السورة: Suratun Nisa’i

الآية : 163

۞إِنَّآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ كَمَآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ نُوحٖ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ مِنۢ بَعۡدِهِۦۚ وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطِ وَعِيسَىٰ وَأَيُّوبَ وَيُونُسَ وَهَٰرُونَ وَسُلَيۡمَٰنَۚ وَءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ زَبُورٗا

Lalle Mun yi maka wahayi irin wahayin da Muka yi wa Nuhu da kuma annabawan da suka biyo bayansa, kuma Mun yi wahayi ga Ibrahimu da Isma’ila da Ishaqa da Ya’aqubu da kuma jikokin (Ya’aqubu) da Isa da Ayyuba da Yunusa da Haruna da Sulaimanu; kuma Muka bai wa Dawuda littafin Zabura



السورة: Suratul An’am

الآية : 84

وَوَهَبۡنَا لَهُۥٓ إِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَۚ كُلًّا هَدَيۡنَاۚ وَنُوحًا هَدَيۡنَا مِن قَبۡلُۖ وَمِن ذُرِّيَّتِهِۦ دَاوُۥدَ وَسُلَيۡمَٰنَ وَأَيُّوبَ وَيُوسُفَ وَمُوسَىٰ وَهَٰرُونَۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Kuma Muka ba shi Ishaqa da Ya’aqubu. Kowanne daga cikinsu Mun shiryar da shi, kuma Mun shiryar da Nuhu tun gabaninsu. Kuma daga cikin zurriyarsa akwai Dawudu da Sulaimanu da Ayyuba da Yusufu da Musa da Haruna. Kuma kamar haka ne Muke saka wa masu kyautata (ayyukansu)



السورة: Suratul Anbiya

الآية : 83

۞وَأَيُّوبَ إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥٓ أَنِّي مَسَّنِيَ ٱلضُّرُّ وَأَنتَ أَرۡحَمُ ٱلرَّـٰحِمِينَ

Kuma (ka tuna) Ayyuba lokacin da ya roqi Ubangijinsa (yana cewa): “Lallai cuta ta same ni, Kai ne kuwa Mafi jin qan masu jin qai!”



السورة: Suratul Anbiya

الآية : 84

فَٱسۡتَجَبۡنَا لَهُۥ فَكَشَفۡنَا مَا بِهِۦ مِن ضُرّٖۖ وَءَاتَيۡنَٰهُ أَهۡلَهُۥ وَمِثۡلَهُم مَّعَهُمۡ رَحۡمَةٗ مِّنۡ عِندِنَا وَذِكۡرَىٰ لِلۡعَٰبِدِينَ

Sai Muka amsa masa (roqonsa) sannan Muka yaye cutar da take tare da shi, Muka kuma ba shi (madadin) iyalinsa (da ya rasa) da kuma kwatankwacinsu tare da su don jin qai daga gare Mu da kuma wa’azi ga masu bauta (ga Allah)



السورة: Suratu Sad

الآية : 41

وَٱذۡكُرۡ عَبۡدَنَآ أَيُّوبَ إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥٓ أَنِّي مَسَّنِيَ ٱلشَّيۡطَٰنُ بِنُصۡبٖ وَعَذَابٍ

Ka kuma tuna bawanmu Ayyuba lokacin da ya kira Ubangijinsa (yana cewa): “Lalle ni Shaixan ya shafe ni da wata wahala da azaba.”



السورة: Suratu Sad

الآية : 42

ٱرۡكُضۡ بِرِجۡلِكَۖ هَٰذَا مُغۡتَسَلُۢ بَارِدٞ وَشَرَابٞ

(Aka ce da shi): “Ka hauri qasa da qafarka; (sai ruwa ya vuvvugo, aka ce da shi): “Wannan ruwan wanka ne mai sanyi da na sha.”



السورة: Suratu Sad

الآية : 43

وَوَهَبۡنَا لَهُۥٓ أَهۡلَهُۥ وَمِثۡلَهُم مَّعَهُمۡ رَحۡمَةٗ مِّنَّا وَذِكۡرَىٰ لِأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ

Muka kuma yi masa baiwar iyalinsa da kuma (qarin) wasu kamarsu (na `ya`ya da jikoki) don jin qai daga gare Mu da kuma wa’azi ga masu hankula



السورة: Suratu Sad

الآية : 44

وَخُذۡ بِيَدِكَ ضِغۡثٗا فَٱضۡرِب بِّهِۦ وَلَا تَحۡنَثۡۗ إِنَّا وَجَدۡنَٰهُ صَابِرٗاۚ نِّعۡمَ ٱلۡعَبۡدُ إِنَّهُۥٓ أَوَّابٞ

Ka xauki danqi na ciyawa da hannunka ka bugi (matarka da shi)[1], kada ka karya rantsuwarka. Lalle Mun same shi mai haquri. Madalla da wannan bawan; lalle shi mai yawan komawa ne (ga Allah)


1- Yayin da matarsa ta yi masa laifi ya yi rantsuwa cewa, idan ya warke sai ya yi mata bulala xari. Allah () ya umarce shi da ya cika rantsuwarsa ta wannan hanyar.