يُسَبِّحُ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ ٱلۡمَلِكِ ٱلۡقُدُّوسِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَكِيمِ
Duk abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa yana yin tasbihi ga Allah Sarki, Tsarkakakke, Mabuwayi, Mai hikima
يُسَبِّحُ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۖ لَهُ ٱلۡمُلۡكُ وَلَهُ ٱلۡحَمۡدُۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ
Abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa yana tasbihi ga Allah; mulki nasa ne kuma yabo ya tabbata a gare Shi; kuma Shi Mai iko ne a kan komai
تَبَٰرَكَ ٱلَّذِي بِيَدِهِ ٱلۡمُلۡكُ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ
Wanda mulki yake a hannunsa alhairansa sun yawaita, kuma Shi Mai iko ne a kan komai
ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٌ
Wanda Yake da mulkin sammai da qasa. Allah kuma Mai ganin komai ne
مَلِكِ ٱلنَّاسِ
“Sarkin mutane