangijinku ne makomarku take, sai Ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna savani a game da shi



السورة: Suratul An’am

الآية : 165

وَهُوَ ٱلَّذِي جَعَلَكُمۡ خَلَـٰٓئِفَ ٱلۡأَرۡضِ وَرَفَعَ بَعۡضَكُمۡ فَوۡقَ بَعۡضٖ دَرَجَٰتٖ لِّيَبۡلُوَكُمۡ فِي مَآ ءَاتَىٰكُمۡۗ إِنَّ رَبَّكَ سَرِيعُ ٱلۡعِقَابِ وَإِنَّهُۥ لَغَفُورٞ رَّحِيمُۢ

“Kuma Shi ne Ya sanya ku halifofi a bayan qasa, kuma Ya xaukaka darajar wasunku a kan wasu, don Ya jarrabe ku game da abin da Ya ba ku. Lalle Ubangijinka Mai gaggawar uquba ne, kuma lalle Shi tabbas Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin qai.”



السورة: Suratul Anfal

الآية : 25

وَٱتَّقُواْ فِتۡنَةٗ لَّا تُصِيبَنَّ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنكُمۡ خَآصَّةٗۖ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

Ku kiyayi fitinar da ba kawai waxanda suka yi zalunci za ta shafa ba, kuma ku sani cewa lalle Allah Mai tsananin uquba ne



السورة: Suratul Anfal

الآية : 28

وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَآ أَمۡوَٰلُكُمۡ وَأَوۡلَٰدُكُمۡ فِتۡنَةٞ وَأَنَّ ٱللَّهَ عِندَهُۥٓ أَجۡرٌ عَظِيمٞ

Kuma ku sani cewa, dukiyoyinku da ‘ya’yanku fitina ne, Allah kuma lalle a wurinsa lada mai girma yake



السورة: Suratu Hud

الآية : 7

وَهُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ وَكَانَ عَرۡشُهُۥ عَلَى ٱلۡمَآءِ لِيَبۡلُوَكُمۡ أَيُّكُمۡ أَحۡسَنُ عَمَلٗاۗ وَلَئِن قُلۡتَ إِنَّكُم مَّبۡعُوثُونَ مِنۢ بَعۡدِ ٱلۡمَوۡتِ لَيَقُولَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٞ

Shi ne kuma wanda Ya halicci sammai da qasa cikin kwana shida, Al’arshinsa kuwa ya kasance a kan ruwa, don Ya jarraba ku a cikinku wa ya fi kyakkyawan aiki. Kuma tabbas idan ka ce (da su): “Lalle za a tashe ku bayan mutuwa,” tabbas kafirai za su ce: “Ai wannan ba wani abu ba ne sai tsafi mabayyani.”



السورة: Suratun Nahl

الآية : 92

وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّتِي نَقَضَتۡ غَزۡلَهَا مِنۢ بَعۡدِ قُوَّةٍ أَنكَٰثٗا تَتَّخِذُونَ أَيۡمَٰنَكُمۡ دَخَلَۢا بَيۡنَكُمۡ أَن تَكُونَ أُمَّةٌ هِيَ أَرۡبَىٰ مِنۡ أُمَّةٍۚ إِنَّمَا يَبۡلُوكُمُ ٱللَّهُ بِهِۦۚ وَلَيُبَيِّنَنَّ لَكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ مَا كُنتُمۡ فِيهِ تَخۡتَلِفُونَ

Kada kuma ku zamanto kamar (mace) wadda ta warware kaxinta wara-wara bayan qarfinsa, kuna xaukar rantse-rantsenku yaudara a tsakaninku, don ganin kasancewar wata al’umma ta fi wata yawa da qarfi. Allah dai Yana jarabtar ku da shi (cika alqawari) ne. Don kuma a ranar alqiyama Ya bayyana muku abin da kuka kasance kuna savani a game da shi



السورة: Suratul Kahf 

الآية : 7

إِنَّا جَعَلۡنَا مَا عَلَى ٱلۡأَرۡضِ زِينَةٗ لَّهَا لِنَبۡلُوَهُمۡ أَيُّهُمۡ أَحۡسَنُ عَمَلٗا

Lalle Mu Mun sanya abin da yake bayan qasa ya zama ado a gare ta, don (kuma) Mu jarraba su, wane ne daga cikinsu ya fi kyakkyawan aiki?



السورة: Suratul Anbiya

الآية : 35

كُلُّ نَفۡسٖ ذَآئِقَةُ ٱلۡمَوۡتِۗ وَنَبۡلُوكُم بِٱلشَّرِّ وَٱلۡخَيۡرِ فِتۡنَةٗۖ وَإِلَيۡنَا تُرۡجَعُونَ

Kowanne rai zai xanxani mutuwa. Muna kuwa jarrabar ku da fitinar sharri da ta alheri, kuma gare Mu ne za a dawo da ku



السورة: Suratul Hajji

الآية : 11

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَعۡبُدُ ٱللَّهَ عَلَىٰ حَرۡفٖۖ فَإِنۡ أَصَابَهُۥ خَيۡرٌ ٱطۡمَأَنَّ بِهِۦۖ وَإِنۡ أَصَابَتۡهُ فِتۡنَةٌ ٱنقَلَبَ عَلَىٰ وَجۡهِهِۦ خَسِرَ ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةَۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡخُسۡرَانُ ٱلۡمُبِينُ

Daga mutane kuma akwai wanda yake bauta wa Allah a kan gava[1]; to idan alheri ya same shi sai ya nutsu da shi, idan kuwa wata masifa ta same shi sai ya juya a kan fuskarsa; to ya yi hasarar duniya da lahira. Wannan (kuwa) ita ce hasara bayyananniya


1- Watau yana bautar Allah cikin shakku, shi ne munafuki.


السورة: Suratul Furqan

الآية : 20

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا قَبۡلَكَ مِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ إِلَّآ إِنَّهُمۡ لَيَأۡكُلُونَ ٱلطَّعَامَ وَيَمۡشُونَ فِي ٱلۡأَسۡوَاقِۗ وَجَعَلۡنَا بَعۡضَكُمۡ لِبَعۡضٖ فِتۡنَةً أَتَصۡبِرُونَۗ وَكَانَ رَبُّكَ بَصِيرٗا

Kuma ba Mu aiko manzanni ba gabaninka sai cewa lalle suna cin abinci kuma suna tafiya cikin kasuwanni. Mun kuwa sanya wasunku su zama fitina ga wasu. Shin za ku yi haquri? Ubangijinka kuwa Ya kasance Mai gani ne



السورة: Suratul Ankabut

الآية : 2

أَحَسِبَ ٱلنَّاسُ أَن يُتۡرَكُوٓاْ أَن يَقُولُوٓاْ ءَامَنَّا وَهُمۡ لَا يُفۡتَنُونَ

Yanzu mutane suna tsammanin za a qyale su ne saboda suna cewa: “Mun yi imani,” kuma ba za a fitine su ba?



السورة: Suratul Ankabut

الآية : 3

وَلَقَدۡ فَتَنَّا ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۖ فَلَيَعۡلَمَنَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ صَدَقُواْ وَلَيَعۡلَمَنَّ ٱلۡكَٰذِبِينَ

Haqiqa kuwa Mun fitini waxanda suke gabaninsu; to tabbas kuwa Allah zai bayyana waxanda suka yi gaskiya, lalle kuma zai bayyana maqaryata



السورة: Suratul Ankabut

الآية : 10

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَقُولُ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ فَإِذَآ أُوذِيَ فِي ٱللَّهِ جَعَلَ فِتۡنَةَ ٱلنَّاسِ كَعَذَابِ ٱللَّهِۖ وَلَئِن جَآءَ نَصۡرٞ مِّن رَّبِّكَ لَيَقُولُنَّ إِنَّا كُنَّا مَعَكُمۡۚ أَوَلَيۡسَ ٱللَّهُ بِأَعۡلَمَ بِمَا فِي صُدُورِ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Kuma cikin mutane akwai mai cewa: “Mun yi imani da Allah,” to idan aka cuce shi a kan hanyar Allah sai yakan xauki fitinar mutane kamar azabar Allah, lalle kuwa idan wata nasara ta zo daga Ubangijinka, tabbas zai riqa cewa: “Lalle mu mun kasance tare da ku.” Yanzu Allah ba Shi Ya fi kowa sanin abin da ke cikin zukatan talikai ba?



السورة: Suratuz Zumar

الآية : 49

فَإِذَا مَسَّ ٱلۡإِنسَٰنَ ضُرّٞ دَعَانَا ثُمَّ إِذَا خَوَّلۡنَٰهُ نِعۡمَةٗ مِّنَّا قَالَ إِنَّمَآ أُوتِيتُهُۥ عَلَىٰ عِلۡمِۭۚ بَلۡ هِيَ فِتۡنَةٞ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

To idan wata cuta ta samu mutum sai ya roqe Mu, sannan idan Mun ba shi wata ni’ima daga gare Mu sai ya ce: “Ai an ba ni ita ne kawai don sanin (cancantata)”. Ba haka ba ne, ita wata jarrabawa ce kawai, sai dai yawancinsu ba sa sanin (haka)



السورة: Suratuz Zariyat

الآية : 56

وَمَا خَلَقۡتُ ٱلۡجِنَّ وَٱلۡإِنسَ إِلَّا لِيَعۡبُدُونِ

Ban halicci aljanu da mutane ba sai don su bauta min



السورة: Suratul Hadid

الآية : 25

لَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا رُسُلَنَا بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَأَنزَلۡنَا مَعَهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡمِيزَانَ لِيَقُومَ ٱلنَّاسُ بِٱلۡقِسۡطِۖ وَأَنزَلۡنَا ٱلۡحَدِيدَ فِيهِ بَأۡسٞ شَدِيدٞ وَمَنَٰفِعُ لِلنَّاسِ وَلِيَعۡلَمَ ٱللَّهُ مَن يَنصُرُهُۥ وَرُسُلَهُۥ بِٱلۡغَيۡبِۚ إِنَّ ٱللَّهَ قَوِيٌّ عَزِيزٞ

Haqiqa Mun aiko manzanninmu da (ayoyi) mabayyana, Muka kuma saukar da littafi da ma’auni a tare da su (manzannin) don mutane su tsaya da adalci; Muka kuma saukar da baqin qarfe wanda a tare da shi akwai tsananin qarfi da kuma amfani ga mutane, don kuma Allah Ya bayyanar da wanda yake taimakon Sa da manzanninsa a voye. Lalle Allah Mai qarfi ne, Mabuwayi



السورة: Suratul Mulk

الآية : 2

ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلۡمَوۡتَ وَٱلۡحَيَوٰةَ لِيَبۡلُوَكُمۡ أَيُّكُمۡ أَحۡسَنُ عَمَلٗاۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡغَفُورُ

Wanda Ya halicci mutuwa da rayuwa don Ya jarraba ku (Ya bayyana) wane ne a cikinku ya fi kyakkyawan aiki? Shi kuma Mabuwayi ne, Mai gafara



السورة: Suratul Insan

الآية : 2

إِنَّا خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ مِن نُّطۡفَةٍ أَمۡشَاجٖ نَّبۡتَلِيهِ فَجَعَلۡنَٰهُ سَمِيعَۢا بَصِيرًا

Lalle Mun halicci mutum daga maniyyi gamin-gambiza[1] don Mu jarrabe shi, sai Muka sanya shi mai ji mai gani


1- Watau tsakanin na namiji da na mace.


السورة: Suratul Fajr

الآية : 15

فَأَمَّا ٱلۡإِنسَٰنُ إِذَا مَا ٱبۡتَلَىٰهُ رَبُّهُۥ فَأَكۡرَمَهُۥ وَنَعَّمَهُۥ فَيَقُولُ رَبِّيٓ أَكۡرَمَنِ

Amma kuma mutum idan Ubangijinsa Ya jarrabe shi sai Ya karrama shi, Ya kuma yi masa ni’ima, sai ya ce: “Ubangijina Ya karrama ni.”



السورة: Suratul Fajr

الآية : 16

وَأَمَّآ إِذَا مَا ٱبۡتَلَىٰهُ فَقَدَرَ عَلَيۡهِ رِزۡقَهُۥ فَيَقُولُ رَبِّيٓ أَهَٰنَنِ

Amma kuma idan Ya jarrabe shi sai Ya quntata masa a arzikinsa, sai ya ce: “Ubangijina Ya wulaqanta ni.”