السورة: Suratul Mumtahana

الآية : 10

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا جَآءَكُمُ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتُ مُهَٰجِرَٰتٖ فَٱمۡتَحِنُوهُنَّۖ ٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِإِيمَٰنِهِنَّۖ فَإِنۡ عَلِمۡتُمُوهُنَّ مُؤۡمِنَٰتٖ فَلَا تَرۡجِعُوهُنَّ إِلَى ٱلۡكُفَّارِۖ لَا هُنَّ حِلّٞ لَّهُمۡ وَلَا هُمۡ يَحِلُّونَ لَهُنَّۖ وَءَاتُوهُم مَّآ أَنفَقُواْۚ وَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ أَن تَنكِحُوهُنَّ إِذَآ ءَاتَيۡتُمُوهُنَّ أُجُورَهُنَّۚ وَلَا تُمۡسِكُواْ بِعِصَمِ ٱلۡكَوَافِرِ وَسۡـَٔلُواْ مَآ أَنفَقۡتُمۡ وَلۡيَسۡـَٔلُواْ مَآ أَنفَقُواْۚ ذَٰلِكُمۡ حُكۡمُ ٱللَّهِ يَحۡكُمُ بَيۡنَكُمۡۖ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, idan muminai mata sun zo muku suna masu yin hijira, sai ku jarraba su; Allah ne Ya fi sanin imaninsu; to idan kuka san cewa su muminai ne, to kada ku mayar da su wurin kafirai; su ba halal ba ne gare su (kafirai), su ma (kafiran) ba halal ba ne a gare su; kuma ku ba su abin da suka kashe. Kuma babu laifi a kanku ku aure su idan kun ba su sadakinsu. Kada kuma ku riqe igiyar auren mata kafirai, ku tambayi abin da kuka kashe, su ma su tambayi abin da suka kashe[1]. Wannan shi ne hukuncin Allah da Yake hukuntawa a tsakaninku. Allah kuma Masani ne, Mai hikima


1- Watau duk matan da suka yi ridda suka gudu zuwa wajen kafirai, to Musulmi su nemi kafiran su biya su abin da suka kashe wajen auren su. Su ma kafiran su nemi Musulmi su biya su sadakin matansu da suka musulunta suka gudo wajen Musulmi.


السورة: Suratux Xalaq

الآية : 1

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ إِذَا طَلَّقۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَطَلِّقُوهُنَّ لِعِدَّتِهِنَّ وَأَحۡصُواْ ٱلۡعِدَّةَۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ رَبَّكُمۡۖ لَا تُخۡرِجُوهُنَّ مِنۢ بُيُوتِهِنَّ وَلَا يَخۡرُجۡنَ إِلَّآ أَن يَأۡتِينَ بِفَٰحِشَةٖ مُّبَيِّنَةٖۚ وَتِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِۚ وَمَن يَتَعَدَّ حُدُودَ ٱللَّهِ فَقَدۡ ظَلَمَ نَفۡسَهُۥۚ لَا تَدۡرِي لَعَلَّ ٱللَّهَ يُحۡدِثُ بَعۡدَ ذَٰلِكَ أَمۡرٗا

Ya kai wannan Annabi, (ka ce da jama’arka): “Idan za ku saki mata sai ku sake su a farkon iddarsu[1], kuma ku kula da kiyaye qidaya idda[2]; kuma ku kiyaye dokokin Ubangijinku; kada ku fitar da su daga xakunansu, su ma kada su fita sai dai idan sun aikata alfasha bayayyananna. Waxannan kuwa su ne iyakokin Allah. Wanda kuwa duk ya qetare iyakokin Allah, to haqiqa ya zalunci kansa. Ba ka sani ba ko Allah zai farar da wani al’amari bayan wannan[3]


1- Watau lokacin da suka yi tsarkin haila wanda kuma ba su sadu da su ba a cikinsa, ko kuma idan ciki ya bayyana.


2- Domin su iya dawo da matansu kafin qarewarta idan suna buqatar yin haka.


3- Watau Allah ya sake kawo jituwa a tsakanin mijin da matar su fahimci juna su mayar da aurensu.


السورة: Suratux Xalaq

الآية : 2

فَإِذَا بَلَغۡنَ أَجَلَهُنَّ فَأَمۡسِكُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٍ أَوۡ فَارِقُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٖ وَأَشۡهِدُواْ ذَوَيۡ عَدۡلٖ مِّنكُمۡ وَأَقِيمُواْ ٱلشَّهَٰدَةَ لِلَّهِۚ ذَٰلِكُمۡ يُوعَظُ بِهِۦ مَن كَانَ يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ وَمَن يَتَّقِ ٱللَّهَ يَجۡعَل لَّهُۥ مَخۡرَجٗا

Idan kuma sun kusa isa qarshen iddarsu, to ku riqe su da kyautatawa (ku yi kome), ko kuma ku rabu da su da kyautatawa, kuma ku kafa shaidar adilai guda biyu daga cikinku, ku kuma tsayar da shaidarku saboda Allah. Wannan shi ne ake yin wa’azi da shi ga wanda ya kasance yana yin imani da Allah da ranar lahira. Wanda kuma ya kiyaye dokokin Allah to zai sanya masa mafita



السورة: Suratux Xalaq

الآية : 3

وَيَرۡزُقۡهُ مِنۡ حَيۡثُ لَا يَحۡتَسِبُۚ وَمَن يَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِ فَهُوَ حَسۡبُهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ بَٰلِغُ أَمۡرِهِۦۚ قَدۡ جَعَلَ ٱللَّهُ لِكُلِّ شَيۡءٖ قَدۡرٗا

Ya kuma arzuta shi ta inda ba ya tsammani. Duk wanda kuma ya dogara ga Allah to Shi Ya ishe shi. Lalle Allah Mai zartar da al’amarinsa ne. Haqiqa kuma Allah Ya sanya iyaka ga kowane abu



السورة: Suratux Xalaq

الآية : 4

وَٱلَّـٰٓـِٔي يَئِسۡنَ مِنَ ٱلۡمَحِيضِ مِن نِّسَآئِكُمۡ إِنِ ٱرۡتَبۡتُمۡ فَعِدَّتُهُنَّ ثَلَٰثَةُ أَشۡهُرٖ وَٱلَّـٰٓـِٔي لَمۡ يَحِضۡنَۚ وَأُوْلَٰتُ ٱلۡأَحۡمَالِ أَجَلُهُنَّ أَن يَضَعۡنَ حَمۡلَهُنَّۚ وَمَن يَتَّقِ ٱللَّهَ يَجۡعَل لَّهُۥ مِنۡ أَمۡرِهِۦ يُسۡرٗا

Waxanda kuma suka xebe qauna ta yin al’ada daga matanku, idan kun yi kokwanto, to iddarsu wata uku ne, da kuma waxanda ba su tava yin al’ada ba. Mata masu ciki kuma qarewar iddarsu ita ce haife cikinsu[1]. Duk kuma wanda ya kiyaye dokokin Allah, to zai sanya masa sauqi game da al’amarinsa


1- Hakanan iddar matar da mijinta ya rasu.


السورة: Suratux Xalaq

الآية : 5

ذَٰلِكَ أَمۡرُ ٱللَّهِ أَنزَلَهُۥٓ إِلَيۡكُمۡۚ وَمَن يَتَّقِ ٱللَّهَ يُكَفِّرۡ عَنۡهُ سَيِّـَٔاتِهِۦ وَيُعۡظِمۡ لَهُۥٓ أَجۡرًا

Wannan shi ne hukuncin Allah da Ya saukar da shi a gare ku. Duk kuma wanda ya kiyaye dokokin Allah, to zai kankare masa zunubbansa Ya kuma girmama masa lada



السورة: Suratux Xalaq

الآية : 6

أَسۡكِنُوهُنَّ مِنۡ حَيۡثُ سَكَنتُم مِّن وُجۡدِكُمۡ وَلَا تُضَآرُّوهُنَّ لِتُضَيِّقُواْ عَلَيۡهِنَّۚ وَإِن كُنَّ أُوْلَٰتِ حَمۡلٖ فَأَنفِقُواْ عَلَيۡهِنَّ حَتَّىٰ يَضَعۡنَ حَمۡلَهُنَّۚ فَإِنۡ أَرۡضَعۡنَ لَكُمۡ فَـَٔاتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ وَأۡتَمِرُواْ بَيۡنَكُم بِمَعۡرُوفٖۖ وَإِن تَعَاسَرۡتُمۡ فَسَتُرۡضِعُ لَهُۥٓ أُخۡرَىٰ

Ku zaunar da su (matayen) a inda kuka zauna daidai da samunku, kada kuma ku cuce su don ku quntata musu. Idan kuwa sun kasance masu ciki to sai ku ciyar da su har sai sun haife cikinsu. Sannan idan sun shayar muku da (‘ya’yanku) sai ku ba su ladansu; ku kuma daidaita a tsakaninku ta hanya tagari; idan kuma kuka kasa daidaitawa, to wata mai shayarwar sai ta shayar masa



السورة: Suratux Xalaq

الآية : 7

لِيُنفِقۡ ذُو سَعَةٖ مِّن سَعَتِهِۦۖ وَمَن قُدِرَ عَلَيۡهِ رِزۡقُهُۥ فَلۡيُنفِقۡ مِمَّآ ءَاتَىٰهُ ٱللَّهُۚ لَا يُكَلِّفُ ٱللَّهُ نَفۡسًا إِلَّا مَآ ءَاتَىٰهَاۚ سَيَجۡعَلُ ٱللَّهُ بَعۡدَ عُسۡرٖ يُسۡرٗا

Mawadaci ya ciyar daidai da wadatarsa; wanda kuwa aka quntata masa arzikinsa, to ya ciyar daidai da abin da Allah Ya ba shi. Allah ba Ya xora wa rai sai gwargwadon abin da Ya ba shi. Kuma da sannu Allah zai sanya sauqi bayan tsanani



السورة: Suratul Bayyina

الآية : 5

وَمَآ أُمِرُوٓاْ إِلَّا لِيَعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ حُنَفَآءَ وَيُقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُواْ ٱلزَّكَوٰةَۚ وَذَٰلِكَ دِينُ ٱلۡقَيِّمَةِ

Ba a kuma umarce su ba sai don su bauta wa Allah suna masu tsantsanta addini gare Shi, suna masu kauce wa varna, suna kuma tsayar da salla, kuma suna ba da zakka. Wannan kuwa shi ne addinin miqaqqiyar hanya