۞يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡخَمۡرِ وَٱلۡمَيۡسِرِۖ قُلۡ فِيهِمَآ إِثۡمٞ كَبِيرٞ وَمَنَٰفِعُ لِلنَّاسِ وَإِثۡمُهُمَآ أَكۡبَرُ مِن نَّفۡعِهِمَاۗ وَيَسۡـَٔلُونَكَ مَاذَا يُنفِقُونَۖ قُلِ ٱلۡعَفۡوَۗ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمُ ٱلۡأٓيَٰتِ لَعَلَّكُمۡ تَتَفَكَّرُونَ
Suna tambayar ka game da giya da caca. Ka ce: “A cikin lamarinsu akwai zunubi mai girma da kuma waxansu amfanunnuka ga mutane. Amma zunubinsu ya fi amfaninsu girma”[1] Kuma suna tambayar ka, me za su ciyar? Ka ce: “Abin da ya daxu a kan buqatunku.” Kamar haka ne Allah Yake muku bayanin ayoyi don ku yi tunani
1- Wannan matakin farko ne na tsawatarwa game da giya. Allah ya haramta giya gaba xaya a Suratul Ma’ida, aya ta 90-91
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّمَا ٱلۡخَمۡرُ وَٱلۡمَيۡسِرُ وَٱلۡأَنصَابُ وَٱلۡأَزۡلَٰمُ رِجۡسٞ مِّنۡ عَمَلِ ٱلشَّيۡطَٰنِ فَٱجۡتَنِبُوهُ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ
Ya ku waxanda suka yi imani, ita dai giya da caca da gumaka da kibau na neman sa’a[1], ba komai ba ne face qazanta daga aikin Shaixan, don haka ku nisance su domin ku sami rabauta.[2]
1-  A jahiliyya balarabe idan zai yi tafiya ko zai yi wani aiki, sai ya xauko wasu kibiyoyi uku, xaya an rubuta ‘aikata’, xaya kuma ‘kada ka aikata’, ta uku kuma ba a rubuta komai a kanta ba, sai ya karkaxa su sannan ya zavi xaya don ya gane sa’arsa ko rashinta.
2-  Da wannan ayar Allah () ya haramta wa Musulmi shan giya da kasuwancinta.            
إِنَّمَا يُرِيدُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَن يُوقِعَ بَيۡنَكُمُ ٱلۡعَدَٰوَةَ وَٱلۡبَغۡضَآءَ فِي ٱلۡخَمۡرِ وَٱلۡمَيۡسِرِ وَيَصُدَّكُمۡ عَن ذِكۡرِ ٱللَّهِ وَعَنِ ٱلصَّلَوٰةِۖ فَهَلۡ أَنتُم مُّنتَهُونَ
Abin da kawai Shaixan yake nufi shi ne, ya jefa gaba da qiyayya a tsakankaninku, ta hanyar giya da caca, kuma ya hana muku ambaton Allah da yin salla. Shin ko kun hanu?