السورة: Suratun Nisa’i

الآية : 145

إِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ فِي ٱلدَّرۡكِ ٱلۡأَسۡفَلِ مِنَ ٱلنَّارِ وَلَن تَجِدَ لَهُمۡ نَصِيرًا

Lalle munafuqai suna cikin matakin qarshe na can qarqashin wuta, kuma ba za ka tava sama musu wani mataimaki ba



السورة: Suratut Tauba

الآية : 64

يَحۡذَرُ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ أَن تُنَزَّلَ عَلَيۡهِمۡ سُورَةٞ تُنَبِّئُهُم بِمَا فِي قُلُوبِهِمۡۚ قُلِ ٱسۡتَهۡزِءُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ مُخۡرِجٞ مَّا تَحۡذَرُونَ

Munafukai suna tsoron a saukar musu da wata sura mai ba su labarin abin da yake cikin zukatansu. Ka ce: “Ku yi ta izgili, lalle Allah Mai bayyana abin da kuke tsoron (bayyanarsa) ne.”



السورة: Suratut Tauba

الآية : 65

وَلَئِن سَأَلۡتَهُمۡ لَيَقُولُنَّ إِنَّمَا كُنَّا نَخُوضُ وَنَلۡعَبُۚ قُلۡ أَبِٱللَّهِ وَءَايَٰتِهِۦ وَرَسُولِهِۦ كُنتُمۡ تَسۡتَهۡزِءُونَ

Kuma lalle idan har ka tambaye su, tabbas za su ce: “Kawai muna kutse ne da wasa.” To ka ce (da su): “Yanzu Allah ne da ayoyinsa da Manzonsa kuka kasance kuna yi wa izgili?”



السورة: Suratut Tauba

الآية : 66

لَا تَعۡتَذِرُواْ قَدۡ كَفَرۡتُم بَعۡدَ إِيمَٰنِكُمۡۚ إِن نَّعۡفُ عَن طَآئِفَةٖ مِّنكُمۡ نُعَذِّبۡ طَآئِفَةَۢ بِأَنَّهُمۡ كَانُواْ مُجۡرِمِينَ

Kada ku kawo wani uziri, haqiqa kun dai kafirta bayan imaninku. Idan Muka yafe wa wata qungiya daga cikinku to za Mu azabtar da wata qungiyar saboda kuwa sun kasance masu laifi ne



السورة: Suratut Tauba

الآية : 67

ٱلۡمُنَٰفِقُونَ وَٱلۡمُنَٰفِقَٰتُ بَعۡضُهُم مِّنۢ بَعۡضٖۚ يَأۡمُرُونَ بِٱلۡمُنكَرِ وَيَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَقۡبِضُونَ أَيۡدِيَهُمۡۚ نَسُواْ ٱللَّهَ فَنَسِيَهُمۡۚ إِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ

Munafukai maza da munafukai mata sun yi kama da juna (wajen munafunci). Suna umurni da mummunan aiki suna kuma hana kyakkyawan aiki, kuma suna damqe hannayensu (wajen yin alheri); sun manta da Allah, sai Shi ma Ya yi watsi da su. Lalle munafikai su ne fasiqai



السورة: Suratut Tauba

الآية : 68

وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱلۡمُنَٰفِقَٰتِ وَٱلۡكُفَّارَ نَارَ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ هِيَ حَسۡبُهُمۡۚ وَلَعَنَهُمُ ٱللَّهُۖ وَلَهُمۡ عَذَابٞ مُّقِيمٞ

Allah kuwa Ya yi wa munafukai maza da mata da kuma kafirai alqawarin wutar Jahannama wadda za su dawwama a cikinta. Ita ta ishe su. Allah kuma Ya tsine musu, suna kuma da azaba mai xorewa



السورة: Suratut Tauba

الآية : 69

كَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ كَانُوٓاْ أَشَدَّ مِنكُمۡ قُوَّةٗ وَأَكۡثَرَ أَمۡوَٰلٗا وَأَوۡلَٰدٗا فَٱسۡتَمۡتَعُواْ بِخَلَٰقِهِمۡ فَٱسۡتَمۡتَعۡتُم بِخَلَٰقِكُمۡ كَمَا ٱسۡتَمۡتَعَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُم بِخَلَٰقِهِمۡ وَخُضۡتُمۡ كَٱلَّذِي خَاضُوٓاْۚ أُوْلَـٰٓئِكَ حَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ

(Kun yi) kama da waxanda suke gabaninku; sun fi ku qarfi da yawan dukiyoyi da kuma ’ya’ya; sai suka more rabonsu (na duniya), to ku ma sai kuka more da naku rabon, kamar yadda waxanda suke gabaninku suka more da irin nasu rabon, kuka kuma kutsa (cikin varna) kamar yadda suka kutsa. Waxannan, ayyukansu sun ruguje a duniya da lahira. Waxannan kuwa su ne hasararru



السورة: Suratut Tauba

الآية : 73

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ جَٰهِدِ ٱلۡكُفَّارَ وَٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱغۡلُظۡ عَلَيۡهِمۡۚ وَمَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

Ya kai wannan Annabi, ka yaqi kafirai da munafukai ka kuma tsananta musu. Jahannama ce kuma makomarsu. Makoma kuwa ta munana



السورة: Suratut Tauba

الآية : 74

يَحۡلِفُونَ بِٱللَّهِ مَا قَالُواْ وَلَقَدۡ قَالُواْ كَلِمَةَ ٱلۡكُفۡرِ وَكَفَرُواْ بَعۡدَ إِسۡلَٰمِهِمۡ وَهَمُّواْ بِمَا لَمۡ يَنَالُواْۚ وَمَا نَقَمُوٓاْ إِلَّآ أَنۡ أَغۡنَىٰهُمُ ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥ مِن فَضۡلِهِۦۚ فَإِن يَتُوبُواْ يَكُ خَيۡرٗا لَّهُمۡۖ وَإِن يَتَوَلَّوۡاْ يُعَذِّبۡهُمُ ٱللَّهُ عَذَابًا أَلِيمٗا فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۚ وَمَا لَهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مِن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٖ

Suna rantsewa da Allah kan ba su faxi (komai) ba, alhali kuwa tabbas sun faxi kalmar kafirci, suka kuma kafirta bayan musuluntarsu, suka kuma yi qudirin aikata abin da ba su samu (dama) ba[1]; ba kuwa abin da suke jin haushi sai kawai don Allah da Manzonsa sun wadata su daga falalarsa. To idan suka tuba zai fi musu alheri; idan kuwa suka juya baya to Allah zai azabtar da su azaba mai raxaxi a duniya da lahira; ba su da kuwa wani majivincin lamari ko wani mataimaki a bayan qasa


1- Watau mugun shirinsu na kashe Annabi () lokacin da yake komawa Madina daga yaqin Tabuka.


السورة: Suratut Tauba

الآية : 75

۞وَمِنۡهُم مَّنۡ عَٰهَدَ ٱللَّهَ لَئِنۡ ءَاتَىٰنَا مِن فَضۡلِهِۦ لَنَصَّدَّقَنَّ وَلَنَكُونَنَّ مِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

Daga cikinsu kuma akwai waxanda suka yi wa Allah alqawarin cewa: “Idan Ya arzuta mu daga falalarsa, to lalle tabbas za mu riqa ba da sadaka, kuma lalle tabbas za mu zama cikin mutane salihai.”



السورة: Suratut Tauba

الآية : 76

فَلَمَّآ ءَاتَىٰهُم مِّن فَضۡلِهِۦ بَخِلُواْ بِهِۦ وَتَوَلَّواْ وَّهُم مُّعۡرِضُونَ

To lokacin da Ya arzuta su xin sai suka yi rowa da ita (sadakar) suka kuma ba da baya suna masu bijirewa



السورة: Suratut Tauba

الآية : 77

فَأَعۡقَبَهُمۡ نِفَاقٗا فِي قُلُوبِهِمۡ إِلَىٰ يَوۡمِ يَلۡقَوۡنَهُۥ بِمَآ أَخۡلَفُواْ ٱللَّهَ مَا وَعَدُوهُ وَبِمَا كَانُواْ يَكۡذِبُونَ

Sai Ya gadar musu da munafunci a cikin zukatansu har zuwa ranar da za su gamu da Shi, saboda sava wa alqawarin da suka yi wa Allah da kuma qaryatawar da suka zamanto suna yi



السورة: Suratut Tauba

الآية : 78

أَلَمۡ يَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ سِرَّهُمۡ وَنَجۡوَىٰهُمۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ عَلَّـٰمُ ٱلۡغُيُوبِ

Yanzu ba su sani ba cewa, lalle Allah Ya san asirinsu da kuma ganawar da suke yi, lalle kuma Allah Shi ne cikakken Masanin gaibu?



السورة: Suratut Tauba

الآية : 79

ٱلَّذِينَ يَلۡمِزُونَ ٱلۡمُطَّوِّعِينَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ فِي ٱلصَّدَقَٰتِ وَٱلَّذِينَ لَا يَجِدُونَ إِلَّا جُهۡدَهُمۡ فَيَسۡخَرُونَ مِنۡهُمۡ سَخِرَ ٱللَّهُ مِنۡهُمۡ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٌ

Waxanda kuma suke aibata muminai masu yin sadaka (mai yawa) don neman lada da kuma waxanda ba su da abin da za su bayar sai (kaxan) gwargwadon wahalarsu, sannan su riqa yi musu izgili, to Allah zai mayar musu da sakamakon izgilinsu, suna kuma da azaba mai raxaxi



السورة: Suratut Tauba

الآية : 80

ٱسۡتَغۡفِرۡ لَهُمۡ أَوۡ لَا تَسۡتَغۡفِرۡ لَهُمۡ إِن تَسۡتَغۡفِرۡ لَهُمۡ سَبۡعِينَ مَرَّةٗ فَلَن يَغۡفِرَ ٱللَّهُ لَهُمۡۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَفَرُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡفَٰسِقِينَ

Ko ka nema musu gafara ko ba ka nema musu gafara ba (duk xaya ne). In da za ka nema musu gafara sau saba’in to Allah ba zai gafarta musu ba. Wannan kuwa saboda sun kafirce wa Allah da Manzonsa. Allah kuwa ba Ya shiryar da mutane fasiqai



السورة: Suratut Tauba

الآية : 81

فَرِحَ ٱلۡمُخَلَّفُونَ بِمَقۡعَدِهِمۡ خِلَٰفَ رَسُولِ ٱللَّهِ وَكَرِهُوٓاْ أَن يُجَٰهِدُواْ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَقَالُواْ لَا تَنفِرُواْ فِي ٱلۡحَرِّۗ قُلۡ نَارُ جَهَنَّمَ أَشَدُّ حَرّٗاۚ لَّوۡ كَانُواْ يَفۡقَهُونَ

(Munafukai) waxanda suka qi fita (yaqi) sun yi farin ciki da zamansu (a gida) suna masu sava wa Manzon Allah, suka kuma qi su yi yaqi da dukiyoyinsu da kawunansu saboda Allah, suka kuma ce (da junansu): “Kada ku fita yaqi cikin zafin nan.” Ka ce da su: “Wutar Jahannama ta fi tsananin zafi.” Da sun zamanto suna ganewa



السورة: Suratut Tauba

الآية : 82

فَلۡيَضۡحَكُواْ قَلِيلٗا وَلۡيَبۡكُواْ كَثِيرٗا جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ

Sai su yi dariya kaxan su kuma yi kuka mai yawa a sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa



السورة: Suratut Tauba

الآية : 83

فَإِن رَّجَعَكَ ٱللَّهُ إِلَىٰ طَآئِفَةٖ مِّنۡهُمۡ فَٱسۡتَـٔۡذَنُوكَ لِلۡخُرُوجِ فَقُل لَّن تَخۡرُجُواْ مَعِيَ أَبَدٗا وَلَن تُقَٰتِلُواْ مَعِيَ عَدُوًّاۖ إِنَّكُمۡ رَضِيتُم بِٱلۡقُعُودِ أَوَّلَ مَرَّةٖ فَٱقۡعُدُواْ مَعَ ٱلۡخَٰلِفِينَ

To idan Allah Ya dawo da kai zuwa ga wata jama’a daga cikinsu sai suka nemi izinin fita a wajenka, to sai ka ce (da su): “Ba za ku fita tare da ni ba har abada, kuma ba za ku yaqi wani abokin gaba ba tare da ni ba har abada. Lalle kun yarda da zama tun farko, to sai ku zauna tare da masu zama.” (wato mata da yara)



السورة: Suratut Tauba

الآية : 84

وَلَا تُصَلِّ عَلَىٰٓ أَحَدٖ مِّنۡهُم مَّاتَ أَبَدٗا وَلَا تَقُمۡ عَلَىٰ قَبۡرِهِۦٓۖ إِنَّهُمۡ كَفَرُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَمَاتُواْ وَهُمۡ فَٰسِقُونَ

Kada ka qara yi wa xaya daga cikinsu da ya mutu salla har abada, kada kuma ka tsaya a kan qabarinsa (don addu’a). Lalle su sun kafirce wa Allah da Manzonsa, suka kuma mutu suna fasiqai



السورة: Suratut Tauba

الآية : 85

وَلَا تُعۡجِبۡكَ أَمۡوَٰلُهُمۡ وَأَوۡلَٰدُهُمۡۚ إِنَّمَا يُرِيدُ ٱللَّهُ أَن يُعَذِّبَهُم بِهَا فِي ٱلدُّنۡيَا وَتَزۡهَقَ أَنفُسُهُمۡ وَهُمۡ كَٰفِرُونَ

Kada kuma dukiyoyinsu da ‘ya’yansu su qayatar da kai. Lalle kawai Allah Yana nufin azabtar da su ne da su (dukiyoyin da ‘ya’yan), rayukansu kuma su zazzago suna kafirai



السورة: Suratut Tauba

الآية : 86

وَإِذَآ أُنزِلَتۡ سُورَةٌ أَنۡ ءَامِنُواْ بِٱللَّهِ وَجَٰهِدُواْ مَعَ رَسُولِهِ ٱسۡتَـٔۡذَنَكَ أُوْلُواْ ٱلطَّوۡلِ مِنۡهُمۡ وَقَالُواْ ذَرۡنَا نَكُن مَّعَ ٱلۡقَٰعِدِينَ

Idan kuma aka saukar da wata sura mai cewa: “Ku yi imani da Allah kuma ku yi yaqi tare da Manzonsa,” sai masu wadata daga cikinsu su nemi izininka su ce: “Qyale mu mu kasance tare da masu zama (a gida, wato mata da yara).”



السورة: Suratut Tauba

الآية : 87

رَضُواْ بِأَن يَكُونُواْ مَعَ ٱلۡخَوَالِفِ وَطُبِعَ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ فَهُمۡ لَا يَفۡقَهُونَ

Sun yarda da su kasance tare da mata masu zaman gida, an kuma doxe zukatansu, saboda haka ba sa ganewa



السورة: Suratut Tauba

الآية : 101

وَمِمَّنۡ حَوۡلَكُم مِّنَ ٱلۡأَعۡرَابِ مُنَٰفِقُونَۖ وَمِنۡ أَهۡلِ ٱلۡمَدِينَةِ مَرَدُواْ عَلَى ٱلنِّفَاقِ لَا تَعۡلَمُهُمۡۖ نَحۡنُ نَعۡلَمُهُمۡۚ سَنُعَذِّبُهُم مَّرَّتَيۡنِ ثُمَّ يُرَدُّونَ إِلَىٰ عَذَابٍ عَظِيمٖ

Kuma daga mutanen qauye waxanda suke kewaye da ku akwai munafukai, haka kuma daga mutan Madina; sun qware a kan munafunci, kai ba ka san su ba; Mu ne Muka san su. Za Mu azabtar da su sau biyu, sannan a komar da su zuwa ga azaba mai girma



السورة: Suratul Ahzab

الآية : 73

لِّيُعَذِّبَ ٱللَّهُ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱلۡمُنَٰفِقَٰتِ وَٱلۡمُشۡرِكِينَ وَٱلۡمُشۡرِكَٰتِ وَيَتُوبَ ٱللَّهُ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمَۢا

Don Allah Ya azabtar da munafukai maza da munafukai mata, da mushirikai maza da mushirikai mata, Ya kuma karvi tubar muminai maza da muminai mata. Allah kuwa Ya kasance Mai gafara ne, Mai jin qai



السورة: Suratul Fat’h

الآية : 6

وَيُعَذِّبَ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱلۡمُنَٰفِقَٰتِ وَٱلۡمُشۡرِكِينَ وَٱلۡمُشۡرِكَٰتِ ٱلظَّآنِّينَ بِٱللَّهِ ظَنَّ ٱلسَّوۡءِۚ عَلَيۡهِمۡ دَآئِرَةُ ٱلسَّوۡءِۖ وَغَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡ وَلَعَنَهُمۡ وَأَعَدَّ لَهُمۡ جَهَنَّمَۖ وَسَآءَتۡ مَصِيرٗا

Ya kuma azabtar da munafukai maza da mata, da mushirikai maza da mata, masu munana zato ga Allah. Mummunar azaba ta koma a kansu; kuma Allah Ya yi fushi da su, Ya kuma la’ance su, Ya kuma tanadar musu Jahannama; makoma kuwa ta munana



السورة: Suratul Hadid

الآية : 13

يَوۡمَ يَقُولُ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ وَٱلۡمُنَٰفِقَٰتُ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱنظُرُونَا نَقۡتَبِسۡ مِن نُّورِكُمۡ قِيلَ ٱرۡجِعُواْ وَرَآءَكُمۡ فَٱلۡتَمِسُواْ نُورٗاۖ فَضُرِبَ بَيۡنَهُم بِسُورٖ لَّهُۥ بَابُۢ بَاطِنُهُۥ فِيهِ ٱلرَّحۡمَةُ وَظَٰهِرُهُۥ مِن قِبَلِهِ ٱلۡعَذَابُ

A ranar da munafukai maza da munafukai mata za su riqa cewa da waxanda suka yi imani: “Ku saurara mana mu xan xosani haskenku.” Aka ce (da su): “Ku koma bayanku (watau duniya) sai ku nemi haske.” sai aka raba tsakaninsu da katanga wadda take da wata qofa, daga cikinta akwai rahama, bayanta kuma azaba ce (take bugowa) daga gare ta



السورة: Suratul Hadid

الآية : 14

يُنَادُونَهُمۡ أَلَمۡ نَكُن مَّعَكُمۡۖ قَالُواْ بَلَىٰ وَلَٰكِنَّكُمۡ فَتَنتُمۡ أَنفُسَكُمۡ وَتَرَبَّصۡتُمۡ وَٱرۡتَبۡتُمۡ وَغَرَّتۡكُمُ ٱلۡأَمَانِيُّ حَتَّىٰ جَآءَ أَمۡرُ ٱللَّهِ وَغَرَّكُم بِٱللَّهِ ٱلۡغَرُورُ

(Munafukan) suna kiran su cewa: “Yanzu ba mu kasance a tare da ku ba ne?” Suka ce: “Haka ne, sai dai ku kuma kun fitini kanku (da munafunci) kuka kuma saurari (aukuwar mummunan abu ga muminai), kuka kuma yi shakka (game da addini), burace-burace kuma suka ruxe ku har mutuwa ta zo, Shaixan kuma ya ruxe ku game da Allah



السورة: Suratul Hadid

الآية : 15

فَٱلۡيَوۡمَ لَا يُؤۡخَذُ مِنكُمۡ فِدۡيَةٞ وَلَا مِنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۚ مَأۡوَىٰكُمُ ٱلنَّارُۖ هِيَ مَوۡلَىٰكُمۡۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

“To a yau ba za a karvi wata fansa ba daga gare ku da kuma daga waxanda suka kafirta. Makomarku wuta; ita ce ta kamace ku, makoma kuwa ta munana.”



السورة: Suratul Mujadila

الآية : 14

۞أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ تَوَلَّوۡاْ قَوۡمًا غَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مَّا هُم مِّنكُمۡ وَلَا مِنۡهُمۡ وَيَحۡلِفُونَ عَلَى ٱلۡكَذِبِ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ

Shin ba ka ga waxanda suka yi abota da wasu mutane da Allah Ya yi fushi da su[1] ba, su ba cikinku suke ba, ba kuma cikinsu suke ba; su kuma riqa rantsuwa a kan qarya, alhali kuwa su suna sane (da yin ta)?


1- Su ne Yahudawa waxanda munafukai suke abota da su.


السورة: Suratul Mujadila

الآية : 15

أَعَدَّ ٱللَّهُ لَهُمۡ عَذَابٗا شَدِيدًاۖ إِنَّهُمۡ سَآءَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Allah Ya tanadar musu azaba mai tsanani, lalle su abin da suke aikatawa ya munana