السورة: Suratu Xa Ha

الآية : 117

فَقُلۡنَا يَـٰٓـَٔادَمُ إِنَّ هَٰذَا عَدُوّٞ لَّكَ وَلِزَوۡجِكَ فَلَا يُخۡرِجَنَّكُمَا مِنَ ٱلۡجَنَّةِ فَتَشۡقَىٰٓ

Sannan Muka ce: “Ya Adamu, lalle wannan maqiyinka ne kai da matarka, to kada (ku yarda) ya fitar da ku daga Aljanna, sai ka wahala



السورة: Suratu Xa Ha

الآية : 118

إِنَّ لَكَ أَلَّا تَجُوعَ فِيهَا وَلَا تَعۡرَىٰ

“Lalle (Allah) Ya yi maka alqawarin ba za ka ji yunwa ba a cikinta, kuma ba za ka yi tsiraici ba



السورة: Suratu Xa Ha

الآية : 119

وَأَنَّكَ لَا تَظۡمَؤُاْ فِيهَا وَلَا تَضۡحَىٰ

“Kuma lalle kai ba za ka ji qishi ba a cikinta, kuma ba za ka ji zafin rana ba.”



السورة: Suratu Xa Ha

الآية : 120

فَوَسۡوَسَ إِلَيۡهِ ٱلشَّيۡطَٰنُ قَالَ يَـٰٓـَٔادَمُ هَلۡ أَدُلُّكَ عَلَىٰ شَجَرَةِ ٱلۡخُلۡدِ وَمُلۡكٖ لَّا يَبۡلَىٰ

Sai Shaixan ya yi masa waswasi ya ce: “Ya Adamu, yanzu ba na nuna maka wata bishiya ta dawwama da kuma mulki wanda ba zai qare ba?”



السورة: Suratu Saba’i

الآية : 20

وَلَقَدۡ صَدَّقَ عَلَيۡهِمۡ إِبۡلِيسُ ظَنَّهُۥ فَٱتَّبَعُوهُ إِلَّا فَرِيقٗا مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Kuma haqiqa Iblisu ya tabbatar da zatonsa a kansu gaskiya ne[1], sai suka bi shi, in ban da wata qungiya ta muminai


1- Watau na cewa zai iya vatar da su ya raba su da gaskiya.


السورة: Suratu Saba’i

الآية : 21

وَمَا كَانَ لَهُۥ عَلَيۡهِم مِّن سُلۡطَٰنٍ إِلَّا لِنَعۡلَمَ مَن يُؤۡمِنُ بِٱلۡأٓخِرَةِ مِمَّنۡ هُوَ مِنۡهَا فِي شَكّٖۗ وَرَبُّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٍ حَفِيظٞ

Shi kuwa ba shi da wani qarfi a kansu, sai dai (Mun yi haka ne) don Mu bayyana wanda yake imani da ranar lahira da kuma wanda yake cikin shakka game da ita. Ubangijinka kuwa Mai kiyaye komai ne



السورة: Suratu Sad

الآية : 71

إِذۡ قَالَ رَبُّكَ لِلۡمَلَـٰٓئِكَةِ إِنِّي خَٰلِقُۢ بَشَرٗا مِّن طِينٖ

(Ka tuna) lokacin da Ubangijinka Ya ce da mala’iku: “Lalle Ni zan halicci wani mutum daga tavo



السورة: Suratu Sad

الآية : 72

فَإِذَا سَوَّيۡتُهُۥ وَنَفَخۡتُ فِيهِ مِن رُّوحِي فَقَعُواْ لَهُۥ سَٰجِدِينَ

“To idan Na daidaita shi Na kuma busa masa ruhina, sai ku faxi kuna masu yi masa sujjada.”



السورة: Suratu Sad

الآية : 73

فَسَجَدَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ كُلُّهُمۡ أَجۡمَعُونَ

Sai mala’iku dukkaninsu gaba xaya suka yi sujjada



السورة: Suratu Sad

الآية : 74

إِلَّآ إِبۡلِيسَ ٱسۡتَكۡبَرَ وَكَانَ مِنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Sai Iblisa da ya yi girman kai ya kuma zama cikin kafirai



السورة: Suratu Sad

الآية : 75

قَالَ يَـٰٓإِبۡلِيسُ مَا مَنَعَكَ أَن تَسۡجُدَ لِمَا خَلَقۡتُ بِيَدَيَّۖ أَسۡتَكۡبَرۡتَ أَمۡ كُنتَ مِنَ ٱلۡعَالِينَ

(Allah) Ya ce: “Ya kai Iblisa, me ya hana ka yin sujjada ga abin da Na halitta da hannayena biyu? Ka yi girman kai ne, ko kuwa da man can ka kasance daga masu nuna isa?”



السورة: Suratu Sad

الآية : 76

قَالَ أَنَا۠ خَيۡرٞ مِّنۡهُ خَلَقۡتَنِي مِن نَّارٖ وَخَلَقۡتَهُۥ مِن طِينٖ

Sai ya ce: “Ni ai na fi shi; (domin) Ka halicce ni ne daga wuta, (shi) kuma Ka halicce shi daga tavo.”



السورة: Suratu Sad

الآية : 77

قَالَ فَٱخۡرُجۡ مِنۡهَا فَإِنَّكَ رَجِيمٞ

(Sai Allah) Ya ce (da shi): “To ka fice daga cikinta (wato Aljanna) saboda kai lalle korarre ne (daga rahama)



السورة: Suratu Sad

الآية : 78

وَإِنَّ عَلَيۡكَ لَعۡنَتِيٓ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلدِّينِ

“Kuma lalle la’antata tabbas ta hau kanka har zuwa ranar alqiyama.”



السورة: Suratu Sad

الآية : 79

قَالَ رَبِّ فَأَنظِرۡنِيٓ إِلَىٰ يَوۡمِ يُبۡعَثُونَ

(Sai Iblisa) ya ce: “Ya Ubangijina, Ka saurara min har zuwa ranar da za a tashe su.”



السورة: Suratu Sad

الآية : 80

قَالَ فَإِنَّكَ مِنَ ٱلۡمُنظَرِينَ

(Sai Allah) Ya ce: “To lalle kana cikin waxanda za a saurara wa



السورة: Suratu Sad

الآية : 81

إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡوَقۡتِ ٱلۡمَعۡلُومِ

“Har zuwa ranar lokaci sananne.”



السورة: Suratu Sad

الآية : 82

قَالَ فَبِعِزَّتِكَ لَأُغۡوِيَنَّهُمۡ أَجۡمَعِينَ

Sai ya ce: “To na rantse da girmanka tabbas zan vatar da su baki xaya



السورة: Suratu Sad

الآية : 83

إِلَّا عِبَادَكَ مِنۡهُمُ ٱلۡمُخۡلَصِينَ

“Sai dai bayinka waxanda aka tsarkake daga cikinsu.”



السورة: Suratu Sad

الآية : 84

قَالَ فَٱلۡحَقُّ وَٱلۡحَقَّ أَقُولُ

(Allah) Ya ce: “Gaskiya (daga gare Ni take), kuma gaskiyar kawai Nake faxa!



السورة: Suratu Sad

الآية : 85

لَأَمۡلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنكَ وَمِمَّن تَبِعَكَ مِنۡهُمۡ أَجۡمَعِينَ

“Tabbas zan cika Jahannama da kai da kuma waxanda suka bi ka baki xaya.”



السورة: Suratul Jinn

الآية : 4

وَأَنَّهُۥ كَانَ يَقُولُ سَفِيهُنَا عَلَى ٱللَّهِ شَطَطٗا

“Kuma lalle yadda lamarin yake, wani wawa daga cikinmu ya kasance yana faxar mummunar qarya game da Allah