۞إِنَّآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ كَمَآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ نُوحٖ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ مِنۢ بَعۡدِهِۦۚ وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطِ وَعِيسَىٰ وَأَيُّوبَ وَيُونُسَ وَهَٰرُونَ وَسُلَيۡمَٰنَۚ وَءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ زَبُورٗا
Lalle Mun yi maka wahayi irin wahayin da Muka yi wa Nuhu da kuma annabawan da suka biyo bayansa, kuma Mun yi wahayi ga Ibrahimu da Isma’ila da Ishaqa da Ya’aqubu da kuma jikokin (Ya’aqubu) da Isa da Ayyuba da Yunusa da Haruna da Sulaimanu; kuma Muka bai wa Dawuda littafin Zabura
وَإِسۡمَٰعِيلَ وَٱلۡيَسَعَ وَيُونُسَ وَلُوطٗاۚ وَكُلّٗا فَضَّلۡنَا عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ
Da Isma’ilu da Alyasa’u da Yunusu da Luxu. Kowanne daga cikinsu kuma Mun fifita shi a kan (sauran) talikai
فَلَوۡلَا كَانَتۡ قَرۡيَةٌ ءَامَنَتۡ فَنَفَعَهَآ إِيمَٰنُهَآ إِلَّا قَوۡمَ يُونُسَ لَمَّآ ءَامَنُواْ كَشَفۡنَا عَنۡهُمۡ عَذَابَ ٱلۡخِزۡيِ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَمَتَّعۡنَٰهُمۡ إِلَىٰ حِينٖ
Babu wasu mutane na wata alqarya da suka yi imani, sannan imaninsu ya amfane su, sai fa mutanen Yunusa, lokacin da suka yi imani sai Muka yaye musu azabar wulaqanci a rayuwar duniya, Muka kuma jiyar da su daxi har zuwa wani lokaci (iyakantacce)
وَذَا ٱلنُّونِ إِذ ذَّهَبَ مُغَٰضِبٗا فَظَنَّ أَن لَّن نَّقۡدِرَ عَلَيۡهِ فَنَادَىٰ فِي ٱلظُّلُمَٰتِ أَن لَّآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنتَ سُبۡحَٰنَكَ إِنِّي كُنتُ مِنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Kuma (ka tuna) ma’abocin kifi (wato Yunusa) lokacin da ya tafi yana cike da fushi[1], sannan ya zaci cewa ba za Mu quntata masa ba, sai ya kira (Mu) a cikin duffai[2] yana cewa: “Ba wani abin bauta da gaskiya sai Kai (ya Allah), tsarki ya tabbata a gare Ka, lallai ni na kasance cikin azzalumai!”
1-  Watau saboda mutanensa sun kafe a kan kafirci sun qi yin imani.
2-  Watau duhun dare da duhun kogi da duhun cikin kifi.            
فَٱسۡتَجَبۡنَا لَهُۥ وَنَجَّيۡنَٰهُ مِنَ ٱلۡغَمِّۚ وَكَذَٰلِكَ نُـۨجِي ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Sai Muka amsa masa Muka kuma tserar da shi daga baqin ciki. Kamar haka kuwa Muke tserar da muminai
وَإِنَّ يُونُسَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Kuma lalle Yunusa tabbas yana daga cikin manzanni
إِذۡ أَبَقَ إِلَى ٱلۡفُلۡكِ ٱلۡمَشۡحُونِ
(Ka tuna) lokacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwan da yake maqare
فَسَاهَمَ فَكَانَ مِنَ ٱلۡمُدۡحَضِينَ
Sannan ya shiga quri’a, sai ya zama cikin waxanda aka yi galaba a kansu
فَٱلۡتَقَمَهُ ٱلۡحُوتُ وَهُوَ مُلِيمٞ
Sai kifi ya haxiye shi, alhali yana abin zargi[1]
1- Watau a kan guduwa ya bar mutanensa ba tare da izinin Allah ba.
فَلَوۡلَآ أَنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلۡمُسَبِّحِينَ
Ba don dai shi ya zama daga masu tsarkake Allah (da yawan tasbihi) ba
لَلَبِثَ فِي بَطۡنِهِۦٓ إِلَىٰ يَوۡمِ يُبۡعَثُونَ
Tabbas da ya zauna a cikin cikinsa har zuwa ranar da za a tashe su[1]
1- Watau ranar alqiyama, domin zai zama shi ne qabarinsa.
۞فَنَبَذۡنَٰهُ بِٱلۡعَرَآءِ وَهُوَ سَقِيمٞ
Sai Muka jefa shi a tudu, a halin yana cikin rashin lafiya
وَأَنۢبَتۡنَا عَلَيۡهِ شَجَرَةٗ مِّن يَقۡطِينٖ
Muka kuma tsirar masa wata bishiya ta kabewa[1]
1- Domin ya rufe tsiraicinsa da ganyenta, ya kuma ci ‘ya’yanta, ya kuma sha inuwarta.
وَأَرۡسَلۡنَٰهُ إِلَىٰ مِاْئَةِ أَلۡفٍ أَوۡ يَزِيدُونَ
Muka kuma aika shi zuwa ga mutum dubu xari, ko kuma sama da haka
فَـَٔامَنُواْ فَمَتَّعۡنَٰهُمۡ إِلَىٰ حِينٖ
Sai suka yi imani, sai Muka jiyar da su daxi har zuwa wani lokaci
فَٱصۡبِرۡ لِحُكۡمِ رَبِّكَ وَلَا تَكُن كَصَاحِبِ ٱلۡحُوتِ إِذۡ نَادَىٰ وَهُوَ مَكۡظُومٞ
To ka yi haquri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar ma’abocin kifi (Yunus) a yayin da ya yi kira, alhali shi yana cike da baqin ciki
لَّوۡلَآ أَن تَدَٰرَكَهُۥ نِعۡمَةٞ مِّن رَّبِّهِۦ لَنُبِذَ بِٱلۡعَرَآءِ وَهُوَ مَذۡمُومٞ
Ba don wata rahama daga Ubangijinsa ta riske shi ba, da an jefar da shi a qungurmin daji alhali shi yana abin suka
فَٱجۡتَبَٰهُ رَبُّهُۥ فَجَعَلَهُۥ مِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ
Sai Ubangijinsa Ya zave shi Ya sanya shi daga (bayi) nagari