السورة: Suratul Baqara

الآية : 96

وَلَتَجِدَنَّهُمۡ أَحۡرَصَ ٱلنَّاسِ عَلَىٰ حَيَوٰةٖ وَمِنَ ٱلَّذِينَ أَشۡرَكُواْۚ يَوَدُّ أَحَدُهُمۡ لَوۡ يُعَمَّرُ أَلۡفَ سَنَةٖ وَمَا هُوَ بِمُزَحۡزِحِهِۦ مِنَ ٱلۡعَذَابِ أَن يُعَمَّرَۗ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِمَا يَعۡمَلُونَ

Kuma lalle za ka same su sun fi kowa kwaxayin tsawon rai, fiye ma da waxanda suka yi shirka. Kowane xayansu yana burin ina ma za a raya shi shekara dubu. Hakan kuma ba zai nesanta shi daga azaba ba don an yi masa tsawon rai. Kuma Allah Mai ganin abin da suka kasance suna aikatawa ne



السورة: Suratul Baqara

الآية : 165

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَتَّخِذُ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَندَادٗا يُحِبُّونَهُمۡ كَحُبِّ ٱللَّهِۖ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَشَدُّ حُبّٗا لِّلَّهِۗ وَلَوۡ يَرَى ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ إِذۡ يَرَوۡنَ ٱلۡعَذَابَ أَنَّ ٱلۡقُوَّةَ لِلَّهِ جَمِيعٗا وَأَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعَذَابِ

Kuma akwai wasu mutane waxanda suke bauta wa wasu kishiyoyi ba Allah ba; suna son su kamar son Allah; waxanda kuwa suka yi imani sun fi son Allah (fiye da komai). Da a ce waxanda suka yi zalunci za su ga lokacin da suke ido huxu da azaba (to da sun gane) cewa, lalle duk wani qarfi na Allah ne gaba xaya, kuma lalle Allah Mai tsananin azaba ne



السورة: Suratul Baqara

الآية : 200

فَإِذَا قَضَيۡتُم مَّنَٰسِكَكُمۡ فَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ كَذِكۡرِكُمۡ ءَابَآءَكُمۡ أَوۡ أَشَدَّ ذِكۡرٗاۗ فَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَقُولُ رَبَّنَآ ءَاتِنَا فِي ٱلدُّنۡيَا وَمَا لَهُۥ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنۡ خَلَٰقٖ

To idan kun gama ayyukanku na Hajji, to ku yi ta ambaton Allah kamar yadda kuke ambaton iyayenku, ko ambaton (Allah) ya fi yawa. To daga cikin mutane akwai wanda yake cewa: “Ya Ubangijimu, Ka ba mu (rabo) a nan duniya”, kuma a lahira ba shi da wani rabo



السورة: Suratul Baqara

الآية : 212

زُيِّنَ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا وَيَسۡخَرُونَ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْۘ وَٱلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ فَوۡقَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ وَٱللَّهُ يَرۡزُقُ مَن يَشَآءُ بِغَيۡرِ حِسَابٖ

An qawata wa kafirai rayuwar duniya, kuma suna yin izgili ga waxanda suka yi imani. Waxanda kuwa suka yi taqawa su ne a samansu a ranar alqiyama. Kuma Allah Yana arzurta wanda ya ga dama, ba tare da lissafi ba



السورة: Suratul Baqara

الآية : 216

كُتِبَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡقِتَالُ وَهُوَ كُرۡهٞ لَّكُمۡۖ وَعَسَىٰٓ أَن تَكۡرَهُواْ شَيۡـٔٗا وَهُوَ خَيۡرٞ لَّكُمۡۖ وَعَسَىٰٓ أَن تُحِبُّواْ شَيۡـٔٗا وَهُوَ شَرّٞ لَّكُمۡۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ

An wajabta muku yaqi (ku muminai), ga shi kuwa kuna qin sa, kuma zai iya yiwuwa ku qi wani abu alhalin shi alheri ne a gare ku, kuma zai iya yiwuwa ku so wani abu alhalin shi sharri ne a gare ku. Kuma Allah Shi yake da sani, ku ba ku sani ba



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 14

زُيِّنَ لِلنَّاسِ حُبُّ ٱلشَّهَوَٰتِ مِنَ ٱلنِّسَآءِ وَٱلۡبَنِينَ وَٱلۡقَنَٰطِيرِ ٱلۡمُقَنطَرَةِ مِنَ ٱلذَّهَبِ وَٱلۡفِضَّةِ وَٱلۡخَيۡلِ ٱلۡمُسَوَّمَةِ وَٱلۡأَنۡعَٰمِ وَٱلۡحَرۡثِۗ ذَٰلِكَ مَتَٰعُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَٱللَّهُ عِندَهُۥ حُسۡنُ ٱلۡمَـَٔابِ

An qawata wa mutane son sha’awace-sha’awace na mata da ‘ya’ya da dukiya mai yawa abar tarawa ta zinariya da azurfa da kuma kiwatattun dawaki da dabbobi na gida da amfanin gona. Waxannan duk morewa ce ta rayuwar duniya; Allah kuwa a wurinsa ne kyakkyawar makoma take



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 85

وَمَن يَبۡتَغِ غَيۡرَ ٱلۡإِسۡلَٰمِ دِينٗا فَلَن يُقۡبَلَ مِنۡهُ وَهُوَ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

Duk kuma wanda ya nemi (bin) wani addini ba Musulunci ba, to har abada ba za a karva daga gare shi ba, kuma shi a lahira yana cikin hasararru



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 152

وَلَقَدۡ صَدَقَكُمُ ٱللَّهُ وَعۡدَهُۥٓ إِذۡ تَحُسُّونَهُم بِإِذۡنِهِۦۖ حَتَّىٰٓ إِذَا فَشِلۡتُمۡ وَتَنَٰزَعۡتُمۡ فِي ٱلۡأَمۡرِ وَعَصَيۡتُم مِّنۢ بَعۡدِ مَآ أَرَىٰكُم مَّا تُحِبُّونَۚ مِنكُم مَّن يُرِيدُ ٱلدُّنۡيَا وَمِنكُم مَّن يُرِيدُ ٱلۡأٓخِرَةَۚ ثُمَّ صَرَفَكُمۡ عَنۡهُمۡ لِيَبۡتَلِيَكُمۡۖ وَلَقَدۡ عَفَا عَنكُمۡۗ وَٱللَّهُ ذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Kuma tabbas haqiqa Allah Ya cika muku alqawarinsa yayin da kuka riqa kisan su da yawa da izininsa; har zuwa lokacin da kuka yi rauni, kuma kuka yi jayayya a cikin umarnin (Manzo), kuma daga qarshe kuka sava bayan (Allah) Ya nuna muku irin abin da kuke so. Cikinku akwai waxanda suke nufin duniya, kuma cikinku akwai waxanda suke nufin lahira. Sannan sai Ya kautar da ku kuka bar su don ya jarrabe ku; kuma tabbas haqiqa Allah Ya yi muku afuwa. Kuma Allah Ma’abocin falala ne ga muminai



السورة: Suratu Ali-Imran

الآية : 188

لَا تَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ يَفۡرَحُونَ بِمَآ أَتَواْ وَّيُحِبُّونَ أَن يُحۡمَدُواْ بِمَا لَمۡ يَفۡعَلُواْ فَلَا تَحۡسَبَنَّهُم بِمَفَازَةٖ مِّنَ ٱلۡعَذَابِۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Kada ka yi tsammanin waxanda suke yin farin ciki da irin abin da suka aikata, kuma suna son a riqa yabon su da abin da ba su aikata ba, to kada ka yi tsammanin za su tsira daga azaba, kuma suna da azaba mai raxaxi



السورة: Suratun Nisa’i

الآية : 94

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا ضَرَبۡتُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَتَبَيَّنُواْ وَلَا تَقُولُواْ لِمَنۡ أَلۡقَىٰٓ إِلَيۡكُمُ ٱلسَّلَٰمَ لَسۡتَ مُؤۡمِنٗا تَبۡتَغُونَ عَرَضَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا فَعِندَ ٱللَّهِ مَغَانِمُ كَثِيرَةٞۚ كَذَٰلِكَ كُنتُم مِّن قَبۡلُ فَمَنَّ ٱللَّهُ عَلَيۡكُمۡ فَتَبَيَّنُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٗا

Ya ku waxanda suka yi imani, idan kuka fita yaqi don xaukaka kalmar Allah, to ku riqa bincike, kuma kada ku ce ma wanda ya yi muku sallama: “Kai ba mumini ba ne,”[1] don kawai kuna neman wani jin daxi na rayuwar duniya, to a wurin Allah ne ganimomi masu yawa suke. Kamar haka ku ma a da kuka kasance[2], sai Allah Ya yi muku baiwa, don haka ku riqa bincike. Lalle Allah Ya kasance Mai cikakken sanin abin da kuke aikatawa ne


1- Watau su xauke shi kawai a matsayin wanda yake qoqarin kare kansa amma ba da gaske yake ba.


2- Watau suna voye imaninsu daga mutanensu mushirikai har Allah ya ba su ikon bayyana addininsu.


السورة: Suratul A’araf

الآية : 169

فَخَلَفَ مِنۢ بَعۡدِهِمۡ خَلۡفٞ وَرِثُواْ ٱلۡكِتَٰبَ يَأۡخُذُونَ عَرَضَ هَٰذَا ٱلۡأَدۡنَىٰ وَيَقُولُونَ سَيُغۡفَرُ لَنَا وَإِن يَأۡتِهِمۡ عَرَضٞ مِّثۡلُهُۥ يَأۡخُذُوهُۚ أَلَمۡ يُؤۡخَذۡ عَلَيۡهِم مِّيثَٰقُ ٱلۡكِتَٰبِ أَن لَّا يَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡحَقَّ وَدَرَسُواْ مَا فِيهِۗ وَٱلدَّارُ ٱلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ يَتَّقُونَۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ

Sai waxansu bara-gurbi suka maye bayansu, sun gaji littafin (Attaura), suna karvar abin duniya, suna kuma cewa: “Za a gafarta mana.” Kuma idan wani abin duniyar irinsa ya zo musu sai su sake karvar sa. Shin yanzu ba a xauki alqawari daga wurinsu ba a cikin littafin (Attaura) cewa, kada su faxi wata magana game da Allah sai gaskiya, kuma sun karanta abin da yake cikinsa? Kuma lalle gidan lahira shi ne mafi alheri ga dukkan waxanda suke da taqawa. Shin ba za ku hankalta ba?



السورة: Suratut Tauba

الآية : 24

قُلۡ إِن كَانَ ءَابَآؤُكُمۡ وَأَبۡنَآؤُكُمۡ وَإِخۡوَٰنُكُمۡ وَأَزۡوَٰجُكُمۡ وَعَشِيرَتُكُمۡ وَأَمۡوَٰلٌ ٱقۡتَرَفۡتُمُوهَا وَتِجَٰرَةٞ تَخۡشَوۡنَ كَسَادَهَا وَمَسَٰكِنُ تَرۡضَوۡنَهَآ أَحَبَّ إِلَيۡكُم مِّنَ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَجِهَادٖ فِي سَبِيلِهِۦ فَتَرَبَّصُواْ حَتَّىٰ يَأۡتِيَ ٱللَّهُ بِأَمۡرِهِۦۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡفَٰسِقِينَ

Ka ce: “Idan iyayenku da ‘ya’yanku da matanku da danginku da dukiyoyin da kuka tara da kasuwanci da kuke tsoron gurguncewarsa da kuma gidajen da kuke sha’awa; idan har su kuka fi so fiye da Allah da Manzonsa da kuma jihadi saboda Shi, to sai ku saurara har Allah Ya zo da al’amarinsa. Allah kuwa ba Ya shiryar da mutane fasiqai.”



السورة: Suratut Tauba

الآية : 38

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَا لَكُمۡ إِذَا قِيلَ لَكُمُ ٱنفِرُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ ٱثَّاقَلۡتُمۡ إِلَى ٱلۡأَرۡضِۚ أَرَضِيتُم بِٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا مِنَ ٱلۡأٓخِرَةِۚ فَمَا مَتَٰعُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا فِي ٱلۡأٓخِرَةِ إِلَّا قَلِيلٌ

Ya ku waxanda suka yi imani, me ya same ku ne idan aka ce da ku ku fita yaqi saboda Allah sai ku yi nauyin jiki? Yanzu kun zavi rayuwar duniya a kan ta lahira? Ai jin daxin rayuwar duniya abu ne qanqani dangane da na lahira



السورة: Suratu Yunus

الآية : 7

إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يَرۡجُونَ لِقَآءَنَا وَرَضُواْ بِٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَٱطۡمَأَنُّواْ بِهَا وَٱلَّذِينَ هُمۡ عَنۡ ءَايَٰتِنَا غَٰفِلُونَ

Lalle waxanda ba sa tsammanin gamuwa da Mu, suka kuma yarda da rayuwar duniya, kuma suka nutsu da ita, da kuma waxanda suke gafala daga ayoyinmu



السورة: Suratu Yunus

الآية : 8

أُوْلَـٰٓئِكَ مَأۡوَىٰهُمُ ٱلنَّارُ بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ

Waxanan makomarsu wuta ce saboda abin da suka kasance suna aikatawa



السورة: Suratur Ra’ad

الآية : 26

ٱللَّهُ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُۚ وَفَرِحُواْ بِٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا فِي ٱلۡأٓخِرَةِ إِلَّا مَتَٰعٞ

Allah ne Yake shimfixa arziki ga wanda Ya ga dama, Yake kuma quntatawa (ga wanda Ya ga dama. (Kafirai) kuma sun yi farin ciki da rayuwar duniya, rayuwar duniya kuwa ba komai ba ce illa xan jin daxi kaxan dangane da na lahira



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 2

ٱللَّهِ ٱلَّذِي لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَوَيۡلٞ لِّلۡكَٰفِرِينَ مِنۡ عَذَابٖ شَدِيدٍ

(Watau) Allah, Wanda abin da yake cikin sammai da na cikin qasa duka nasa ne. Bone na wata azaba mai tsanani kuma ya tabbatta ga kafirai



السورة: Suratu Ibrahim

الآية : 3

ٱلَّذِينَ يَسۡتَحِبُّونَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا عَلَى ٱلۡأٓخِرَةِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَيَبۡغُونَهَا عِوَجًاۚ أُوْلَـٰٓئِكَ فِي ضَلَٰلِۭ بَعِيدٖ

Waxanda suke fifita son rayuwar duniya a kan lahira, suke kuma hanawa (a bi) hanyar Allah, kuma suke neman ta zama karkatacciya. To waxannan suna cikin vata mai nisa



السورة: Suratun Nahl

الآية : 107

ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمُ ٱسۡتَحَبُّواْ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا عَلَى ٱلۡأٓخِرَةِ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Wannan kuwa (ya faru) saboda su sun fi son rayuwar duniya a kan ta lahira, kuma lalle Allah ba Ya shiryar da mutane kafirai



السورة: Suratul Isra’i

الآية : 18

مَّن كَانَ يُرِيدُ ٱلۡعَاجِلَةَ عَجَّلۡنَا لَهُۥ فِيهَا مَا نَشَآءُ لِمَن نُّرِيدُ ثُمَّ جَعَلۡنَا لَهُۥ جَهَنَّمَ يَصۡلَىٰهَا مَذۡمُومٗا مَّدۡحُورٗا

Wanda ya kasance yana nufin duniya ne (kawai) to za Mu gaggauto masa a cikinta abin da Muka ga dama ga wanda Muka yi nufi; sannan Mu sanya masa Jahannama, ya shige ta (a lahira) yana abin zargi, korarre (daga rahamar Allah)



السورة: Suratun Nur

الآية : 33

وَلۡيَسۡتَعۡفِفِ ٱلَّذِينَ لَا يَجِدُونَ نِكَاحًا حَتَّىٰ يُغۡنِيَهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦۗ وَٱلَّذِينَ يَبۡتَغُونَ ٱلۡكِتَٰبَ مِمَّا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡ فَكَاتِبُوهُمۡ إِنۡ عَلِمۡتُمۡ فِيهِمۡ خَيۡرٗاۖ وَءَاتُوهُم مِّن مَّالِ ٱللَّهِ ٱلَّذِيٓ ءَاتَىٰكُمۡۚ وَلَا تُكۡرِهُواْ فَتَيَٰتِكُمۡ عَلَى ٱلۡبِغَآءِ إِنۡ أَرَدۡنَ تَحَصُّنٗا لِّتَبۡتَغُواْ عَرَضَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۚ وَمَن يُكۡرِههُّنَّ فَإِنَّ ٱللَّهَ مِنۢ بَعۡدِ إِكۡرَٰهِهِنَّ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Waxanda kuma ba su sami wadatar yin aure ba su kame kansu har Allah Ya wadata su daga falalarsa. Waxanda kuwa suke neman fansar kansu daga bayinku[1], sai ku ba su damar fansar kansu, idan kun san suna da halin iya biya; kuma ku ba su wani abu daga dukiyar Allah da Ya ba ku. Kada kuma ku tilasta wa kuyanginku ‘yan mata a kan yin zina idan sun nemi kame kai, don ku nemi amfanin rayuwar duniya. Wanda duk kuwa ya tilasta su, to lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai bayan tilastawar da aka yi musu


1- Watau ta hanyar biyan wani kuxi da za a yanka musu idan sun biya sun zama ‘yantattun ‘ya’ya.


السورة: Suratul Qasas

الآية : 79

فَخَرَجَ عَلَىٰ قَوۡمِهِۦ فِي زِينَتِهِۦۖ قَالَ ٱلَّذِينَ يُرِيدُونَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا يَٰلَيۡتَ لَنَا مِثۡلَ مَآ أُوتِيَ قَٰرُونُ إِنَّهُۥ لَذُو حَظٍّ عَظِيمٖ

Sai ya fito wa mutanensa a cikin adonsa; sai waxanda suke burin rayuwar duniya suka ce: “Ina ma da za mu mallaki irin abin da aka bai wa Qaruna? Lalle shi mai babban rabo ne.”



السورة: Suratul Qasas

الآية : 80

وَقَالَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ وَيۡلَكُمۡ ثَوَابُ ٱللَّهِ خَيۡرٞ لِّمَنۡ ءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗاۚ وَلَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ٱلصَّـٰبِرُونَ

Waxanda kuwa aka bai wa ilimi sai suka ce: “Kaiconku, ai ladan Allah shi ya fi alheri ga wanda ya yi imani, ya kuma yi aiki na gari. Ba kuwa wanda ake yi wa katari da shi sai masu haquri.”



السورة: Suratu Sad

الآية : 32

فَقَالَ إِنِّيٓ أَحۡبَبۡتُ حُبَّ ٱلۡخَيۡرِ عَن ذِكۡرِ رَبِّي حَتَّىٰ تَوَارَتۡ بِٱلۡحِجَابِ

Sai ya ce: “Lalle ni na fifita son dukiya (watau dawakai) a kan ambaton Ubangijina (watau sallar La’asar) har sai da (rana) ta faxi.”



السورة: Suratun Najm

الآية : 29

فَأَعۡرِضۡ عَن مَّن تَوَلَّىٰ عَن ذِكۡرِنَا وَلَمۡ يُرِدۡ إِلَّا ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا

Sai ka kau da kai daga duk wanda ya ba da baya daga ambatonmu, bai kuma yi nufin komai ba sai rayuwar duniya



السورة: Suratun Najm

الآية : 30

ذَٰلِكَ مَبۡلَغُهُم مِّنَ ٱلۡعِلۡمِۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِمَنِ ٱهۡتَدَىٰ

Wannan ne maqurar iliminsu. Lalle Ubangijinka Shi ne Ya fi sanin wanda ya vace daga hanyarsa kuma Shi Ya fi sanin wanda ya shiriya



السورة: Suratul Jumu’a

الآية : 11

وَإِذَا رَأَوۡاْ تِجَٰرَةً أَوۡ لَهۡوًا ٱنفَضُّوٓاْ إِلَيۡهَا وَتَرَكُوكَ قَآئِمٗاۚ قُلۡ مَا عِندَ ٱللَّهِ خَيۡرٞ مِّنَ ٱللَّهۡوِ وَمِنَ ٱلتِّجَٰرَةِۚ وَٱللَّهُ خَيۡرُ ٱلرَّـٰزِقِينَ

Idan kuma suka ga kasuwanci ko wasa sai su watse zuwa gare su, su bar ka a tsaye (kana huxuba). Ka ce: “Abin da yake wurin Allah ya fi wasa da ciniki. Kuma Allah Fiyayyen masu arzutawa ne.”



السورة: Suratul Munafiqun

الآية : 9

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُلۡهِكُمۡ أَمۡوَٰلُكُمۡ وَلَآ أَوۡلَٰدُكُمۡ عَن ذِكۡرِ ٱللَّهِۚ وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada dukiyoyinku da ‘ya’yanku su shagaltar da ku daga ambaton Allah[1]. Duk wanda ya aikata haka kuwa, to waxannan su ne tavavvu


1- Watau su xauke muku hankali daga salla da sauran farillan Musulunci da zikirin Allah.


السورة: Suratul Qiyama

الآية : 20

كَلَّا بَلۡ تُحِبُّونَ ٱلۡعَاجِلَةَ

Haba, ku dai kawai kuna son duniya ne



السورة: Suratul Insan

الآية : 27

إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ يُحِبُّونَ ٱلۡعَاجِلَةَ وَيَذَرُونَ وَرَآءَهُمۡ يَوۡمٗا ثَقِيلٗا

Lalle waxannan suna son mai gaggawar qarewa (watau duniya), suna kuma watsi da rana mai nauyi[1] a bayansu


1- Watau ranar alqiyama mai cike da wahalhalu da musibu iri-iri.