ٱذۡهَبُواْ بِقَمِيصِي هَٰذَا فَأَلۡقُوهُ عَلَىٰ وَجۡهِ أَبِي يَأۡتِ بَصِيرٗا وَأۡتُونِي بِأَهۡلِكُمۡ أَجۡمَعِينَ
“Ku tafi da rigata wannan sannan ku jefa ta a fuskar babana, zai dawo mai gani, ku kuma zo min da iyalanku gaba xaya.”
وَلَمَّا فَصَلَتِ ٱلۡعِيرُ قَالَ أَبُوهُمۡ إِنِّي لَأَجِدُ رِيحَ يُوسُفَۖ لَوۡلَآ أَن تُفَنِّدُونِ
Lokacin da ayarin ya baro (Masar) sai babansu ya ce: “Lalle ina jin qanshin Yusufu; ba don dai kada ku ce na susuce ba!”
قَالُواْ تَٱللَّهِ إِنَّكَ لَفِي ضَلَٰلِكَ ٱلۡقَدِيمِ
Suka ce: “Wallahi mun tabbata ba shakka (har yanzu) kana nan cikin daxaxxiyar rikicewar nan taka!”
فَلَمَّآ أَن جَآءَ ٱلۡبَشِيرُ أَلۡقَىٰهُ عَلَىٰ وَجۡهِهِۦ فَٱرۡتَدَّ بَصِيرٗاۖ قَالَ أَلَمۡ أَقُل لَّكُمۡ إِنِّيٓ أَعۡلَمُ مِنَ ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ
To lokacin da mai albishir ya zo masa sai ya jefa ta (rigar) a fuskarsa, sai ya dawo yana gani. Ya ce: “Ban gaya muku ba cewa lalle ni na san abin da ku ba ku sani ba game da Allah?”
قَالُواْ يَـٰٓأَبَانَا ٱسۡتَغۡفِرۡ لَنَا ذُنُوبَنَآ إِنَّا كُنَّا خَٰطِـِٔينَ
Suka ce: “Ya babanmu, ka nema mana gafarar zunubanmu, lalle mun zamanto masu kuskure!”
قَالَ سَوۡفَ أَسۡتَغۡفِرُ لَكُمۡ رَبِّيٓۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ
Ya ce: “Ba da daxewa ba zan nema muku gafarar Ubangijina; lalle Shi ne Mai yawan gafara, Mai jin qai.”
فَلَمَّا دَخَلُواْ عَلَىٰ يُوسُفَ ءَاوَىٰٓ إِلَيۡهِ أَبَوَيۡهِ وَقَالَ ٱدۡخُلُواْ مِصۡرَ إِن شَآءَ ٱللَّهُ ءَامِنِينَ
Lokacin da suka shiga wurin Yusufu sai ya jawo iyayensa ya kuma ce: “Ku shigo Masar in Allah Ya ga dama kuna amintattu.”
وَرَفَعَ أَبَوَيۡهِ عَلَى ٱلۡعَرۡشِ وَخَرُّواْ لَهُۥ سُجَّدٗاۖ وَقَالَ يَـٰٓأَبَتِ هَٰذَا تَأۡوِيلُ رُءۡيَٰيَ مِن قَبۡلُ قَدۡ جَعَلَهَا رَبِّي حَقّٗاۖ وَقَدۡ أَحۡسَنَ بِيٓ إِذۡ أَخۡرَجَنِي مِنَ ٱلسِّجۡنِ وَجَآءَ بِكُم مِّنَ ٱلۡبَدۡوِ مِنۢ بَعۡدِ أَن نَّزَغَ ٱلشَّيۡطَٰنُ بَيۡنِي وَبَيۡنَ إِخۡوَتِيٓۚ إِنَّ رَبِّي لَطِيفٞ لِّمَا يَشَآءُۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡعَلِيمُ ٱلۡحَكِيمُ
Ya kuma xora mahaifansa a kan gadon mulki, suka kuma faxi suna masu gaisuwa a gare shi, ya kuma ce: “Ya babanmu, wannan shi ne fassarar mafarkina na tun tuni. Lalle Ubangijina Ya mai da shi gaskiya; haqiqa kuma Ya kyautata min lokacin da Ya fitar da ni daga kurkuku, Ya kuma zo da ku daga qauye bayan Shaixan ya shiga tsakanina da ‘yan’uwana. Lalle Ubangijina Mai tausasawa ne ga wanda Ya ga dama. Lalle Shi ne Masani, Mai hikima
۞رَبِّ قَدۡ ءَاتَيۡتَنِي مِنَ ٱلۡمُلۡكِ وَعَلَّمۡتَنِي مِن تَأۡوِيلِ ٱلۡأَحَادِيثِۚ فَاطِرَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ أَنتَ وَلِيِّۦ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۖ تَوَفَّنِي مُسۡلِمٗا وَأَلۡحِقۡنِي بِٱلصَّـٰلِحِينَ
“Ya Ubangijina, haqiqa Ka ba ni wani abu na mulki, Ka kuma sanar da ni wani abu daga fassarar mafarki; Ya Mahaliccin sammai da qasa, Kai ne Majivincina a duniya da lahira; ka karvi raina ina Musulmi, Ka kuma haxa ni da (mutane) salihai.”